Sashe 11
Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Ta yi shiru na lokaci mai tsawo, na dauka zagina za ta yi ko ta rufeni da duka, ko me ta tuna? Sai ta yi ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, “Ki yi hakuri Kyauta, ban sani ba na hade miki, amma gobe ba zan kuma ba”.
Muka koma barci, amma har garin Allah ya waye idanuna basu rintsa ba, zuciyata ba ta bar tukuki ba, haka ban bar yin nannauyar ajiyar zuciya ba, yadda na ga rana haka na ga dare, na kuma tabbata ita ma Innar ba ta yi baccin ba sai juyi a kan gado.
Kwanaki biyar da yin hakan, ina durkushe a bakin ramin da na haka don wanke allona a ciki, misalin karfe biyar na yamma, allo na nake wankewa don shiga sabuwar sura. A gefe toka ce a cikin dan kokon ludayin duma da zan shafe allon da ita kamin in sake yarfa wani sabon rubutun.
Ina diban ruwa daga cikin kwarya ina wanke allon a hankali tamkar mai wanke jariri, na tallabeshi da hannuna na hagu cike da tunanin Ya Faruk dake Sokoto, kowacce wainar yake toyawa?
Na yi murmushi ni kadai a raina ina kwatanta Ya Faruk a cikin babbar makaranta, na tabbata nan ba da jimawa ba zai bada mamaki.
Domin ko da nike yarinya kankanuwa ‘yar kimanin shekaru goma sha biyu, na san samun maza irin Yayana, ba abu ne mai sauki ba.
Faruk ko a cikin tsararrakin shi daban ne a komai, haka yake da aji na musamman, sannan jarumi ne ko ta yawan kunyaryakin da yake nomewa Malam, wanda aiki ne da almajirai goma majiya karfi ke yi. Shi ba wani mugun kyakkyawa bane amma namiji ne ta kowanne fanni, kuma baiwarwakin da Allah yai mishi suna da yawa, har ba zan iya lissafasu ba. Kasancewar shi da namiji guda daya amma Malam bai taba takaicin rashin ‘ya’ya ba. Ya kan ce,
“Faruk daya ne tamkar da goma!
Da haihuwar yuyuyu, gara daya kwakkwara, ta kowanne fanni yana alfahari da Umar-Faruk….!!
Ban ji karar (horn) din mota ba ko kadan, nayi nisa a cikin tunanina, illa takun Baba Sa’idu na GIRMA da nutsuwa, da ya bakunci kunnuwana. Yana kwarara mana sallama da wankakkiyar muryarsa tamkar wani balaraben Madina, saboda yadda muryar shi ke fita tar-tar.
Ita kanta Inna Rabi na san ba ta zaci zuwansa a wannan lokacin ba, kasancewar ranar Juma’a ce ba Asabar din karshen wata da ya saba zuwa ba, wannan tabbas ne, da tun kan ya shigo ta shige dakinta ta rufe.
Da na wulwula allon na yar sai a kan gadon bayan Inna Rabi dake gefe tana barar gyadar miya, ji kake tim! Ba kuma tare da na san aika-aikar da na aikata ba na yi tsalle na rikeshi ina “Oyoyo Babana!”
Mikewa daya Inna Rabi ta yi sai ji na yi tana fizgata tana cewa, “Gafara ki bawa mutane wuri”. Shi kuma cikin ladabi ya russuna rike dani tamau yana “Allah ya baku hakuri Inna, Inna Allah ya huci zuciyarku”.
Ta ce, “Sakar min ‘yata na ce Sa’idu, na yi ma kama da wadanda kudi ke rudinsu, a yaudare su? Da zuciyar ba ta huce ba da na kawo yau ne?”
Kanshi a duke, cikin tsananin girmamawa da kaskantar da kai, ya ce,
“Bani da kudin da za na yaudareku dasu Inna!!!
Har gobe ni almajirinku ne dake neman albarkarku, dake neman abin da za ya sanya a bakin salatinshi daga tukunyarku.
Hakurin nan nake dada badawa, wanda har abada ba zan daina ba, ko da yawun bakina zai kare.
Dukkanmu ‘yan Adam ne da bama sama da aikata KUSKURE, ‘yan adam ne da shaidan ya yi alkawarin janmu ga ba dai-dai ba, kamar yadda ya ja Ubanmu Annabi Adamu Alaihis Salamu. Amma da ya roki Ubangijinsa, sai ya yafe mishi bai barshi ya rafkana ba.
