Sashe 17
Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba. Sharewa ya yi ya bagarar ta hanyar yin zaman direshan a gabana bisa carpet, yayin da ni nake zaune a gefen gado na zubo fararen kafafuna kasa, na tokare gefe da gefena da hannaye na biyu. Imran ya sunkuyo ya leka fuskata muka hada ido, ya sakar mun lallausar murmushinsa cikin son ganin na saki jiki na daina jin kunyar tasa. Na sanya tafukana na rufe fuska ina murmushi. Ya ce, “ZAY-NA-B”. Yadda ya kirayi sunan sai da tsigar jikina gaba daya ya kara tashi, ban iya na amsa ba. Ya ce, “Maza sauke hannuwanki daga fuskarki, kada ki sa in taba su”. Da sauri na sauke amma har yanzu ban bari mun hada kwayar ido ba. Ya ce, “Na ce ki gaya mun ciwon da ke damun ki, a kalla idan ban baki maganin sa ba zan baki shawara a matsayina na babba wanda ya fi ki shekaru. Idan kin barshi a ranki kin ki fadi, mai yiwuwa ne ya ci gaba da cutar dake ba tare da kowa ya sani ba, wanda a karshe hakan zai iya zamowa illa ga lafiyarki”. Ya yi shiru yana mai kokarin son mu hada ido amma na ki. Na yi tunanin dukkanin maganganun shi a kan hanya suke, ba wadda babu gaskiya a ciki. Don in ban mance ba Baba Sa’idu ma ya sha gargadi na a kan barin sanya abu a rai illa ne ga lafiya da kwakwalwa. To amma ni kaina wallahi ba na ce ga hakikanin abin da ke damuna ba, abin ya fi karfin bayyanuwa, ya fi karfin kwatance, ya fi karfin duk kokarin harshe na ya fassara shi. Unxpressable feeling kadai zan iya kiran al’amarina. Wanda in ban da ni da zuciyata da kuma Ubangijin da ya assasa mani shi a ruhi da gangar jiki, babu wanda ya san iyakar sa. Abin da na sani kawai shine, “I need Imran! I need Imran!! I need Imran a tare dani”. To amma idan na fadi mishi ai kamar na zubar da mutuncin kaina ne, na zubar da tarbiyyar gidanmu, duk da ban san wannan abun mene ne ba? Na san ba abun kirki bane, haka ba abin alheri bane kamar yadda ya fada mani. Don haka na kasa magana, tunda na fara tunanina bai katse ni ba. Ya yi nacin ya yi juyin duniyar nan amma na ki magana har ya gaji ya zuba mun ido da alamun ranshi ya baci, duk kuma sai na ji babu dadi. Wasu hawaye suka zubo min na sanya bayan hannuna ina sharewa. Ya mike zai fita ba tare da ya ce dani komi ba, har ya kai bakin kofa ba tare da ya juyo ba, ban san sanda na samu kaina ina mai cewa cikin rishin kuka “Ka yi hakuri Ya Im, mara ta ce take ciwo!”. Ya juyo a hankalce ya dawo, hannayenshi duka biyu cikin aljihunshi, ya dube ni sosai, na nutsar da kaina kas, kamar in ce, “Wayyo Allah!” Ya fi mintuna biyar yana kallo na kamin ya ce, “Al’ada kike yi ne ko zaki yi Zaynab?’ Da wata muhimmiyar kunya da haushin kaina mai tsanani suka taso suka kara lullube ni ban san sanda na fashe da kuka ba, yau tozarcin duniya na gama jin shi a rayuwata, da wanne ido zan daga in kuma duban Ya Im? Na wulakanta kaina na tozarta kaina na yi abin kunya. Imran ya ce dani kamar cikin tsawa, “Ba tambayar ki nake ba za ki sakar min sauti sai kin tara mana mutane a ka?” Na hadiye kukan gaba daya ji kake “mukut”, sai hadiyar rai nake tare da fyace majina da bakin dankwalina. Ya sake maimaita tambayar sa, wannan karon babu alamun wasa cikin maganarshi. Jikina na karkarwa na ce da shi, “A’a, ban ma jima da gamawa ba”. Ya yi ajiyar zuciya ya sassauta murya ya ce, “To meye abin kuka? Daga na tambaye ki don in san maganin da ya dace in amso miki sai ki bare baki ki fasa min kuka a zaci ma wani mugun abu nake miki, yanzu idan su Azizah suka zo suka ga irin wannan kukan da kike kamar na fitar rai suka tambaye ki me za ki ce musu? Maza share hawayen nan ki mai da mood din ki, mu yi karatun tun ban sa kafar wando daya dake ba”. Na koma cikin nutsuwata, na share fuskata tas na dauko littafin na budo mishi aikin. Ya zauna gefena yana dubawa, ya ce, “An excellent handwriting! Zaynab haka kika iya rubutu?” Sai yanzu ne na yi murmushi, domin dai ni mutum ce mai son yin abin yabo a yaba mani, yana kara (encouraging) dina. Cikin dan lokaci Ya Im ya fahimtar dani abin da na kasa har ma da abin da ban sani ba, da dabarun cimma nasara a darasin ‘Physics’ da muke cin kwakwa a kan shi ni da su Azizah. Ji na yi in zamu kwana muna karatun ba zan gaji ba, don kuwa Imran ba dai hikimar koyarwa ba. Imran S. Bindawa cool ne, reserve! Ga wani lafiyayyen kamshi da ban taba jiba dake fita bakinsa (Albaan mouth-fresh) in yana magana. Sai nake tambayar kaina dama akwai wadanda Allah ya halitta da kamshin baki ne? Ko da yake in ban manta ba ai Iftihal ta ce Yayanta daban yake a cikin al’umma. A haka su Azizah suka shigo kwanciya suka tadda mu, karfe goma sha daya da rabi na dare, don su tuni har sun yi barci a falon taso su aka yi. Suka saki baki galala! Suna kallon mu don basu zaci har lokacin yana nan ba. To shi kuma sai ya bi duk ya daure fuska, ya buga musu tsawa ya ce duk su dauko nasu littafin. A take kowacce ta shiga taitayinta barci ya nemi inda ya fito. Karatu ya dawo sabo, ya hadamu gaba daya yana koya mana, bai kyale mu ba sai da ya tabbatar mun gane, ya bamu aiki muka gwada mai a kan idonshi ya gani, sannan ya fita ya ja mana kofa, ko kallon mu bai kara yi ba. Azizah tana ta korafin ita dai da Abba bai ce Imran ya koya min karatu ba, gashi nan yanzu ya jawo mana masifa sai ya mai damu wasu alhuda-huda, su kam sun shiga uku kenan. Iftihal dake ta fi kowa son Ya Im cikin gidan ta ce, “Ai ba zama zai yi ba, baki ji Abba ya samo masu aiki ba? Yanzu haka next week in ya tafi duk da fadan shi ke da kanki za ki yi kewar shi”. Sai na ji duk hankalina ya tashi, Imran zai tafi aiki, ina? Ni kuma ina zan sanya rayuwata? Kasancewana tare da shi a yau na wani lokaci mai tsawo, ya kawo sauki 50% cikin ciwon zuciya da gangar jikina, ya wanke wani babban kaso na ciwon shi dake damuna, ya kuma kara gina wani makeken al’amarin da ya wuce na jin shi a gangar jiki kadai, maimakon haka, sai ya shigo har cikin bargo da kasusuwana. Ni kaina na san yau idan na ce idanuwana sun ga barci, to wannan karya ne. cikin kowanne juyina IMRAN ne, cikin kowanne kiftawar ido IMRAN ne, cikin kowanne zama da tashi IMRAN ne, cikin kowanne kwanciya da mikewar kafa IMRAN ne, cikin kowanne mafarki da ido biyuna shi din ne dai kadai ya mamaye, ya babbake yayi babakere a ko ina, bai barni da ko sako daya da zan sanya tunanin kaina ba. Da safe na sanya (uniform) dina cikin sauri ne saboda makarar da na yi, su Azizah tuni sun gama suna diniing suna karyawa, wannan ya samo asali ne da rashin isasshen barcin da na samu daren jiya, bayan sallar asubahi kuma wani nannauyan wahalallen barci ya yi awon gaba dani mai cike da mafarkai na ni da Y Im cikin wata irin rayuwa mai dadi, da kyar Mama ta tashe ni. Na ja cambas na daura na juya a hankali ina kallon kaina a mudubi. Ban yi mamakin ‘yar zabgewar da na yi ba cikin ‘yan kwanakin nan da duniyar Imran ta sanya ni gaba. Banda su Azizah shiriritattu ne ya dace su fahimto sauyuka da dama a tare dani, to ita kanta Mamar su haka take, ko cikin dare ba ta rabo da call na emergency case, don haka ba ta samun nutsuwar da har za ta fuskanci kananun abubuwa kamar wannan. Na ci gaba da kallon kaina cikin mudubin, ba wata kwalliya na yi ba ban da mai da farar powder da na shafa, amma ni kaina ina alfahari da ‘yar zagayayyar kayatattar fuskata, wadda in ba son kai irin na dan adam ba, zan iya cewa alhamdulillahi, babu abin da Allah subhana bai kawatata da shi ba. Fararen idanu, giran ido kakkaura, dogon hanci da tsararren baki mai daukar hankali. Idan kuma aka yi maganar zubin halitta abin sai shukrah ga Maqagina, domin ko yaro dan shekaru biyar ba zai iya yi min kallo daya bai maimaita ba. Farina kuwa ba fari ne sol ba, ja ce ni kalar uslin Abzinawa na Damagaram. Ko a farce ba za ka ce na hada jini da Bahaushe ba, domin komi nawa har yatsun kafata irin na Inna na Rabi ne. Na dauki jakata (school bag) na rataya a kafadar hagu, nasa kai zan fita, Imran na sawo kai zai shigo sai muka yi karo garam, da goshinmu, kasancewar nima ba baya ba ce wurin tsawo zamu yi kafada da Imran, illa ya nuna min kaurin jiki. Na yi saurin ja da baya ina ta faman ba shi hakuri don ni har ga Allah ban ji tahowar shi ba, kasancewar shi mutum mai nutsatstsen taku, duk na gigice saboda yadda ya yi min jiya na dan fara shakkun sa, da alama dariya na ba shi. Ya ce, “Ni ne mai ba da hakuri Zaynab, kin kwana lafiya?” Kalaman shi sun matukar bani haushi, wannan rainin hankali ne, kuma kamar son jin halin da mutum ke ciki ne, wanda shi din ba zai maganta mini ba, ba sai ya kyale ni in ji da ciwona ni kadai ba? “Don haka maganar na kwana lafiya ko ban kwana lafiya ba, ba damuwar ka bane….” Magana nake a zuci, ban san cewa har ta