← Book details Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 24

Sashe 20

Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin da ya wuce a bar shi a matsayin wanda ya wuce a fuskanci na gaba…..” Na dago cikin murmushin takaici na katse shi da cewa, “Kana manta da wa kake magana Ya Im, ba da Mami bane da Zaynab ne. Ka shirya shiga uku ne da kake marmarin auren jarababbiya kamana?” Da sauri kuma cikin murmushi ya ce, “Na shirya Zaynab, in ma sau goma-goma ne a rana duk za ayi miki, me ake da ‘yan mazan? Ke irin ki hudu ma idan ana ciki a rana a kuma haife za ku haife goma-goma a rana daya, in dai Imran ne mijin”. Ya kanne min idonshi daya cikin zolaya yana murmushin sa mai girgiza zuciyana, na kyabe baki na ce, “Ban ga alama ba, wai Liman babu Mamu…” Da sauri ya mike ya nufo ni yana kokarin cire riga ya ce, “Eye! Me kika ce Zaynab sake fadi ban ji sosai ba, bari in nuna miki ko waye Imranan nan da kike rainawa… wayon ki kadan ne haka maganganunki ko daya babu respect a cikin su. Ko da yake mantawa na yi ke din babbar mace ce ba karama ba, tunda tun kina karama babba ce, to babu laifi yau kin samu babban namijin da zai sa ki raina kanki….” Na ga da gaske yake tubewar zai yi, sai ‘ya’yan hanjina suka hautsine, na koma lallashi na ce, “Haba don Allah Ya Im, idan Mama ta zo fa? Allah ni wasa nake….” Ya ce (yana kara dosoni) “Wannan ne kuma baki isa ba, tunda ba matse bakin ki na yi kika fadi abin da kika fada ba”. Ya wancakalar da shirt din da ke jikinsa ya rage singileti fara sol. Na dauka da wasa yake ba cirewar zai ba, na cira kai a hankali na hango wani irin ingarman kirji lullube da muscles baibaye da lallausar gashi baki sidik nannade da gurayen karfi ta ko ina. Ban taba ganin babban mutun irin Imran ba, ban taba ganin Da namiji mai halittar GIRMA irin Imran ba. Na tabbata duk abin da ya fadi babu kuskure a ciki, zai iya yin abin da ya fi hakan. Ubangiji da ya halicce shi ya iya halitta, ya kyautata halittarsa yadda ta zamo mabambanciya da ta sauran maza kwatankwacin sa. Kenan tsarki da GIRMA sun tabbata gare shi. Ganin ya nufo ni gadan-gadan yana shirin cafka ta, na ce, kafa! Me na ci ban baki ba! Zuwa cikin toilet na murza key sai karkarwa nake saboda tsabar kaduwa. Ina jiyo shi yana cewa, “Karyar banza cika bakin wofi, da ki tsaya mana ki ga aiki da cikawa, ki ga in ana haihuwa a gobe baki haifewa Abba dan jika a gidan nan gobe ba!” A raina na ce, “Allah ya tsare ni da haihuwar SHEGE!” Ashe har ya fito ya shiga kunnensa, ya ce, “Na ji abin da kika ce Zaynab, ina mai tabbatar miki in baki amince da bukatata ba wato daura auren mu bayan kammala jarrabawar ki, za kuwa ki haifi SHEGEN! In yaso daga baya ayi mana auren mu rike abin mu ko ya kika gani?” Zaynabu dai baki ya mutu, sai Uban mazari da jikina ke ta yi kamar wadda ta yi gamo. Ya yi dariya shi kadai yana fita daga dakin yana cewa, “Yarinya baki san Imrana ba, watakila sai a (foot-ball field) watau filin saka kwallo, ranar Innar taki, Abban naki da Ya Faruq din naki basu isa su kwace ki ba. Kuma in gaya miki ke karamar jarababbiya ce, su manyan jarababbun tsayawa suke a doka kwallon don a ga hazakar kowa, in ya so mai sa’a ya dauka, ba gudu suke suna neman mafaka ba alamar weakness (ragonta) kenan”. Bani na fito ba sai da na ji muryoyin su Iftihal suna cigiyata a dakin za su kwanta, na kasa ko da shakar kwakkawaran numfashi don yanzu su Iftihal sun zame min surukai, na rasa yadda zan yi in iya hada ido da su. Sai na jiyo Iftihal na dariya tana gulmatawa Azizah, “Allah sarki Anti Abu! Ya Im ya takurata a gidan nan, Allah ni har tausayi take bani, dazu da muka shigo baki gani ba tana ta kuka abin tausayi, yanzu zaman falo ya gagareta tana tsoron ko zamu gayawa Mama ne”. Azizah ta ce, “Ke rabu da ita, gulma ce ita ma tana son sa, baki san duk ranar da na yi zancen Mami da kuka take kwana ba? Gaskiya in suka yi sa’ar yin aure, they’ll make a perpect couple, domin sun dace da juna. Sai dai kin san ba karamin abu bane a ce Hajiya ta amince, yadda take son Ya Im da auren Mami, amma daga Abba ba za su samu matsala ba”. Na ga dai in zan kwana cikin bayin nan su ba abin da ya dame su, ba kuma fita za suyi daga dakin ba hirarsu kawai suke. Karewa ma tare zamu kwana cikin dakin, to boyon har na yaushe zan yi? Sai na share ido na murje kunyar na fito, duk suka juyo suka dube ni kamin su kyalkyale min da dariyar su ta ‘yan biyu mai ban haushi. Ban ce musu komai ba na bi lafiyar gado na ja bargo har kaina. A sannan ne kowacce ta bi gadon ta suka kwanta suma. Dakin nau gadaje ne na ‘silver’ kanana guda uku, nawa ne a farko sai na Iftihal sannan na Azizah. Can anjima Iftihal da ta fi makotaka dani ta kwaye bargon da ta rufe kanta iya wuyanta ta ce cikin rada yadda Azizah ba za ta ji ta ba, “Anti Abu don Allah in ce wani abu?’ Na dauka tsokanata za ta yi sai na sha mur na ce, “Ki rike abunki bana son ji”. Ta yi shiru, can ta ce, “Am serious, don Allah ya ya so yake? Ina nufin ya ya za ki iya kwatanta son Ya Im a zuciyarki?” (Tana murmushi mara amo). Na lumshe ido na a hankali ina jin wata sabuwar kauna na ratsa zuciyata. Ni kaina na san son da nake ma Imran ba za ya kwatantu ba, ba shi da iyaka, kwakwalwata ba ta yi kaifin da za ta fahimce shi ba, harshena ba zai iya bayyna shi ba, domin ya fi yawan silin gashin kaina. Ta tabbatar ba za ta ji kalma ko daya daga baki na ba, (shiru ma amsa ce, amma ga mai hankali), sai ta hakura ta juya ta kwanta. Washegari ya kama asabar din karshen wata, kuma rana ce da muke sanitary watau kakkabe komi na dakin mu, mu fidda kaya masu datti mu cire yana, mu kintsa sif din mu. Wannan wani aiki ne da muka sanya kanmu bama son masu aiki suyi mana saboda baya gamsar damu. Imran yayi sallama a dakin ya shigo, turaren da ya fesa na (Gucci-Rush) ya bakunci hancinmu. Na lumshe ido zuciyana na girgiza domin ba karamin kyau ya yi ba, cikin bakar shadda ghalila. Mu kuwa ko wanka ba muyi ba. Ni sanye nake da doguwar rigar barci fara sol mai gajeran hannu, sai dai na daura zanen atamfa a kai, kaina babu kallabi, don haka murdaden gashin kaina ke dunkule cikin tufka guda a gadon bayana, rike da abin sharo yana ina sharowa. Su Azizah duk suka russuna suna gayas da shi, ya amsa yana cewa, “Zance na zo Azizah, ina fatan ban yi sammako ba?” Kunya ta kama su duka, suka dukar da kai suna dariya kasa-kasa, ta ce, “Gaskiya ka yi sammako, Anti Abu ko wanka ba ta yi ba”. Ya ce (idanun shi a kaina), “Kin san meye ne Azizah? In da kin san kyan da ta yi min a haka, da na ce ta daina wanka. Wannan Zaynabun dake tsaye gabana, ta fi mun duk matan duniya. Idan na daga ido na dubi wata mace, komi wankanta da kwalliyar ta sai in ganta kodaddiya a kan Zaynab dina. Wanka da kwalliya ba su ke sawa a so mace ba, wannan daga Allah ne. Don haka in kina tunanin hakan ki daina. Ina tabbatar miki in Zaynab za ta shekara ba ta yi wanka ba, ba zan daina sonta ba, ba zan daina ganin ta a matsayin wadda ta fi kowacce mace a idanuna ba….” Dariya suka yi suna kokarin ficewa saboda su dai basu saba jin irin wadannan maganganun ba, balle kuma daga bakin da suke matukar girmamawa. Ya ce, “Ku yi zaman ku ayi hirar da ku, watakila in ci arzikinku ta amshi kokon bara na, in kun tafi ko kallo na ba za ta yi ba. Ku taimaka ku tambaya min Zaynab, shin kalamanta masu tsada na sayarwa ne? Ko-ko kwalliyar da na yo mata ne bai burge ta ba in koma in sako?” Suka sa dariya gaba dayansu, nima kaina ban san sanda na murmusa ba, still ban juyo ba na ci gaba da abin da nake, kamar in ce da shi shin ba yanzu ka gama cewa ba kwalliya ke sawa a so mutum ba? Ya karaso ya amshi abin sharar a hannuna yana cewa, “Kawo nan in karasa miki ko kya zauna mu yi zance?” Ya dubeni cikin idanun shi cike da abubuwa da dama, na yi hanzarin zama a gefen gado saboda kafafuna dake neman kayas dani. Iftihal ta ce, “Hala baka taba zuwa zance wurin Mami ba?” Ya ce, “Eh, yes, ban taba ba, ita ne take zuwa”. Ta girgiza kai ta ce, “Ko da na ji”. Ya dube ta bayan ya aje sandar ya ce, “Me kike nufi?” Ta ce, “Na ga baka iya bane, duk da ban taba yi ba na san ba haka samari ke gayawa ‘yammatan wai sun zo zance gatse-gatse ba, abin babu ko dadin ji”. Ta zura da gudu Azizah ta rufa mata baya ita ma ta ce, “Gaskiya idan baka koyo zance ba, ba za a karbe ka ba”. Ya zauna a gefena na yi saurin rufe fuska da tafukana ina dariyar su, ya ce, “Da gaske ne ban iya ba Zaynab?” Na girgiza kai ba tare da na bude fuskar ba. Ya ce, “Wallahi ko ki bude fuskar nan ko in sumbaci hannun ki”. Da sauri na bude. Ya ce, “Ashe dai yanzu an san ni wane ne, da kar ki bude mana”. Na tsuke
Chapter 20 · 0% Book details