← Book details Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 24

Sashe 13

Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na sha kimantawa raina ko ya Imran yake? Yadda abin ya bayyana a gareni shine, duk gidan kowa na son Imran, babba da yaro kowa bakin shi baya daina ambaton (Ya Im) kamar yadda na ji suna kiran sunan a takaice. Na san zai zamo mai kyawun sura kamar su Hassan, mai kyan hali kamar Baba Sa’idu. Tun ban ganshi ba na san dole ganinsa ya fi jin sa. Iftihal kan ce;
“A duniya ba mutum irin Yayana Abu!”.
Na tambayi kaina mai yasa shi din suke son sa, basa son kannensa su Hassan? Me yasa zai kasance na daban din, kamar yadda suke ikirari? Abubuwa da yawa kan sa a so mutum, muhimmi shine halayensa. A ganina ni ya dace in fadi cewa ba mutum irin Yayana Faruq amma ba su ba.
Na kan so Ya Faruq in kaunace shi, kauna irin ta su Iftihal ga Yayansu, saboda halayensa. Faruq mutum ne mai tsarge gaskiya komi dacinta, ko da hakan na nufin ya bata maka ne, hakan ba zai dame shi ba in har ya gaya maka ita wannan gaskiyar. Ba ya shiga abin da ba ruwan shi, baya da karya, baya da daukar duniya da zafi.
Babban abin da yake burge ni da shi shine, addininshi da gudun sabon Allah, a ko da yaushe yana kokarin fin karfin zuciyarshi a kan abinda take so, musamman idan ya fahimci wannan abun ba alhairi bane a gare shi.
Idan kuwa aka juya ta bangaren halitta, to su Faruq sune ‘maza’ da za a kira su da wannan sunan suyi gaggawar amsawa a ko ina. Ga tsayi ga zati, irin wadanda kowacce mace za ta yiwa kanta burin mallakar su.
Tunda na taso a rayuwata bani da abin tsoro irin MAGE, na tsani mage, ina tsoron mage tun ina mitsitsiyata. Idan na ga mage na kan firgita ne ko in kwalla kara. Idan kuwa ta hada yankwalallen jikinta da nawa, na kan suma ne ko in fita hayyacina, in yi ta firgita a yayin barci. Wannan dalilin ne yasa duk son kiwon mage da Malam ke yi ya hukura.
Rannan muna dawowa makaranta a motar yara (school bus), dama kullum sai an fara dauko su Hassan da suke da nisa, sannan a biyo ta makarantar mu a debo mu. Mun dauko hanyar gida Hassan ya ce, “Wai Rufa’i baka san magen gidan su Na’im ta haifi ‘ya’ya har guda goma ba? Suna nan baka gani ba in suna boxing abin sha’awa”.
Jauhar ya ce, “To su sammana man ko guda uku ne muyi kiwon su?” Rufa’i ya ce, “Ka ga ko Hajiya na son missa, don da tana da (Laura) da ta mutu ne ba ta sake samun wata ba”. Hassan ya juya ya ce da direba, “Maza kamin mu shiga gida juya kaimu gidan su Na’im”. Tuni Shehu direba ya cika aikinsa.
Ban san sanda na fashe da kuka ba na ce, “Don Allah don Annabi Hassan kada ku amso ‘yar mussan nan”. Rufa’i ya ce, “To ‘yar iko da gidan Uban wasu, idan Malam mai almajirai ne ya sayi gidan sai ki hana mu zuba mage”. Hassan ya ce, “Bar ‘yar banza, mai bakin baki irin na karuwai. Tunda an hana mu ce da ke BARAROJI to SADAKA-YALLAH ce???
Suka bude motar da kafa fut! Suka shige gidan mataimakin Abban su. Basu dade ba sai ga kowanne dauke da farar babyn mage, in ban da mazari ba abinda jikina yake. Suna shigowa suka watso su jikina. Da na kwalla wata azababbiyar kara sai da suka razana dukkansu, na mimmike ba ko kwakkwaran motsi balle kyakkyawan numfashi.
Iftihal tasa kuka ta ce, “Ai ga shi nan kun kashe ta, wallahi sai na fadi ma Abba”. Shi kansa Shehu direba ya tsorata, ya ja motar da gudu yana cewa, “Ku dai Hassan baku da kirki wallahi”.
Yana sanya hancin motar cikin gate din dai-dai lokacin da Faruq ya yi parking karamar Honda Prelude ta Imran, suka fito a tare, dukkaninsu sanye da kanyan NYSC, bakin Abia, zuwan su garin kenan.
Azizah ce ta fara fitowa daga motar a rude tana kiran “Ya Im!”. Shi ko Faruq ido yake warawa ya ga bullowar Abun shi, ya ga wane GIRMA da wane irin kyau ta kara, wane irin sauyin rayuwa ta samu a tsayin lokacin da ya yi bai ganta ba?
Kullum, cikin sabani suke, sau tari duk sanda suka zo Sokoton daga Abia, wanda kwata-kwata ma zuwan su uku cikin shekara daya, za su tarar su kuma anyi musu hutu suna Gwarzo, sanda suke Gwarzon su kuma sun dawo Sokoto abin dai kamar shiri, amma ya faru ne cikin ikon Allah. Kuma gareni sai ya zamanto rayuwa da su Iftihal ya debe min kewar Faruq din kusan kashi saba’in cikin dari.
