Sashe 7
Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da alama Iftihal yarinya ce mai saurin sabo da kuma wayewar kai, gami da karbar rayuwa a duk inda ta tsinci kanta. Kafa ta nade tana cin gyada, tana bani labarin Aziza (twin- sister) dinta.
Ba ta daddara ba ta sake kallon gefen da Inna take, ta ce, “Innar Abu sammun rogon nan da kike tsamewa, hadawa nake da gyadar”. Inna ko kallon ta ba ta yi ba, yayin da kirjina ya shiga luguden uku-uku. Tsoro na Allah tsoro na kada Iftihal da ta zo yau din nan ta fahimci cewa gabar da Innana ke yi da Babanta itama ya shafe ta. Idan rogon Innar ya amsa mata, to ita ma Innar ta amsa. Ta sake maimaita tambayar ta na Inna ta ba ta rogon. Budar bakinta sai cewa ta yi,
“Ai ba ubanki ne ya saya ba!”.
Na yi saurin kai hannuwa na dafe kai, cikin wasu hawaye da suka ciko idona. Inna Dubu ma ranta ya baci da wannan halayya ta Inna ta. Ta zo tana dibar rogon cikin roba tana cewa,
“Bari ta ci kasona, ai ni mijina ne ya saya idan ita ba Ubanta ne ya saya ba!”.
Tana fadi ne cikin dariya, domin gusar da damuwar da fuskar ‘yar yarinya Iftihal ta shiga. Watakila ba a taba yi mata irin wannan gwasalen ba a rayuwarta. Ta kawo rogon ta dangwarar mana, tana cewa da Iftihal, “Ke ci ki rabu da ita, ba ta jin Hausa sosai, ba ta fahimci me kike cewa ba”.
Ta ce, “Abu ma ba ta jin Hausar? To wanne yare suke ji?” Ta ce, “Abu ta fita jin Hausa, ita faransanci take ji irin na kasarsu, ai kin sani ko?” ta ce, eh na sanshi, ana koya mana a makaranta, Abu ina ce ce kasar ku?” Na yi dan diri-diri na rashin sani, don kuwa ni ban san da wata kasa ba banda wannan da muke ciki. Inna Rakiya dake gefe ce ta ce da ita,
“Niger!”.
Malam da Baba Sa’idu ne suka shigo, suna hirarsu irin ta wadanda suka aminta da juna. A yau ban yi gigin yin tsallen taren Baba Sa’idu ba, kamar yadda na saba. Duk da kankantata na san ba abinda Innata ta tsana kamar ta ganni a jikin Baba Sa’idu, don haka na yi ma kaina alkawarin na daina, daga ranar da hakan ya janyowa Baba Sa’idu wulakancin da bai taba gani ba.
Sai muka russuna mu duka muna gaishe su, ni ina gayar da Baba ne, Iftihal na gayar da Malam. Murmushin jin dadi ya bayyana a fatar bakin Baba Sa’idu, yayin da Malam ke ta tsokanar Iftihal da amaryarsa.
Ya ce, “Yanzu-yanzu zai kwashe kayan dakin Rabi ya sanya ta, don ita ta tsufa ita ko gata nan sabuwa gar a leda”. Iftihal tana ta dariya, ta ce, “Baba Malam ka ce da Abu ta rakani in ga gari don in ba Aziza labari”. Malam ya ce, “Maza Abu sako takalmanki ki raka amaryata gidan gonar Babanta, ki kaita har gidan Halima da Safiya, ki gaya musu diyar Babanku ce”.
Muna tafe tare da Iftihal tana ta yi min hira, wadda duk rabin maganarta Turanci ne ba duka nake fahimta ba, amma ita ta kasa gane hakan ta hutar da bakinta, ni dama tuntuni Allah bai dauran yawan magana ba.
Da alama yarinya ce mai surutun tsiya, fadi ba a tambaye ka ba. Takaicin al’amarin Innata a kan Baba Sa’idu ke damuna, abin har ya wuce kansa ya shafi ‘ya’yan cikinsa? Rabona da su Iftihal tun suna kanana da suka zo da babarsu wadda abin mamaki ita suna shiri da Rabi, sabanin uwargidan da suke narka matsananciyar kiyayya.
Shin har yanzu lokaci bai yi ba da ya kamata in san duk musababbin wannan? Tambayar da Iftihal ta jefo min ta sake jefa ni a cikin rudani,
“Abu Innarki na da tabin hankali ne?”
Nayi gaggawar juyowa na dube ta tamkar ta soka min mashi a kahon zuci, amma na kasa ba ta amsa, don ban san me zan ce mata ba. Gaskiya ne al’amuran Innata sun fi kama da na masu tabi hankali, kuma a yadda kowa yake biyar da ita a gidan, ba a dauke ta cikakkar mai hankali ba.
Kishiyoyinta basa kishi da ita, basa takaicin duk gwasalen da take musu. Mijinta bai dauki yanayin rayuwarta da muhimmanci ba, balle har ya damu da hakan, binta kawai ake da yadda take so, don a zauna lafiya.
To amma ni ba zan taba yarda da cewa da ake wai Innata na da tabin hankali ba, musamman in aka yi la’akari da irin kalaman da ke fita a bakinta na hankali da sanin yakamata ne. Illa in ce yanayin rayuwa ne ya mai da ta hakan, ya sanya ta daina kaunar kowanne dan adam sai mu da muka zame mata dole.
