← Book details Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 24

Sashe 22

Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kanon Dabo, yaro ko da me ka zo an fika, mai Dala da Gwauron Dutse, tushen Maguzawa ta Dabo tumbin giwa. Kwanan mu biyu a gidan Baba Sa’idu na Kano dake Sultan Raod sannan muka tattaro muka yo Gwarzo. In ba don idon Abba ba, da Hajiya Sa’a da iyalanta ba za su Gwarzo ba iyakacinta Kano, domin ita a gareta takura ne zaman kauye ai sai dole. Amma shi Abban baya ganin haka. Kar ku yi mamakin jin cewa Hajiya Sa’a ‘yar Gwarzo ce ‘yar kanwar Inna Dubu da aka rike a gidan Malam Ali, domin iyayen Dubu talakawa ne futuk amma duk sun rasu. Don haka Dubu ta daukota ta rike. Shi kuma Abban a rayuwarshi ba shi da kamar Malam Ali, a shirye yake kuma da ya bata da kowa in dai a kanshi ne, daga ‘ya’yan shi har matan shi ya sha gaya masu wannan. Don haka wannan lokacin take taka-tsan-tsan. Ita dama ‘yar dakin Innar Faruq ne, don haka can suka sauka da ‘ya’yanta. Ni da su Mam, ‘yan biyu da Gambo muna dakin Innana dake ta faman makale ni kamar ta maishe ni ciki. Yau abin da sauki tunda kuwa ban ga ta hana su Iftihal shiga dakinta ba, ko don ganin idon uwarsu ne, oho! Ko kuma ‘yan mutuncin ne a kanta? Na danganta hakan da dokin zuwana da take, domin na yi dadewar da ban taba yi ba har watanni shaida ban zo ba. Rabi da Mama sun barke da hirar yaushe gamo wadda duk rabinta labarin rayuwata ne da ke burge kowa, yake kuma baiwa kowa sha’awa a can Sokoto. Ta ce, “Zaynabu-Abu uwar addini ce, ban taba ganin yarinya Abida (mai ibada) irin Zaynabun ki ba”. Inna ta kara janyo ni ta rungume tana murmushi dadi ya cika ta. Don ba abin da take so a rayuwarta irin ta ji ana yabon Abun ta, Kyautar ta, Kyautar Allah (kamar yadda take cewa). Sai na samu kaina da kara godiya ga Allah da ya kare ni daga aikata ZINA, kamar yadda zuciyata da gangar jiki ke so, har suka so su ja ni. Wannan ya samo asali daga addu’ar da Malam yai min a sanda aka haifeni a al’aurata, domin kariya daga aikata zina. Aya ta ( ) cikin Suratul-Maryam. (Don haka iyaye a dage da kula da ita wannan addu’ar a yayin da aka haifi yaro, to insha Allah ba dai ya aikata zina a rayuwarshi ba). Na tabbata da na karya zuciyar Inna Rabi, fiye da wanda ta samu kanta a gaba dayan tsayin rayuwar ta, wanda ni ba zan ce ga shi ba. Da duk wannan kaunar da take mun, ta koma kiyayya, watakila irin kiyayyarta ga BABA SA’IDU. Sai na samu kaina a mai tambayar kaina, wannan na nufin BABA SA’IDU ya aikata ZINA ne shi yasa ta tsane shi? To da WA????? (Wa’iyazubillahi). Wama taufeeqee illa billahil aliyul azeem…. Kada Allah yasa tunanin nawa na banza ya zama gaskiya, kada Allah yasa tunanin nawa na wofi tabbatacce ne. ya Allah ka fitar mun da wannan mugun tunanin a zuciyata…. Allah ka dube ni, kasa tunanina ba gaskiya bane rudin shaidan ne. Ba abin da ke dadadawa Innana kamar ganin yadda nake girma da wani irin murjewa, kai ka ce irin Larabawan nan ne na Lebonon. Duk na fi ‘ya’yan