Azizah ke fadin “Ya Im, su Hassan sun zubawa Anti Abu mage ta sume mana a motar”. Gaba daya Imran da Faruq suka yo motar, Imran ya riga Faruq dauko ni. Wannan shine karo na farko da ya daura idanun shi a kan Abun-Faruq, Abun-Baba Sa’id.
Maimakon ya yi sauri, tafiya yake dauke da ita a hannun shi tamkar wanda ya taka kaya, ko ko wanda kwai ya fashewa a ciki. Ganin irin tafiyar da yake yi ne ta marasa kuzari ya sanya Faruq karbe Abun daga hannunshi zuwa dakin Mama. A ransa yana cewa,
“Ashe Imran duk wannan physique nashi ragon maza ne, mace wannan kamar ‘yar shilla ya kasa daukar ta”.
Mama ce ta yayyafa min ruwa na farfado tana shafa kaina tana zagin su Hassan kaman ta ci babu. Farfadowa na yi ina makyarkyata, hawaye na tsiyaya ta gefen idona, fadi nake ina maimaitawa, “Mage ce fa a cikin jikina Mama”. Ta aza kaina bisa cinyarta ta ce, “Ba wata mage, sai ni sai Ya Faruq, gashi nan ya zo”. Ni ko na dage, “Gata nan fa a hannun su Hassan har guda uku wallahi….”
A ranar dai daga ni har Mama da su Imran babu wanda ya kwanta da wuri, don da na rufe ido barcin ya fara fizgana zan farka a firgice ina kiran mage. Washegari Imran ya tattara magen ya sanya a buhu ya ba Shehu direba ya ce ya mai da inda suka karbo. Ai kuwa a ranar su Hassan sun sha tafka da belt, sunyi kuka da majina, daman Imran ba daga nan ba (very-disciplined-brother).
Duk hakan bai ishe shi ba sai da ya sanya su duka cikin store ya kulle, ya hana masu aiki basu abinci tun safe har yamma. Hajiya Sa’a ba ta san me ake yi ba sai yamma lis ta dawo aiki. Ta yi murna da zuwan Imranan ta da kammaluwar bautar kasar sa, suka barke da hirar yaushe gamo irin na Da da Uwa a babban falon ta.
Ta nemi su Hassan ta aika su kawo mai lemu, ya ce, “Ai suna (store) ya kulle su”. Ta ce, “Dalili?” Ya yi kwafa cikin takaicin su da ya ki sakin sa har zuwa lokacin, ya ce, “Sun san yarinyar nan ‘yar Malam ba ta son mage suka watsa mata maguna ta suma, har yanzu ba ta san inda kanta yake ba”.
Ga mamakin shi sai ta buga tsaki ta ce, “Shine me? Gidan Uban su ta zo, ban ga dalilin da za ta takura su ba ta hana su yin abin da suke so. In ba ta son magen ta koma gidan Ubanta mana? Sallamamme kawai ka san me ake a cikin gidan ne? A kan Buzuwar nan aurena da ubanka ya kusa mutuwa, da sai dai ka dawo ka nemo ni a kauyenmu, in baka sani ba in gaya maka dalilin cewa da ya yi in tafi kenan kwanakin baya da na gaya maka a waya don sun ce da ita BARAROJI, ko ka bude min yara yanzu-yanzun nan ko in sabar maka wallahi”.
Ba musu Imran ya bude su Hassan domin dai shi mutum ne mai biyayya da baya saba umarnin iyayen shi ko ya ya ne. Ya samu Faruq a dakinsu yana cin abinci, ya zauna bakin gado ya dafe kai ya rasa abin da ke mai dadi, anjima kadan ya yi tsaki ya girgiza kai duk sai ya ba Faruq dariya.
Ya ce, “Kai Imran ya ya za ka yi when you become a father? (in ka zama uba) baka san sha’anin yara bane?” Imran ya sake yin tsakin ya ce, “Ni ba wannan ke damuna ba, maganganun Hajiya ne ban ji dadinsu ba, ban gane inda ta dosa ba. Ita fa babba ce, da ya dace ta dauki kowa nata ne a gidan nan, duk da dai na san ita mai nuna son ‘ya’yanta ne, amma saboda Allah su Hassan basu yi laifin da suka cancanci a hukunta su ba?”
Faruq ya dafa kafadunshi cikin murmushi “Common dear, don’t talk about this matter again, plz…” Shima sai ya share zancen bai kuma yin shi da Faruq din ba, to amma sai ya rika jin nauyin Faruq din ta yadda zai ga mahaifiyarshi a matsayin maras tunani, ga Faruq din shi bai dauki al’amarin wani serious ba ma.
Kwana biyu na warware case din mage ya wuce, sai dai cike nake da tunanin mene ne BARAROJI mene ne SADAKA-YALLAH?
Wannan tambaya ce da ta dade tana cina a rai, na kuma rasa wanda zan yi mawa, don haka da na ga abin ya fi karfin tunanina, dole na yakice shi karfi da yaji.
Chapter 13 · 0% Book details