Sashe 8
Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Muna bakin motar Baba Sa’idu yana kara yi mun nasiha a kan muhimmancin kula da sallah a kan lokacin ta. Ya ce, “Zaynabu in kika kyautata sallarki, dukkan aiyukanki za su kyutata. A kullum ki yi kokari ki fi karfin zuciyarki, kada ki yarda ta fi karfinki. Ki kiyaye wadannan tsokokin guda biyu ‘harshe da zuciya’. Idan kika iya musu za ki iya ma dukkan rayuwarki. Idan suka yi kyau, dukkan al’amuranki za su yi kyau.
Ki ci gaba da yi ma Innarki biyayya, kada ki taba yarda da kallon da ake mata na cewa ita din ba ta da hankali. Idan akwai mai hankali a duniya to ita ce, tana da kirki tana da alhairi yanayin rayuwa ne ya maida ta hakan.
Kada ki yarda da yin mu’amala ko yaya take da namijin da ba muharramin ki ba, har sai kin san kanki, har sai kin san ke din WACE CE? Kada ki dinga sa abubuwa a ranki har su dameki kamar Innarki, ta fiya kullaci! Domin hakan lahani ne ga lafiya da kwakwalwa. Jeki gida Allah ya bamu alkhairi”.
Na juya ina tafiya sannu-sannu, har na kai bakin kofar gida na sake juyowa, shima Baban bai shiga motar ba kallona yake. Na dawo da sauri, da na tuna ban yi masa addu’ar da na saba ba, na ce,
“Baba Sa’idu Allah ya kaika lafiya”.
Ya ce, “Amin Zayanabu, Allah yai miki albarka….”. Muna dagawa juna hannu ni da Iftihal direba ya ja suka tafi. Ban koma gida ba sai da na ga bacewar su cikin rairayi da kurar da ke bisa hanya.
Dawawo ta kenan har zan shiga dakin Inna, amma jin muryar Malam yana ta fada yasa ni dakatawa ba don na so ba.
“Kin dauka har yanzu Zaynabu yarinya ce ne? Irin abubuwan da kike nunawa Sa’idu a gabanta zai sanya ta sanya ma kanta ayar tambaya. Abu anyi shi ya wuce shekara da shekaru ya wuce amma kullum sabo kike mai da shi.
Rabi kullum kina girma amma kina mai da kanki baya, idan don kin ga ba ta yin magana ne kike yi masa hakan a gabanta, ni na gaya miki wataran za ta tambaye ki dalilin haka, me za ki ce mata?
Allah ma muna mishi laifin da ya fi wannan ya yafe mana, balle ke mutum dan adam? Wace ce ke da ba za ki yi afuwa ga wanda ya saba miki ba? Inda Allah baya yin afuwa a garemu, da tuni bai nade duniyar ba saboda dimbin sabon da ke cikin ta? Ina jiye miki ranar da ABU ZA TA JUYA MIKI BAYA A KAN SA’IDU, wannan a rubuce yake! Don haka ki sanyama ranki salama….”
Na yi hanzarin juyawa na koma soro ina ta yarfe gumi da hawaye. Ni ZAINABU ABU wace irin rayuwa ce wannan? Babu ranar Allah da za ta fito ta fadi, ba’a yi musayen yawu a kaina ba. To ni din WACE CE? Kenan ba daya nake da sauran ‘ya’ya su Hafsisi ba, tunda kuwa ban taba jin an samu sabanin ra’ayi a kansu ba.
Kai ba wanda yake zancensu cikin gidan, kowa ya bude baki ZAYNABU…. KYAUTA… ABU.. ...
“Kada ki dinga sa abubuwa a ranki har su dameki tamkar Innarki, domin hakan lahani ne ga lafiya da kwakwala….”. Na tuna nasihar Baba Sa’idu, don haka na yi kokarin mantawa da wannan tunanin kada ya zamomin lahani ga kwakwalwa.
Sati biyu a tsakani sai ga Ya Faruk ba zato ba tsammani. Ai kuwa na kwashi murna ba ji ba gani, na rasa ina naka-saka ina naka-aje da shi don farin ciki, inda duk yasa kafa cikin gidan nan nake mayas da tawa, na like masa tamkar cingam. Shima cike yake da farin cikin ganina, ya kara kyau da tsayi, ga wani irin gogewa da yake yi, jikinshi ya koma irin na Iftihal, mai santsi da taushin gani.
A dakin Inna Dubu muke, na kwanta lamo aikinsa, cikin karamar murya na ce, “Ya Faruk Iftihal ba ta baka sako ka bani ba?” Ya ce, “Ta bani mana, fara kawo salala!”.
Murmushi na yi, “Salalar me kake so?” Ya ce, “Ki daina wannan son jikin kamar mage, musamman kwanciya a jikin maza, ba kowa ne na gari ba, wani maye ne wani dan iska ne…”. Ba ni kadai ba hatta Inna Dubu ta ji kunyar maganarsa.
Ta ce, “La’ilaha illallahu!…..” Amma shi din ko a jikinsa, iyakar gaskiyar shi ya fada zuciyarshi sak! Cikin sanyin jiki na tashi daga jikinsa na koma can gefen Inna na takure, duk raina ya baci.
Bai kara bi ta kaina ba ya jawo jakarsa ya bude ya fiddo damin littattafan yara (junior readers series) na Turanci guda hudu ya miko mini. (An African Night Entertainment, Akin Goes To School, Suger Girl, da The Boy Slave). “Ga shi in ji ta”.
Ya kuma fiddo wani takalmi (cover) rufaffe baki mai tsinannen kyau cikin kwalinsa, shima ya turo mani duk in jita. Ya sanya hannu ya fiddo ‘yar takardar littafin memo ta sha zanen shudayen furanni, ita ma ya miko mani. Na bude cikin zumudi, ga abin da ta rubuta layi daya kacal.
“Abu plz, come soon”.