To Ubangiji ma kenan yana afuwa a garemu balle ku mutane?”
Ta fiddo fararen idanunta ta zube su a kanshi za ta fara lailayo ire-iren ashariyar da ta ke narka mishi kenan Malam ya shigo gidan rike da tazbaha yana ja, ya ce,
“Subhanallahi! Rabi’atu meye haka? Me zan gani haka? Saketa mana, karyata za ku yi?”
Ni kam sai kuka nake ganin Baba Sa’idu yana kuka, abinda ban taba gani ba. Ta sake ni bayan ta ja wani mikakken tsaki da wasu dunkulallun hawaye da suka biyo kumatunta, ta shige dakinta. Bammm! Ta danno kofa, muna ji bayan sakata da ta sanya har kuba tasa ta kara kulle dakin. Allah kadai ya san halin da take ciki a yau.
Haka ya ci gaba da durkuson bai dago ba. Malam ya samu wuri ya zauna yace,
“Sa’idu lokaci ya yi da kai da Rabi za ku fuskanci gaskiya, ku daina aiki da karya, lokaci ya yi da za ku fuskanci abin da ya dace, wannan rayuwar ina za ta kaimu? Meye amfaninta?”
Ya dago ya dubeni yana murmushi. “Yanzu cikata in aike ta tukunna”. Baba Sa’idu ya cikani, ba tare da ya dago ya dubi Malam ba. Ya ce, “Maza Zaynabu-Abu a samowa Sa’idu ruwa a randar Inna Dubu”.
Na ruga da gudu dakin Inna Dubu amma kamin in shiga sai da na rabe na share hawayen idanuna. Na ce, “Inna kawo sabon kwanon shan ki a bawa Baba Sa’idu ruwan randarki”.
Ta ce, “Abulle ‘yar gidan Sa’idu, ko dai kema can Sokoton za ki bisu ne wajen Yayanki?” Na yi murmushi domin ta yi mun susa a inda ke min kaikayi, na ce,
“Ai kema kin san Inna ba za ta bari ba.
Tun yaushe Baba Sa’idu ke cewa in bishi muje Sokoto a sani a makarantar su Iftihal, in na fadawa Inna tasa ludayi ta bubbuge min baki”.
Ko kamin na iso sun gama maganar Innana sun koma ta karatun Faruk da amfanin gonar Baba Sa’idu dake nan Gwarzo. Isowana duk suka maido hankulansu gareni suna min murmushin su mai cike da kauna. Tsakanin Malam da Baba Sa’idu na kasa tantance wanda ya fi kaunata, dukkaninsu abu daya nake gani cikin kwayar idanunsu tun ina jaririya.
Na russuna na mika mishi ruwan randar Inna Dubu, garai-garai da shi, ga sanyi kamar na firinji, duk gidan shi muke sha, abin kamar karama, ruwan randar Innar Ya Faruk ya fi na randar kowa sanyi, gardi da ratsa zuciya. Don haka ne kowa ya zo cewa yake a debo mishi ruwan randar Inna babba, ban da Ya Faruk mai son na Inna Rabi.
Ya kan ce shi ta fi mishi ta kowa sanyi, duk da a zahiri ba hakan bane, illa kasancewar shi wani mutum mai son faranta mata a koyaushe, da kokarinsa na gusar mata da bakin cikin dake damun zuciyarta, amma duka a banza, wai kirari a gidan kurame.
Baba Sa’idu ya ce,
“To Zaynabu ni za ni koma, yau ban kawo miki komai ba saboda nima tafiyar ban shirya mata ba. Na je taron ‘convocation ’ ne a nan cikin Jami’ar Bayero, na ga don me zan koma ban biyo ba tunda gani a cikin Kano?” Na ce,
“Babu komai Baba Sa’idu, Allah ya kaika lafiya”.
Ya ji dadin addu’ar da na yi mishi. Ya kamo hannuna ya ce, “To meye sakonki ga yayanki da su Aziza?” Na washe dukkan hakorana ina fara’a, don jin dadin ya tuna min da Ya Faruk wanda dama ke makale cikin raina.