Na kan tambayi kaina don me kiyayyar ta ya fi yawa a kan Baba Sa’idu? Me ya yi mata? Me yasa ta tsane shi fiye da kowa a duniya? Me yasa kome zai mata don ya faranta mata baya burgeta? Tunda nake ban taba ganin mutum mai kirki, karamci da mutuncin Baba Sa’idu ba, kamar yadda ban taba ganin mutum mai arzikinsa ba!.
Na daga kai na yi duba ga Gidan Gonarsa makeken gaske, dabbobin dake ciki dukkaninsu farare ne sol. Girman gidan gonar kadai ya isa a gina gidaje biyar manya-manya, ba tare da kowanne ya gogi dan’uwansa ba.
Ita kanta Iftihal sakin baki ta yi galala! Tana kallon Agwagin ruwa farare kal sama da dari na yawo a cikin tafki, fararen Tantabaru rainon Ingila na tashi daga wannan daki zuwa wancan. Fararen Babba-Da-Jaka dika-dika goye da ‘ya’yansu cikin jikkunansu, fararen Dawaki kosassu na ta haniniya tare da harba kafafunsu cikin koshin lafiya, fararen kaji (buloras) wadanda ba za su kidayu ba, haka kwaikwayen da suka sassaka mutum goma ba za su iya kwashe su a yini daya ba.
Idan ka nutsa cikin gidan gonar sosai fararen ragunan Sudan ne buka-buka masu manyan kahonni suma cikin fili guda. Wannan ba zai burgeka ba sai ka ga fararen Balbelun dake shawagi cikin wayar da aka zagaye su. Ga kuma Tinkiyoyi da ‘ya’yansu suma farare sol-sol kai ka ce kullum sai an yi musu wanka, sun fi guda dari cikin fili guda.
A can wani katon fili ‘zebra’ ne (jakin dawa) guda uku manya-manya masu zanen fari da baki. Babban swimming-pool cike yake da fararen kifi (salmon) manya da kanana, kai ka ce a (Dambatta-Dam_ kake. Iftihal bakinta ya kasa rufo da mamakin wai na ce wannan duk na Babanta ne.
Ta daga kai ta yi duba ga Dawisu korra sharr dake ta shawagin su bisa doguwar katangar ginin kai ka ce katangar gidan Zoo ce saboda tsayi. Sun zubo dogon bindinsu kasa, wasunsu kuwa sun bude shi cikin nuna baiwar kyau da Allah yai musu dai bai yiwa wata dabba ko wani tsuntsu a duniya ba.
Ma’aikatan wajen sun tsinko mata kayan marmari nunannu, sun wanke sun zubo mata a cikin kwando a matsayinta na bakuwarmu da ba ta taba zuwa ba, kuma diya ga Baba Sa’idu. Amma ta kasa sha, extremely puzzled! Sai tambaya ta take wai Baba shekaru nawa ya kwashe yana assasa gidan gonar nan? Wannan ai ya fi karfin a kira shi gidan gona sai gidan Zoo!
Na ce, “Kin taba ganin gidan Zoo da babu zaki babu damisa? An ce Baba tun yana sakandire ya fara assasa gidan gonar da ‘yan tsirarun dabbobin da Malam ya bashi, amma bata fara habaka ba sai dawowar shi karatu daga Turai”.
Ta ce a sanyaye, “Amma Baba mai yasa bai taba gaya mana yana da wannan gidan gonar ba?” Na girgiza kai na ce, “Ba zan sani ba, mai yiwuwa yawan abubuwan da ke kansa su suka mantar da shi ga yin hakan. Don shima sai ya zo garin nan sau uku bai zo nan din ba, duk albashin ma’aikatan ta hannun Malam yake basu”.
Akwai shuke-shuke na kayan marmari musamman guava, Roman, fasa-dabur, inibi, tuffa, lemun zaki, ayaba, cashew da abarba. Muka debi iyakar iyawarmu a leda, daga nan muka tafi gidan Yaya Halima. A nan muka yi sallar magariba muka ci abinci.
Na yi zaton Iftihal ba za ta ci ba, musamman da yake tuwon dawa ne miyar kuka, amma ita ce mai cewa a karo har tana side hannu.
Yaya Halima ta ba ta dakakken yajin daddawa mai dadi da ta ce tana so. A kan hanyar mu ta dawowa gida Iftihal tace,
“Shin Abu mai yasa Innarki ba za ta bari Baba ya tafi dake ba a sanyamu makaranta daya kamar yadda Babba ke so ba? Muma mun gama firamare, JSS 1 za a kai mu. Kinga ga Ya Faruk ba za ki yi kewa ba, za ki ji dadin zama da Mamarmu, don tana sonki”.
Na yi sauri na ce, “Innata ma na sona, Iftihal ba za ta amince ba”. Na yi gaba abina na barta a baya.
A kwanaki biyun da muka yi tare da Iftihal mun shaku sosai. Wasu halayen ta ne guda biyu, suka sa ta shiga raina; batasan mene ne girman kai ba, kuma ba ta dauki kanta a bakin komai ba. Duk wanda ta ga Babanta na so tana girmama shi.
Da za su tafi mun sha kuka, ta rantse ba za ta tafi ta barni ba a barta a nan mu zauna tare. Sai da Malam ya yi mata alkawarin in Allah ya yarda WATARANA Zaynabu-Abu gidansu za ta koma baki daya, sannan ta hakura suka tafi.
Inna na daga gefe ta ce, “Me kake nufi da da wannan alkawarin? To kada Allah ya yarda! In ma wani mugun nufi ne kuke da shi a kaina da Zainabu, kaida Sa’idun naka, to Allah ya fiku. Bani da kowa sai shi, don haka da shi na dogara. Na kuma tabbata zai fiddani da Abu daga kutunguila da sharrin Sa’idu”.