Sashe 10
Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da alama Malam bai san idanuna biyu ba. Ya ce, “Rabi’atu na zo miki da umarni ne ba yardarki nake nema ba. Ki yi duba izuwa rayuwarki, tun daga farkon ta har karshen ta cikin kunci take. Kina nufin a haka za ki kare ta? Wannan hukuncin da kika yanke na tsanar Sa’idu da al’amarinsa ba shi zai sa ba, ba kuma abin da zai rage sai dai ya kara dagula rayuwar Zaynabu. Ki yi hakuri ki ba shi ita ya sanya ta a makarantar, tunda BAKI FISHI IKO DA ITA BA!
In kin dauki al’amuran rayuwa da sauki, watarana sai labari, za ki ga kamar ba a yi ba.
Ke baki bar zuciyarki ta huta ba, ita yarinya kin hanata amfani da damar da Allah ya bata ta yin ilimi, wanda zai zamo gata ga rayuwar duk da ta tsinci kanta a gaba.
Ya gaya mun hujjojinsa cikin takarda, kuma na gamsu. Ya yi alkawarin duk hutu Abu za ta zo nan tare da Faruku, in ta kare hutun sai a zo a tafi da ita. In kin sanyata a daki kin kulle me za ki yi mata itama me za ta yi miki? Ki duba ki ga duk tsararrakin ta sun wuce ta a karatu, shekarunta goma sha biyu, amma har yau ba ta fara sakandire ba sai yaushe? Sai shekarun karatun sun wuce mata?
Su Hafsisi duk bana za su shiga aji uku na sakandire, amma ita ki kama kina mummukewa a daki haba Rabi! Ni mijinki ban ji dadin ki ba, abokan zamanki basu ji dadin ki ba, haka ‘yarki hakuri take da ke, duk da ta san babu wata uwa a duniya mai hali irin na tata uwar. Wannan kaunar da kike wa Abu wace iri ce tunda kuwa ita ba ta ganta ba? Wannan ba so bane, kwarar ta kike yi….. in gaya miki gaskiya in baki barta ta bishi ba za ta kullace ki, ko da ba ta gaya miki ba. Kuma IDAN NURATU CE BA HAKA ZA TA YI BA..…!!!.”
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Wata irin rayuwa ya yi mai ban tausayi da rashin galihu, amma a komi Malam Ali da mai dakinsa sun tsaya mishi. Ko taron iyaye da ake yi a makaranta Malam ne yake wanke kafa ya je a matsayin mahaifinshi da ya rasu tun bai yi nisa da karatun ba. Haka ranar taron iyayen yara Rabi ke shan lullubi ta je matsayin mahaifiyar shi, duk da idan ka dube ta za ka san a haife ba ta haife shi ba.
Don haka a girman Sa’idu, da ci gaban da aya samu a rayuwa, baya da kamar Malam da Inna Rabi. Ka’ida ne duk karshen wata ya zo duba su, ya cika su da abin arziki kamar don su kadai yake nema, baya ga tarin iyalin da yake da shi a can Sokoto.
Na taso cike da dokin, ranar zuwan BABA SA’IDU, wadda a kullum take lissafe cikin kaina. Ba don komai ba sai don na san ranar duk da ya zo, to ni ranar take sallah. Sabbin dinkuna da kayan ‘ya’yan gayu da yake kawo mini kamar shago za a bude mini, cakulet da biskit kamar (super-market) din su gare shi, don haka duk hakorana suka cinye da zaki suka gwaigwaye kamin in soma famfara, sabbin littattafai da sabbin uniform wannan duk wata ne sai ya sake mini, don haka nake daban a cikin yaran gidan dama garin Gwarzo baki daya, babu ‘yar gata kuma ‘yar gayu kama na. Ga kuma kyawun sura.
Ribbon kuwa Baba Sa’idu dozin-dozin yake saya mani kala daban-daban. Ya Faruk ya zauna ya jera min su reras a kaina, in zamo kamar wata ‘yar Turawa, sai ka rantse da Allah Baba Sa’idu bai san ciwon kudinsa ba in dai a kaina ne. Allah ne ya hada jininmu da wata irin kakkarfar kauna, sai dai babban abin da ke bani mamaki, yake kuma sanyaya min jiki shine, duk wannan hidimar da Baba Sa’idu ke min, ko kadan baya burge Rabi, haka ko sau daya koda wasa bata taba sanya hannu ta taba kayan da suka fito daga hannun Baba Sa’idu ba.
