Sashe 10
Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Wallahi sai dai ka daina alaka da ni din Ussy, da dai in bari ka auri Sumayya, kai ne ba ka san irin halinta ba, wallahi annamimiya ce zuciyarta bata da kyau bata kauna ta.
Sai kin gaya min me ta yi miki na rashin kauna, sai kin gaya min me tayi na annamimancin, alhalin ita din ba kishiyarki ba ce, kanwar mijinki ce, uwa daya uba daya.
Madinah ta kara hassala ta ce, Yaya Usman ban yi niyyar gaya muku ba sam, nikadai na binne abun ina fama dashi a raina don kada Daddy ya kashe min aure, amma yau tunda ka dage a kan Sumayyah zan gaya maka, Hajjah Ramlah ma zan gaya mata. Sarham ya kara aure a Kano, itada uwarsu sun baiwa yarinyar masauki, tun filazal Sumayyah bata taba sona ba, na rasa laifin da na yi mata.
Ko don in rama abin da Sumayyah tayi min na kiyayyar babu gaira babu dalili na rantse ba zaa yi auren nan ba, don na lura ita ma munafukar tana raayinka, har da yi min wani sabon ladabi yanzu, ba ta san kar nake kallonta kamar takarda ba..
Sumayyah ta yi mata gyaran murya daga bakin kofa, Madinah ta kashe wayar ta tsuke fuska, sai ta karasa shigowa dakin ta kwantar da Waheedah a gadonta hannunta rataye da jakar kayanta, kamar ba ta ji me Madinah ke fada a kanta ba, ta ce,
To Anty Madinah da alkhairi, zan koma hostel, tunda Yaya Sarham ya ce yau zai dawo, nagode da zumuncin ki.
Madinah ta harareta kasa-kasa, ta ce,
A gaishe su!.
Sumayyah ta juya cikin bacin rai za ta bar dakin tana fadi a ranta, ko son Usman zai kashe ta itama ta hakura ba za ta aure shi ba, ko da gold aka kera shi.
Har ta kai kofa zata fita Madinah ta ce, Umh! Ji mana Summy???”
Sumayyah ta dakata ba tare da ta juyo ba, idonta fal kwallah don har ga Allah tana son Usman Sorondinki. Ba ta san me ya sa zuciyarta ta yi mata wannan rashin adalcin ba, tunda Yayan Madinah ne da baasa ga maciji.
Madinah ta ce, Makauniya ba ta da Yaya ne? I mean ita kadai ce a wurin iyayenta babu dan uwa babba namiji haka?”
Cikin rashin fahimta Sumayyah ta juyo tana kallonta.
Madinah ta ware mata fararen idanunta sosai, ta kwance ribbons din data daure gashinta dashi ya zubu a wuyanta ta girgizashi sannan ta kara daure shi cikin ‘hairbound’ din, ta ce,
Eh, ai ba za ta rasa dan uwa ba, I mean makauniyar gidanku, ina ga shi zai fi dacewa da ke, dangin yar Badala yan cikin gari ba nawa dan uwan ba haifaffen Saudiyyah.
Sumayyah ta saki kwallar idonta, ta fice ba tare da ta ce da Madina komai ba, tana tsoron tayi abinda zaa ce tayi fitina a gidan Yayanta amma data baiwa Madinah amsa, ta so ta ce da ita “dadin abun ma mun san asalin balbela, kowa ya san SORONDINKI a Kano, nan ma cikin Badalar ne yar rainin wayo kawai hankaka maida gidan wani naka.
Wannan da yar sarkin Kano ce watakila ko daga ido ba za ta rika yi tana kallon mutane da kima ba.
Shin me ta maida yaran cikin badala ne? Yan kauye ko? Za kuwa ta ga kauyanci ganin idonta, sai ta kilar da HAUWA, duk da haka ma Mama tana yawan gaya mata irin ci gaban da Hauwa ke samu a jamiah tun dawowarsu.
Daga karshe kuma tana tafe a hanya don komawa hostel ta canza shawara, ta sa a ranta rashin mutuncin Madina a kan alakarta da Usman ba zai sa ta fasa son Usman ba, kuma ba zai sa ta barshi ba, don kam tana matukar sonshi. Gara ma ta rike abinta tayi ta gumawa Madina haushi. Ai Usman gaba yake da ita ba shine kanin ta ba da zata saka shi ko ta hana shi ba, bakin cikin ta daya yadda ta gama bata ta gun mahaifiyarsu Hajjah Ramlah.
Ko awanni biyu Sumayya ba ta yi da komawa hostel ba, Ajrah ta sauke Dr. Sarham da maidakinsa, wato amaryarsa Hauwau a kofar flat dinsu. Watakila Sumayyah da ta san cewa da Hauwa ya taho da ba ta tafi ba.
