← Book details Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 23

Sashe 22

Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ASIBITIN SAUDI-GERMAN
RANAR AIKIN IDON HAUWA-KULU
(KARO NA BIYU)
Dr. Sarham, da sauran masu taimaka maa a yayin tiyata sun zama ready a dakin tiyatar da zaa yiwa Hauwa aikin ido, haka masu allurar anaesthesia. Dr. Madinah Attahiru, ta turo yar uwarta Hauwa Bilyaminu a kan gadon marassa lafiya tana sanye da korayen kayan aiki na wanda zaa yiwa tiyata, haka shima likitan korayen kayanne a jikinsa da hularsu. Bisa umarnin likita Sarham, masu allurar tafi da ranka suka fara, daga nan suka shiga aikinsu ba ka jin tashin komai sai tashin yaren likitanci a yayin surgery na idanu. Kalmomin da su kadai suka san me suke nufi da fadarsu. Da yake sun dade da gano matsalar Hauwa-Kulu tuntuni sun kuma dade da tsara komai daga binciken da suka dade suna gudanarwa akan idon Hauwa nada nan aka gama phacoemulsification surgery din, cikin abinda baifi mintuna 45 ba.
Ana fatan kwancewa nan da awanni biyu masu zuwa. Zukatan su Mama, Madinah, Sumayyah, Usman, da Mardhiyyah dake gefe goye da baby Sumayyah, ga ‘yan biyu suma a hannunta na hagu da dama tana lallashinsu kamar su fita daga cikin kirazansu with so much high anticipation.
**** **** ****

KOFAR DANAGUNDI (KANO)
C
ikin rikicewa da tsananin tashin hankali yake ta trying kiran wayar Dalha ana cewa bata shiga, sai ya koma kiran dansa Jamilu cikin hada uban gumi. Baba zakari kenan cikin gigicewar rasa Dalha babban yaronsa daya tattarawa dukkan jarinsa ya tafi Cotonou domin shigo da atamfofi. Ba wannan ne karo na farko da suka fara wannan sanaar shida Dalha ba sun fara da yi kadan kadan ne har Dalha ya tabbatar Zakari ya gama amincewa da shi kafin yace suyi babban sari na atamfofi da shaddoji kasancewar karamar sallah ta matso.
Amma yau kwana goma sha biyar ya kasa samun layin Dalha wato tun tafiyarsa. Da ya kasa samun Dalha sai ya koma kiran Jamilu, Jamilu ya daga ya tabbatar masa motarsu Dalha ta kife a bisa binciken da yasa aka yi masa kuma ba abinda ya tsira a motar, kamar yadda babu wata rai data tsira.
Tsananin gigicewa (bata mutuwar dalha daya shekara kusan 10 yana wahalta masa ba, aah ta kafatanin dukiyarsa da ya tattatara ya damka masa ya tafi da ita ne) tasa ya kama hanyar Singa a kafa, yana tafe yana sambatu, duk nisan kofar Danagundi zuwa kasuwar Singa bai ganshi ba, saboda tashin hankali.
Bai yarda da abin da Jamilu ya fada ba shi ya sa ya taka sayyadarsa har Singa, don ya san yana zuwa zai ga Dalha a shago yana fama da kwastomomi yadda suka saba kullum.
Tun daga nesa yake hango hayakin dake tashi kamar bakin hadari a kasuwar SINGA. Ya kara daga kafa yana fadi a ransa lallai damuna ta zo ba shiri a watan da ba nata ba. irin wannan hadari haka?
Yana kara matsowa yaga dafifin mutane suna darawa yan kwana-kwana suna wucewa da motar su bayan already wutar tagama cinye rabon sa, ciki har da sashen yan atamfa. A kusa da shi yaji daya daga cikin yaransa yaa gaya masa.
“Baba Zakari sai hakuri. Haruna ne jiya da yamma ya jona heater a shagonmu, sai ya manta ya tafi gida, kuma a kofin roba ya jona, shi ne heater ta cinye kofin ta kama shagon da wuta”.
Abinka da wutar dare, ko kafin masu gadin kasuwar su ankara wutar ta lashe shagon Alh. Zakari mai atamfa har ta soma laso makwabtansa.
Baba Zakari sai kwasar shi akayi a wheel-barrow zuwa gida saboda sumewa yayi a wurin aka tattakeshi a wurin baa sani ba sabida dafifin alumma da kokarinsu na kashe wutar shikuma sai kara kutsawa yake yi har karfin sa ya kare jininsa ya hau, ya fadi a wurin baa kula ba aka yi ta bi ta kansa ana tuntube ana wucewa saida wasu suka daga shi da kyar suka saka a wheel-barror yaran da suka san shi a kasuwar suka tura shi zuwa gidan sa a dan agundi.
**** **** ****
Chapter 22 · 0% Book details