Farfesa daukar ido da kwarjini, haka duk kalar kayan da nasa kyau suke min su kuma amshe ni kasancewata jajur, masu tsada ne ko akasi, kai ka ce don ni aka kirkire su. Ni Zaynabu-Abu shiru-shiru ce, bani da kwaramniya, kuma bana sonta. Da wuya ka ga ina magana in ba a kan abu mai muhimmanci a gareni ba. Sun baro Gwarzo bayan motarsu cike da tsarabobin da suka saba komawa dasu, wato kamar su man shanu, garewanin man gyada, kindirmo, madarar shanu, kwan kaji da na zabbi da sauransu. Wannan karon har kajin gidan gona ishirin Malam ya ba su Hassan, amma an fige an gyara ya kuma ba Haydar takwaransa dan maraki, Abba ya ce a bar shi a nan a kiwata masa. Ni da su Azizah bamu so rabuwa ba, don dai ina son samun lokaci da Innana ne su kuma sun kallafa ran su a son zuwa Porthearcourt, akwai tambayoyi da dama da nake son in yiwa inna, musamman a kan irin gore-goren da su Hassan ke mani a shekarun baya, wanda wancan lokacin karancin shekaru da rashin wadatar hankali bai barni na kuma waiwayarsu ba, sai yanzu da hankali ya zo mini nake ganin hakan tamkar wani barazana ne ga mutuncina a nan gaba. Mun kwanta ne da daddare, sauro ya gallabe mu, duk kuwa da maganin sauron da muka kunna da (Rambo) da na fesa, amma ni ko jin cizon suron bana yi balle in sosa, abubuwa ne da yawa ke damuna a zuci. Wurin karfe daya na dare na ja tsuka “Tsut!” don tuno shekarun baya. Ashe Inna Rabi barcinta ba wani nisa ya yi ba, ta ce, “Ke in wani abu ne ya dame ki, ba kya gaya mun? Haka kawai ki bi ki isheni da tsaki cikin dare”. Maimakon in amsa mata sai tsakin ne (by mistake) ya sake subutowa daga bakina, na ce, “Kai abin ne ma Inna na kasa ganewa wallahi”. Ta ce, “Can gidan Baba Sa’idun naki, fi sauran-Babanni ne kike da matsala ko-ko satittikan da za ki yi mana ne kike ganin kyashin su, kin baro A/C sauro na cizon ki? Abin da na guda kenan ai tun farko Kyauta na hana tafiyar ki hannun su Azumi, amma Malam bai saurare ni ba, saboda dukkanku baku dauke ni a cikakkar mai hankali ba sai SA’IDU. Sa’idu ya fini GIRMA a idanun ku, komi Sa’idu ya ce shine dai-dai, amma Rabi ai MAHAUKACIYA ce…..” Wasu hawaye suka balle min, na ce cikin rishin kuka, “Ki daina gaya min haka Inna, wallahi-wallahi a kowanne hali, a kowanne matsayi babu inda ya fiye mun dakin nan naki kwanciyar hankali. Babu inda nake ji na sake, freely, cikin walwala da kwanciyar hankali tamkar nan. Bani da wanda ya fiki, bani da wanda nake so fiye dake. Baba Sa’idu bai taba daukar ki matsayin maras hankali ba, ke ce dai kike zaton haka. Ya sha cewa inda mai hankali a duniya to ke ce, in da wanda zan dage wurin bin maganarsa to ke ce, in da wanda ta san ciwon kanta a duniya to ke ce. Abin da ke damuna kwata-kwata bai shafi abin da ke kike tunani ba. So nake in tambaye ki ashe mu ba Fulanin Gwarzo bane? Kuma meye BARAROJI? Mene ne SADAKA-YALLAH?????” Inna Rabi ta mike zaune a nutse ta yi murmushi. Ta mika hannu ta latsa makunun wutar lantarki dakin ya gauraye da haske, iare-iren wadannan gorarrakin ita