Kwankwalatin lemu ne da ni guda talatin, a karkashin gadon Rabi me fameka, kullum sai in ciri daya in jefa a kofi, ranar da suka kare kenan ita ce ranar zuwan Baba Sa’idu. In ina wannan kirgen, Rabi kallona take kawai, sai dai ba ta magana, na san tsabar takaicina ke hana ta magana. A raina sai in ce, “Inna ai ke rayuwarki sai ke, tunda Malam da Ya Faruk ma basa burgeki, shi Baba Sa’idu wane ne da zai maki gwaninta?”
Ni dai haka nan nake son Baba Sa’idu saboda kirkinsa, saukin kai da haibarsa, ba shi da girman kai ko kadan, haka yadda yake sonmu ni da Ya Faruk yake kuma janmu a jiki, ko ‘ya’yan cikinsa basa samun hakan.
Tun karatun sakandire ya so ya dauki Ya Faruk ya koma gidansa ya yi karatu a can Sokoto, Ya Faruk ya ki don a lokacin babu wani babban da namiji a gidan kusa da Malam sai shi, sai ko yanzu da manyan almajiran Malam su Lawal da Harisu suka tasa.
Baba Sa’idu Malam ya dankawa alhakin nemawa Faruk gurbi a Jami’ar Ahmadu Bello, inda Faruk ya jima yana burin shiga, sai dai shi Farfesa so yake Faruk ya je UDUS don ya zauna kusa da shi, don haka ba tare da shawara da Faruk ba, a can Danfodiyon ya nema masa gurbi mai kyau, inda za ya karanci (computer-science). Dole Faruk ya koma gidan Farfesa kwata-kwata, sai bayan watanni uku-uku yake zuwa mana hutu.
Na yi kewar Ya Faruk ba kadan ba, na yi kewar kulawa da kaunar sa, na yi kewar komai nashi, domin shi Yaya ne mai karamci da nuna kauna, mai muhimmanta zumunci da kyautata shi, mai gudun duk wani abu da zai zubar da mutuncina da na mahaifinmu. To amma ni kaina ina son ya yi karatun, kasancewar sa babban burin rayuwarshi.
Ya kan ce yana so ya zamo mutun irin Baba Sa’idu, yana sha’awar duk wasu halayen shi banda abu daya, yana son ya zama mai hidima da iyayenmu da al’umma kwatankwacin Baba Sa’idu.
Kwaikwayon halayen Alhaji Sa’idu dole ne ga duk wani mutum da ya san ciwon kansa, mutum ne wanda ilimi, daukaka, da duniyar da Allah ya ba shi basu sa ya manta alkhairin da wasu tsirarun mutane su kai mishi ba, he’s really a model!
Kullum cikin hidima yake da Malam da almajiransa, da lafiyar shi, aljihunsa da karfinsa a gwamnati, amma ko kadan wannan baya burge Inna Rabi.
Kai ni sai da na fara wayo ma na lura inda wanda Innana ta tsana da gani a duniya, take kuma kyamatar abin hannunshi, to Baba Sa’idu ne.
Daga sanda ta ji rurin motarshi a kofar gida, kasancewar karar motar shi daban take da ta duk sauran motoci masu zuwa wurin Malam, domin ba ta da kwaramniya sai dai ka ji wani irin suuuuu! Kawai, to za ta shige dakinta ta bame da sakata, har ni ba ta kara nema na sai ya tafi, don ta san inda duk yake cikin garin to ina nanike da shi yana ta haba-haba dani.
Yau da dare har mun kwanta na tuna ban saka kwankwalatin zuwan Baba Sa’idu a kofi ba. Sadaf-sadaf na sauko daga gadon, kada motsina ya tada ita. To amma duhun dare bai sa na ga kwankwalatin ba, don haka na kunna aci bal-bal na zarosu daga kasan gado.
Abin takaici abin bakin ciki, sai na taras baki daya an hade min su wuri guda baki dayansu, bayan sun kusa karewa. Na tabbatar Inna ce da ta zo shara dazu ta sharo su daga kasan gadon ta hade su waje guda. Kenan wannan watan ban san takamaiman ranar zuwan BABA SA’IDU ba. Sai nasa kuka, ina yi ina karawa har da shessheka.
Gunjin kukana ya ta da Inna Rabi, ta zuro fararen kafafunta kasa daga gadon ta ce,
“Kyautar Allah me ya faru?’
Cikin kuka na ce
“Bayan kece kika hade mun kwankwalatan ZUWAN BABA SA’IDU???”.