Na ruga da gudu dakin Inna Dubu inda na boye kullin (awara da yaji) da Innar ta soya dazu, kasancewar shi mai son ta. Haka kawai yake sayo waken suya (soya-bean) ya kawowa Inna Rabi ya ce tayi mishi Awara, ya yi ta ci yana dangwala yaji yana santi. Wani zubin ya kan ce, “Amma dai ana hadawa da kwai ko Inna?” Sai ta yi murmushi ta ce, “Eh, ana hadawa amma kwan wake”.
Na dawo da gudu na kawo mishi, na ce, “Ka kai mishi wannan”. Bai damu da maikon da ya mamaye ledar ba ya karba ya sanya a aljihun farar sassalkar shaddar dake jikinshi da a kalla ta ba naira dubu talatin baya. Ya ce, “To ina na su Aziza?”
Na sunkuyar da kai ina murmushi na ce, “Ai basu sanni ba, kuma su ‘yan gayu ne basa cin awara”. Daga shi har Malam dariya na basu. Ya ce, “Wa ya gaya miki haka? Kada in kara jin haka, dake dasu duka daya kuke, sai ma ke da kika fisu. Ke da kike da haddar Izfi talatin a cikin kanki, su ko ko izfi biyu basu haddace ba, wawaye ne kurum! In zan dawo zan kawo miki su suyi sati tare da ke, ki dinga koya musu irin karatun nan naki mai dadin sauraro, mai kira’ar ‘yan Aljannah (warshu), kin ji Zaynabu?” Na ce, “Na ji Baba Sa’idu. Allah ya kaika lafiya”.
A ranar sai a dakin Inna Dubu na kwana, don Inna na har washegari ba ta bude kofar ba. Kayan abincin da Baba Sa’idu ya zo mana dasu su doya da dankali, da safe Inna Dubu ta kasa ta kaiwa kowacce kasonta kofar dakinta.
Inna na bude kofa ta ci karo da tsarabar Baba Sa’idu, ni kuma ina gefe ina rubutuna a allo da ban samu jiya na yi ba saboda zuwan Baba Sa’idu. Sai gani na yi ta samu fanteka tana jida tana fita dasu tana kaiwa almajirai. Tana dawowa ta hango katon din taliya da na kayan shayi a gefe, suma ta kinkima ta je soro ta rabar. Daga matan gidan har ni babu wanda ya yi mamaki, kamar yadda babu wanda ya daga ido ya dube ta, don in da sabo mun saba ganin abin da ya fi haka.
Akwai sanda ta zuba turamen Holland da ya kawo musu da sallah cikin masai, ta gidan gabadaya, ranar ne ta ga bacin ran Malam irin wanda ba ta taba gani ba, Inna Dubu ce ta gayamasa, yace,
“Wannan almubazzaranci ne, kuma masu almubazzaranci iyalan shedan ne. In bazata daura ba to ta bayar, amma ba za ayi wannan almubazzaranci a gidansa ba”.
A dan tsukin na dage da addu’ar Allah yasa in ci makarantar sakandiren da nake so wato GGSS Kabo, ba don komi ba sai don su Hafsisi ‘yar dakin Inna Dudu da Indo dake can aji biyu ‘yar dakin Inna Rakiya, mun shaku dasu sosai, musamman Hafsisi da take kusan tsarata, shekaru biyu kawai ta bani.
A satin Ya Faruk ya zo, amma ba jimawa zai yi ba don basu yi hutu ba. Na rasa inda zan sa raina in tsaida murnar, haka shima. Yayo min saye-saye masu yawa har da sabuwar jakar makaranta da wata na’ura mai koyar da harshen Turanci. Na ce,
“Ya Faruk ina ka sami kudi haka, kai da kake karatu?”
Ya ce, “Karatun ma ai don ku nake yin shi Kyauta, haka komi nawa naku ne. Kada ki damu da wannan alawus din dalibai ne da ire-iren kudin da Farfesa yake bamu ni da Imran wanda ni bana bukatarsu, saboda ci da shana da makwancina duk a gidansa yake.
Iyalin Farfesa mutane ne masu karamci da suka san hakkin dan adam, suna kyautata mani sosai, haka shima Abban komi bai banbanta ni da Imran”.
Na tambaye shi ko wane ne haka? Ya ce, “Shine babban dan Farfesa tare suke karatun. Ya ce, “Imran mutum ne mai kirki da dadin mu’amala, yana da saukin kai kamar Farfesa, I would like you to meet him even once (zan so kwarai watarana ki hadu da shi ko da sau daya ne). In kika zauna da shi wuni daya, za ki so ci gaba da zama da shi muddin rayuwarki”.