ma ta sha su wurin kishiyoyinta a zamanin kuruciyar ta, ta kuma tabbata watan-watarana za a yiwa Abun ta. To amma ba ta zaci tun yanzu ba, ta dauka sai a gidan aure ko lokacin aure. Ba ta san daga inda ya fara fitowa ba, don haka ta ce, “Shin wa ke ce da ke hakan a gidan Sa’idu?” Na ce, “Maganar fa ba ta yau ba, tun farkon zamana dasu ne. kuma tun lokacin Baba ya saba musu basu sake ba. Ita Hajiyar ma yanzu ba ta shiga harkata kowa zaman kansa yake a gidan, babu mai shiga shirgin wani. Ita Hajiya Sa’a ta gayawa su Hassan suka samin kahon zuka a wancan lokacin, wai suna kyankyami na saboda mu BUZAYE ne, kazame. Su tofar da miyau, suyi amai wai BARAROJI babu wanda ya kaimu kazanta. Sai nake jin tsoron ko wani ciwo ne hakan abin kyama”. Inna Rabi ta hasala ta ce, “Ita Sa’ar har tana da bakin gaya mun haka? Tana da bakin ce dake SADAKA-YALLAH ba ta fadin babban? Koma meye ta ce a yanzu ai duniya ce, ita din kuma makaranta ce babu abin da ba za ka gani a cikin ta ba. Wanda bai zo ba ma tana nan tana jiran, kuma tarihi MAIMAITA KANSA yake, sannan kowa ya kwana lafiya shi ya so. Idan a yau na ga dama wallahi ba za ta kara jin dadi a rayuwarta ba, daga ita har Sa’idun da take takama da shi, domin GIRMANSU YANA HANNUNA, yau ne ko gobe in na ga dama sai in FADAR DA SHI, in ga karshen kudi da boko, wadanda basu da amfani idan babu mutunci a idon duniya. To amma ba zan yi hakan ba saboda wasu manyan dalilai, akwai ranar da dubunta za ta cika. Tara su nake daga ita har Sa’idun ina jiran ranar da wani a cikinsu zai wulakantaki, ina jiran ranar da zai nuna fifiko tsakaninki da ‘ya’yansa….” Sai kuma ta razana da ta fuskanci ko da wa take magana, Zaynabu ce ba Au ba, da cikakkar budurwa mai hankali take magana ba Kyauta-Abun d ata sani a baya ba ce,. Ta yi hanzarin gyara zancenta da cewar, “Zaynab mu ba Bararoji bane. Sune ‘yan kasarmu dake daji, mu ‘yan kasar Niger ne ‘yan uslin wani gari DAMAGARAM, amma iyayenmu da ‘yan’uwanmu duk a babban birnin Yamai (Niamey) suke zaune, har yanzu suna can. Mahaifinmu fitaccen dan kasuwar fata ne da ya yi fice a Niger, kuma mashahurin dan siyasa ne da ya rike mukamai da dama a gwamnatin Damagaram, wanda gab da rasuwarshi yake dan takara mafi rinjayen magoya baya da suka tsaya neman kujerar gwamnatin Damaragam. Duk dangina suna Niamey, ba fakiri ko daya, bamu taba yin talauci a rayuwarmu ba, bamu san shi ba ni da iyaye da dangi na gaba daya. Kaddarar aure da rabon haihuwar ki ya kawo mu Najeriya mu da mahaifinmu da kanwata NURATU da ta bata a hanuna. Batan Nuratu ne ya hanani komawa gida, ya hanani neman dangina har yau don ban san me zan ce musu a kanta ba, kuma rashinta ne ya tsomani a halin da har yau kike ganina a ciki ake min kallon MAHAUKACIYA ko TABABBIYA. Su kuma danginmu basu san inda muke ba, don mahaifinmu rasuwa ya yi a sanadiyyar hadarin jirgi a kan hanyarshi ta komawa gida, ya gaya masu cewar ya aurar dani ba da saninsu ba. Ki taya ni addu’a Allah ya bayyana min
Chapter 22 · 0% Book details