← Book details Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 24

Sashe 19

Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ban sake dagowa ba. Ya daka mana tsawar da ta firgitamu ya ce, “Da Allah malamai za ku shigo ne ko kuwa mu juya ku kwana a makarantar, ruwan wa? ‘Yan kauye kawai kun saki manyan bakunan ku kuna kallon mutane kamar baku taba shiga mota ba a duniya…” Faruk ya katse shi da cewa, “Haba babban Yaya ayi musu a hankali man da me za su ji? Da yunwar dake damun su ko da shanya sun da aka yi kamar kayan wanki, ko-ko da fadan ka kamar barkono bayan basu suka kar zomon ba….?” Ya ja tsaki “Tsut-tsut!” Kamar ya ci kansa don bala’i. Mu dai tuni mun nabba’a a bayan mota babu wadda tai magana, ya fizgi motar da gudun ta mai kamar na tashi sama, kan ka ce meye wannan sai gamu a gida. Kamin mu fita Ya Faruq ya dubi Azizah ya ce, “Ya ya ne Azzy, na ga mutuniyar tawa ba yada take?” Azizah ta dan saki ranta ta jinjina kai ta ce, “Kai dai bari Ya Faruq, wani mugun malami ne Allah ya hadata da shi yau ya zane ta ya sata kneel down a cikin rana wajen awa daya wallahi”. Iftihal ta ce, “Kai ina jin ba zane ta ya yi ba, wankin kashi ya sa ta. Baki ji ba yana cewa ya za ta shigo mana aji tana warin kashi?’ Haushin su ya ishe ni na bude motar fit na fice kamar guguwa, Faruq yana danne dariyar sa ya ce, “Asshah! Abu bai yi dadi ba, galleliyar yarinya kamar Abu na a ce an sata wankin kashi?” Imran ya daga murya da karfi yadda zan jiyo yana cewa, “Ai madallah, kai madallah, wannan malami ya burgeni. Yanzu haka ba ta karatu sai SOYAYYAH! Ai ni wallahi ya yi min dai-dai, da zan ganshi da na sa Abba yasa an kara mai girma zuwa principal din F.G.C baki daya. Me ake da yaron da ba zai tsaya ya yi karatu ba? Kuma ku shiga taitayinku wallahi don gobe insha Allahu zan je na neme shi mu kulla abota, in ba shi izinin duk wadda ta ki tsayawa ta yi karatu ya ba ta aikin kashi….” Ni dai ban juyo ba sai kuka nake, sai Faruq dake ta shan dariya kamar me. Su Iftihal duk a kumbure suntum suka fito cikin dana-sanin da basu gaya musu ba. Wannan wulakancin da Imran ya yi mani, idan da zuciyata mai hankali ce da ya isa a ce ta saduda ta fidda shi a cikin ta da duk wani al’amari da ya shafe shi. Amma ina! Abu kullum kamar ana kara iza shi. Tun daga lokacin ya daina kaf-kaf din da yake dani ya koma treating dina yadda yake horas da su Azizah. Duk wani wasa da shakuwa dake tsakaninmu ya janye shi, kullum sai fada kamar Babana. Kai ni ko Babana bai taba yi min bala’I da sababi irin na Imran ba, da abin da ya isa da wanda bai isa ba, haka takurar da yakewa su Azizah ya kara ninkata. Ya hana mu kallon talabijin balle kallon fina-finan India wai mun fara lalacewa. Su Azizah da basu san hawa ba basu san sauka ba mamakin su ya kasa boyuwa, suka kai karar shi wajen Abba kan ya takura mana ko music ya hana mu ji a radio wai duk a nan muke debo lalata. Ya sayo kasusuwan kira’ar Jabir ya rika sanyawa duk gidan. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Na runtse idanuna da karfi, wani sanyi ya ratsa zuciyata tare da yin wata irin kakkarfar ajiyar zuciya, amma na kasa bude idon. Babu shakka Ya Im ya yi min bazata, ya shammace ni ya kuma gigita ni. Na rasa da idanun da zan bude in dubi su Azizah. Wata irin kunya da nauyin su da ban taba ji ba suka taru suka yi min mayafi, na bushe a zaunen da nake. Su Iftihal kan su bushewar suka yi, kamar sassakakkun gumaka. Cikin mu babu wanda ya san fitar shi, sai bude ido mu kai muka ganmu a cikin mota, direba ya ja, ko uffan babu wadda ta yi kokarin cewa a cikinmu. Sai me? Mun fito break kenan muka ga motar Ya Im a kofar ofishin principal, aka aika in zo, wani irin kululuuu! Da cikina ya bayar ban san sanda na tsugunne a kasa ba na dafe cikina dake hargagi, ita kanta Iftihal a tsorace take, don dukkan mu munyi tsammanin karar Malaman mu ya kawo da Azizah ta ce suna bamu amsa. Na shiga na tarar ashe ba a nan gizo ke sakar ba, zuwa ya yi a kan makarantar ta yi mun iyaka da su GG da ke cewa suna so na, domin ni matar shi ce an daura mana aure tuntuni. In ka kalli fuskar nan mai bam sha’awa ta Ya Im, ta juye gaba daya da harbadadden kishi zuwa na wani mutum daban mai zuciya da razanarwa. Na yi hanzarin daga ido na dube shi, in tambaye shi