Sashe 4
Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sannan ta dawo. Tabarmar gidan kuwa babu wadda ta isheta zama, sai dai ta zo da katuwar darduma mai laushi irin ta zuwa picnic din nan ta baje a dakin Inna Dubu, ta kishingida suna kwasar hira da yake ‘yan’uwan juna ne. An ce asalin ta ma a nan gidan Innar ta rike ta, Malam ya aurawa Farfesa, amma da yake Hajiyar birni ce shi Farfesa bai san hakan take yi ba in ta zo garin. Yawanci za ka samu wanda tushen sa talaka ne futuk in Allah ya yi mishi arziki rana daya, shi ke yin irin haka, ba wanda ya tashi ya kuma girma cikin arzikin ba, kamar amarya Hajiya Azumi kenan. Mace ce mai saukin kai, faram-faram da daraja kowa da zama ko mutunci ya hada ta da shi. Hajiya Azumi tamkar kawa take da Rabi, don basu fice tsararrakin juna ba, in da akwai wani da ya shafi Farfesa da Inna Rabi ke kulawa to Azumi ce, ina mamakin hakan, tunda kuwa ko ‘ya’yan da ta haifa ita Azumin basu tsira daga kiyayyar Innar ba (su Iftihal), amma ita in ka gansu suna hira rimi-rimi sai ka rantse da Allah Ya da Kanwa ne. Wannan na daga dalilin da yasa Farfesa Baba Sa’idu ya turo ta ga Inna Rabi, don ya san tana ganin mutuncinta fiye da na kowa nashi. Sun nitsa da hirar duniya Hajiya Azumi ke gaya mata makasudin zuwan nasu takanas nata ne, ta ce, “Ashe ni ba zan iya rike Abu tamkar su Aziza ba Rabi? Na yi mamaki da Alhaji ya ce dani wai ke kika ki amincewa da zaman Abu tare damu, wallahi kin ji na rantse Iftihal kullum ba ta zance sai na Abu, haka dan’uwanta, ba yadda za a zauna a mike bai ambaci Abu ba. Ba fa dauke miki ita zamu yi kwata-kwata ba Innarmu, duk hutu tana nan a dakinki. Kaunar Baban su Aziza da Abu Allah ne ya hada ta, mai zai sa ki kasa ganewa? Ba a san me Allah zai mai da Abu a nan gaba ba, a dalilin karatun nan har al’umma su amfana da ita”. Inna ta yi murmushin da bai kai zuci ba, ta ce, “Ni abin naku ku da mijinku ya daina bani haushi ya koma bani mamaki”. Azumi ta ce, “Mamakin me kuma Innar Abu?” Ta ce, “Mamaki mana. Yar daya jallin jal da Allah ya bani kun sa mata kahon zuka, kun dage sai kun rabani da ita duk da bataliyar ‘ya’yan da Allah ya baku, saboda hadama ko saboda mene? Ku daina cewa don Abu ta yi karatu za ta je gidan ku, kawai ku fito fili ku ce kuna so ku kwace ta ta zauna tare da ku, in makaranta ce har Sokoto ce za ta gayawa Kano karatu?” Azumi ta yi dariyar cin nasarar ganin ta fara samo kan Innar, ta ce, “Ayya Innar Abu! Ke din ce kin iya haihuwa, Abun taki abar so ce ga kowa, ga fara’a ga farin jini, yarinya ce mai shiga ran mutum farat daya. Idan aka samu irin su Abu suka yi ilimi mai zurfi suna da matukar amfani ga al’umma, su kuma zamo ababen alfahari ga iyaye. Ba kya gani komi nata, nutsuwar ta da takun rayuwar ta daban ne da na sauran yara? Ki daure ki bamu Abu, da yardar Allah na tabbatar miki ba za ki yi dana sani a kan hakan ba”. Shima Faruq tunaninsa daya ne da na iyayen dakinsa, don dai baya son Inna Rabi ta kullace shi ne kamar yadda ta ji haushin Malam da ya sanya baki. Yana ganin in an bar Abu a kauye, ba ta dandani rayuwar birni irin ta su Iftihal ba, ba ta kuma yi karatu mai tsada ta goge irin Aziza ba, an tauye mata hakki, duk kyawun nan nata da yalolon bakin gashinta maras gyara, a kauye za ta kari rayuwar ta, watakila ma a dauka a baiwa wani gardin kauyen yadda aka yiwa su Halima. Shi kuwa mai farin ciki ne da duk wani ci gaban kanwar sa tilo. A dan zaman da ya yi na shekaru biyu da iyalin Farfesa, sai ya rika tambayar kansa shin su rayuwa suke, ko ko a daji suke?