← Book details Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 23

Sashe 11

Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da farko Madinah gabanta faduwa ya yi, amma haka ta daure ta basu hanya. Wani irin makoko na yunkuro mata, ji ta yi kamar suna shigewa din, ta fita a guje kawai ta bar gidan. Muryar Baban Waheedah ta dawo da ita tunaninta, yana fadin,
Come on Waheedah.
Ya mika hannu ya karbi yarinyar da ke ta mika masa hannu tana zillo daga jikin Madinah.
Madinah ta ba shi hanya, cikin kauda ido, hannunsa daya rike da Waheedah, daya rike da hannun Hauwa suka shiga cikin falon.
Sai da ya tabbatar Hauwa ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, ya mike ya bi bayan Madinah wadda ta yi wucewarta daki ba tare da ta ce musu ko ci kan ku ba. ko ta nuna ta san tare yake da wata halitta, mutum din ma dan adam mai daraja. Wannan abu ya bakantawa Sarham ba da kadan ba.
Tana shiga yana shiga, ya tura kofar. Da ta daga ido ta dube shi bai iya gasgata cewa kwayar idon Madinah ba ce, sabida yadda ta rine da bacin rai da wani zazzafan kishi mai barazanar fasa mata ido.
Kin kyauta kenan Madina? Ai ko ni ba ki yi min sannu da zuwa ba, kya yi wa Maijidda wadda ta zo bakon wuri, ta tadda ke a gidanki.
Dakata don Allah Baban Waheedah!
Ka gaya min za ka zo min da wannan yarinyar?
Kana tsammanin ni Madina zan iya zama gida daya da kishiya ne? Kishiyar ma irin wannan musakar?
Sarham ya yi kokarin kama hannun Madina, ta yi maza ta ja da baya,
Dont dare touch me again, bayan ka gama tattaba makauniya.
Maganar sai da ta yi amsa kuwwa a kunnen Hauwa sabida yadda ta ware makogaro ta fadeta.
Sarham kuma ya kai wa Madinah wani wawan mari, sai dai kafin hannun nasa ya sauka a lafiyayyar fuskar Madinah tayi maza ta kare da hannunta, ta kuma yi saurin ja da baya kada ya illata mata fuska.
Nashi idon har ya fi nata rinewa da bacin rai, ya ce, Munawwarah, ke ce kuwa? Yau ina hankalinki da tunaninki ya je ki ke ma wani dan Adam gorin halitta?
Are you not a medical personnel?
Ni kike dagawa murya kamar wani dan ki? Anya ke ce ko sauya ki aka yi kafin naje na dawo?
Tsaki Madinah ta yi, ta juya ta bar masa dakin tana cewa,
Aah, ba ni ba ce, ko kuma kawai kace daga turu na fito. Ka sa a ranka ba zan taba zama gida daya da wannan musakar ba, balle in hada shimfidar miji da ita. Ko ta fita yanzunnan ka kama mata wani gidan ko ni in fita in bar muku gidanku, amma tareda takardata don bazan yi yaji a dawo dani ba.
Ta yi maza ta shige toilet ta saka key, ganin yadda maganganunta ke kaskanta shi, baa fuskarsa kadai ba har a jikinsa dake mazari kamar ana kada masa gangi.
Ka fita a dakina Sarham, don Allah, saboda wallahi bakidaya ka koma min wani musaki….
Kwafa Sarham ya yi ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya dauki Waheedah da ya ajiye a gado tana tsala kuka ba.
Dakin Sumayyah ya nufa, sai ya tarar da dakin a kulle. Wato ita kuma ta tafi ba izninsa. Ya fiddo waya ya kira ta,
kina ina ne dakinki a kulle?
Wa? Ni? Bhaiya ai na tsufa a hostel, ba ni ba kara kwanan gidanka.
Sarham ya kara hassala fiye da farko, ya ma fasa gaya mata cewa ya zo da Hauwa don bai ga amfani ba, ya ce,
In na kara cewa ki zo gidana Summy ki ce shege ne ni ba haihuwar Maisharia da Prof. ba. Na yafe miki zuwa gidana daga yau har gaban abada.
Jikin Sumayyah ya yi sanyi, ta ce, Bhaiya
Ya yi maza ya kashe wayar, jikinsa yana tsuma da bacin rai, ba tare da ya saurare ta ba, ya koma falo ya tadda Hauwa.
A yadda ya bar Hauwa a haka ya same ta a zaune a kan kujera ita ma ta kumbura tayi fam, kiris ta ke jira ta fashe. Don bata taba jin cin mutunci akan lalurarta rabin wanda ta ji a bakin Madinah yau ba. Hakika makanta abu ce mai saka karfin ji!
Ya yi kamar bai ga kumburin da ta ke yi din ba, ya dauki jakar kayanta ya kama hannunta ya ce,
Taso ki biyo ni mu je ki huta.
Ta ja tunga a inda ta ke zaune ko motsawa ba ta yi ba. Ta kuma warce hannunta.
Yaya Doctor ni gida zan koma!.
Idanuwanta suka yi narai-narai cikin kwalla, wadda ba ta idasa zubowa ba.
Ya dube ta a matukar hassale itama, ya ce,
Ga hanya nan ki koma din, idan ba ku hadu ku ukun kun haukata ni ba, ba ku ci sunanku na mata tumakai ba!.
Ya dauki jakarta ya nufi wani daki da ke rufe wanda ke kallon dakin Madinah, ta shirya dakin ne don bakinta yan gidansu na Sorondinki in sun zo aikin Hajji su kan shigo su kwana, shi kuma nan ya ga nan ya dace Hauwa ta zauna don girmansa daya da dakin Madina.
Dakin a gyare yake tsaf babu abinda babu na bukata, ga sabon bayi (toilet) makale a cikinsa. Ya ajiye jakar Hauwa ya fito.
Daidai fitowarsa ya ga Madinah tana kwashe warmers din abincin da ta girka daga kan dining table. Ta kwashe komai ta juye a leda ta saka a freezer.
Tana kallon Hauwa a zaune tana tsane ido da gefen mayafin abayarta, ta wutsiyar ido ta harare ta, bayan ta gama kwashe komai ta shige dakinta ta kulle ta ciki.
Sarham ya dawo ya zauna daf da Hauwa, ya rasa ta ina ma zai bullo musu su duka. Hauwa jin zamansa a kusa da ita sai ta kara sautin shesshekar kukanta, wai ita kawai ya maida ita wurin Mama bazata kwana a gidan ba.
Ga gajiya, ga yunwa, ga bacin rai da suka tarun masa don haka bai kula ta ba. Ya fiddo waya ya kira Abbansa yana maida fushinsa, ya gaya masa sun sauka lafiya, haka Mama ma. Bai ja hirar da tsayi ba kuma ya kama hannun Hauwa ya soma janta ta karfi zuwa dakin da ya zabar mata.