Shi kuma bai gaya wa kowaccensu cewa tare zai zo da Hauwa ba. Ita Madinah bai samu wayarta ba ita kuma Sumayyah surprising dinta yaso yi.
Usman ne ya yi mata waya cewa su hadu a jamiarsu don Madina ta masa iyaka da zuwa gidanta, shi ya sa ta bar gidan, da kuma maganganun data ji Madinah nayi da Hajjarsu a kanta sun tsoratata.
Dr. Sarham ke danna kararrawar shiga kofar falon gidanshi, Hauwa na daga dan bayansa ta sha glass da shudiyar abaya, harde da hannuwanta biyu a kirji.
Dr. Madinah wadda a lokacin take shilla Waheedah cikin lilonta cikin murnar ta kori Sumayyah at the same time tana waya da Hajja Ramlah, korafin dai taci gaba da kai mata iri-iri kan kanwar mijinnata wadda ta tabbatar ba tun yau ba ba ta kaunar ta bude ido ta ganta tare da dan uwanta.
Ta ce ma Hajja Ramlah,
Ban taba gaya muku ba don bana son ki ce in dawo gida Hajjah, Sarham ya dade da kara aure, kuma sun baiwa yarinyar masauki a gidansu.
Hajjah ke shaida ce kan cewa raina ne kawai ban cire na bai wa Sarham da uwarsa da kannensa ba don so da kauna, duk wata kulawa da mace ke yi wa dangin mijinta babu irin wacce ban yi musu ba. Ta karasa cikin karyewar murya.
Hajja Ramlah bata san sanda ta yi wani ashar mara dadin ji ba, lokacin da Madinah ta idasa gaya mata irin macen da Sarham ya aura da irin nakasarta.
Idan dai ni na haife ki Madinah, to tattaro kayanki ki ajiye masa yarsa ki dawo gida, martabarki da ajinki bai yi wannan lalacewar ba.
Bari Daddy ya shigo in ma kin ki tahowa ni da kaina zan zo in fito da ke tunda Sarham ba shi ne autan maza ba.
Madinah ta ce, Abin da na guda kenan da yasa tun farko na ki gaya muku Hajjah, Sarham ba zai taba sakina ba, don haka ina amfanin in tafi gida da dakon aurensa watarana in dawo?
Besides na lura yanzu baya ta yarinyar, for as long as a year bai je inda ta ke ba, sai yanzu da ya tafi daurin auren kanwarsa ta farko.
Ta ci gaba da dannar mahaifiyarta ta roke ta kada ta daga wa Daddy hankali a kai saboda Sugar (diabet) dinsa yayi tsanani, taroketa tayi shiru kawai, za ta iya da rayuwa da Sarham a duk yadda ta same ta.
Hajja Ramlah ta san cikin yaranta, Madina ce kadai mace amma Allah ya azurtata da hankali. Sau tari ita ce mai yi mata fadan tayi ba daidai ba in ta kuskure wa mahaifinta. Hajja Ramlah ta samu kanta da cewa,
Ke dai ki ka kawo yaron nan ki ka ce kina so Madinah, kada ki tilasta kanki zama da shi in akwai wulakantarwa da tozarci, abu ne da daga ni har mahaifinki ba za mu lamunta ba, wato ya wulakanta ki ko ya kaskantaki ko ya hada matayinki da makauniya.
Hajja kada ki damu, I can handle everything, I can take care myself, amma babu batun ‘yaji’ a policy dina. Yau in Sarham ya sake ni zan bar masa gidansa, amma ba zan taba yin yaji da aure a kaina ba.
Karar kararrawar shigowa ta sa ta yi wa Hajja Ramlah sallama, ta dauki Waheedah da ta fara kuka a kan kafadarta, ta isa ga kofar bayan ta amsa da cewa,
Ina zuwa.
Ko da ta bude ita ta san ko kowa bai gaya mata ba, wannan din da ya rike hannunta cikin nasa, na nufin HAUWA-KULU.
To amma a yadda Surayyah ta fasalta mata ita ba a hakan ta ganta ba, wato irin yan tallan abincin Tashar cikin gari, talauci sama da kasa, yan babu cin yau babu na gobe, almajira, musaka.
Wannan din da ke tsaye a gabanta wata ‘classy’ yarinya ce da idanu ne kawai ba ta da su, amma za ta goga da kowacce irin macen kasar Najeriya.
Sakamakon cewa fuskarta fes, babu ko digon pimples, idanunta cikin gilashi mai duhu ainun don haka ba ta samu ganin kalar kwayar idanunta ba.