dalilin shi na yi mun haka? Wata uwar harara da ya jefe ni da ita ba shiri na dukar da kaina kasa na mai da bakina na dinke na kasa cewa komai. Principal ya ba shi hakuri, ya kuma tabbatar mishi za a tsawatar don wannan dokar makaranta ce dama. Shi kuwa GG anyi neman duniya cikin makarantar ba a ganshi ba ya gudu, tunda ya ga motar Ya Im ya tsere don bai san yau da wacce ya zo ba. Na cika na yi famfam na fito ina hada hanya saboda takaici, wai me Imran ke nufi dani ne? Ya hana mun kurbar ruwa a duniya ko me? Saboda kawai ina zaman cin arziki a gidansu? Ya sanya ni cikin wani hali na matukar kunyar su Azizah, ban fita daga wannan ba ya zo ya lankaya min auren da Allah bai lankaya min ba. Inda na gode Allah daga Azizah har Iftihal babu wanda ta yi mun tambaya ko daya, domin dai su yara ne nutsattsu kuma wayayyu da basu faya mai da hankali a kan abin da bai shafe su ba. Na dawo gida ina ta fushi, da dare kowa yana falo amma ni na kasa fita, gani nake kamar su Azizah za su fadawa kowa abin da ke tsakanina da Yayan su, na ji ni duk na zama wata bare mara gaskiya kuma munafuka, ban san sanda hawaye ya zubo min ba, nasa bayan hannuna ina sharewa duk da haka Imran na nan like a zuciyata, haka komi da yake yi bayan bani haushi illa wannan abu da ya yi mun cikin su Azizah da ya hanani kurbar ruwa cikin gidan gaba daya, duk da na san ba halayyarsu ba ce fadar abin da ba a tambaye su ba. Shi din ne dai ya shigo Iftihal na biye da shi, ya ce, “Kin gani ko abin da na gaya miki, saboda na ce ina sonta a gabanku ta bi ta kuntatawa kanta ta hana kanta sakat, nima ta hana mini. Tunda na zo gidan nan Iftihal Antin nan naki ba ta barni na huta ba, sai garani take kamar gare-gare ko kuwa juyani ya waina a tanda. Ban san me take nufi ba, ban san me take so in mata ba da zai nuna ni Imran mai so da kaunar ta ne. na yi duk iya kokari na ta saurare ni ta kiya, wayar da na kawo dominta ta rufe ta toshe duk wata kafa da zan bi in nuna mata manufata ta alkhairi ce a tare da ita”. Ya samu gefen gadon da nake zaune ya zauna, ya kai hannu ya dago habana ya ga yadda hawaye ke ta gudu, ya ce, “Jibi ki ga Iftihal, shin dama kaunar da kuke wa Anti-Abun na karya ne, da take shakkar ku? Saboda ni dai na san in dai so ne Zaynab na sona, ba tun yau ba, tun sanda ta fara kirgen dangi take sona balle yanzun? Dama so nake ku yi karatu kuma an kare, ba sai aure ba Iftihal? Yau shekaru dai-dai har uku ina rainon Zaynab a cikin raina, ina addu’ar Allah ya bani tsawon ran da zan ga karewar karatun ku, in fiddo burin zuciyata na son mallakar ta. Ki taya ni rokon Zaynab ta amshi kokon bara ta ko na samu nutsuwa, ita ma ta samu damar karasa jarrabawar ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Amma meye amfanin wannan hali da take neman jefa kanta?” Na matsa can gefe na takure cike da wata sabuwar kunyar, kamar in daura hannu aka in ce “Wayyo Allah!” Iftihal ta yi tsaki ta ce, “Kema dai don Allah Anti Abu meye haka kike yi sai ka ce wata Illiterate (jahila), mu fa ba tun yau ba mun san Ya Im na son ki, har amanarki yake bamu in zai tafi to meye wannan mummuken da kike mana sai ka ce baki yarda damu ba? Kina tsammanin zamu so Ya Im ya auri wata fiye da ke ne? Kin yi kuskure. Ko ita Azizah da take yawan yi miki zancen Mami ina tabbatar miki don kawai ta ga hawayen ki ne da kukan da kike mana cikin dare, kin dauka barci muke?” Ta fita tana dariya. Na juya na harari Ya Im da idanuwana da suka kada suka yi jawur, ya rausayar da kai cikin yi min wani lallausan kallo mai nuna yes, abin da yake fadi da wanda ‘yar’uwarshi ke fadi haka yake har zuciyarsu. Cikin kuka na ce, “Don Allah mai yasa ka yi mun haka? Ni da bakina kataba jin na ce ina son ka? Wannan ma ai sharri ne kuma wallahi sai Allah ya saka mini…..” Dariya na ba shi sosai. Ya ce, “Kina bani mamaki Zaynab, abin da baki sani ba shine, duk wani motsinki a tafin hannuna yake. Kuma tun baki da wayo nake da wayo. Maganar kina sona ko bakya sona duk a barta, na ji ni nake son ki, kuma a yau na furta. Amincewar ki kawai nake nema ba wani abu daban ba, ina fatan ranar da kuka kare jarrabawa ranar ne za a daura mana aure, don ba zan koma ko ina ba Zaynab sai tare da ke a matsayin matata (by my side) Insha Allahu.
Chapter 19 · 0% Book details