A gefen gadon dakin ya zaunar da ita, This is your room, in kin ga dama kuma ki kama hanyar Kano a kafa daidai ne. zan je in yi sallah, muje ga toilet in nuna miki yanda yake ki gane komai, ko kina son shiga.
Wannan karon ta bashi amsa cikin share ido jin yace su je kuma bai kama hannunta ba.
Idan na fadi fa, tunda ban san hanyar koina a gidan ba?
Tausayi ne mai tsanani ya kama shi, kawai sai Hauwa taji Sarham ya dauketa yana tafiya da ita zuwa toilet din a hannayensa.
Kunya taji soai ta hau sunne kanta a kirjinsa. Daka barni na tafi da kafata don in gane hanyar koina.

Dr. Sarham bai yarda ya direta ba sai a toilet din, ya nuna mata yadda za ta yi amfani da komai na bandakin, ta hanyar dora hannunta akan komai yana bayani. A karshe ya nuna mata (shower) ta wanka da yadda zata dinga kunnawa da rage zafin ruwan daga famfon kada ya kona ta, ya nuna mata kunna (water heater) wadda yace in ta kunna ba sai ta kashe ba don tana kashe kanta automatically.
Ita ba ta san dalilin yawan taba hannayenta da yake yi ba wai yana nuna mata abubuwa, nan kuwa ba ya gajiya da touching dinsu ne sabida taushin fatar hannunta.
Na gane, ka je zan yi wanka!.
Kin fasa komawa gun Maman? Ya tambaya cikin gatse, yana janyota yana makalewa.
Hauwa ta tsuke fuska da baki, ta ce, Ya danganta da sunan da aka kara kirana da shi a gidan nan. Ni duk duniya ba wanda ya taba ce min musaka. In ma musakar ce shin miskini ba mutum bane? Ni dai na san;

Inna Akramakum Indallahi Atqakum.

Ta hakan ne ya gane cewa ta ji me Madina ta fada a kanta. Ita makanta da ma sanya karfin ji ne da ita. Ya kuma san ba abinda ta tsana a duniya irin sunan da Madinah ta kira ta da shi, yau mafi muni, don haka ya sassauta murya ya sake makalkaleta a jikinsa yana shafa gadon bayanta, yace.
Ki yi hakuri, ki kara yin hakuri, ki kuma koyi karbar ‘labelling’ na sunan lalurarki, hakan ne zai sa ki zauna lafiya ko da wani ya fada ki daina damuwa irin haka da shiga bacin rai, ba lallai ne kowa da niyyar gorin ido yake ce miki makauniya ba, wani kuma bada isgilanci bane, aah suna ne da Malam Bahaushe ke kiran duk wani mai lalurar gani dashi don banbance lalurarsa.
Ki koyi kauda kai a kan hakan muddin kina so ki rabu da bacin rai.
Ya kara sassauta murya, ya ce,
Ki gama wankan kiyi sallah mu je tare mu sayo abinci.
Saboda ya ga sanda matar gidan ta fito ta kwashe nata bakidaya, (amma bai fadi hakan ga Hauwa ba ya barwa ransa).
Chapter 11 · 0% Book details