Sashe 14
Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Imran dogo ne baki kakkaura, sai dai bai kai tsayin Faruq ba, amma ya fishi kauri da fadin kirji (physique), yana da kyakkyawar sura sosai, ya aje zagayayyen gashin baki dan siriri wanda ya tafi ya hade da kauraran zagayayyun lebban shi masu sulbi. Yana da hakora masu haske, jerarru kuma masu sheki. Komai nashi attractive wato mai daukar hankali ya dube su ko da bai yi niyya ba.
Kallon yanayin fatar jikinshi kadai ya isheka kimanta irin hutu da jin dadin da yake ciki, haka idanunshi za su nuna maka tsantsar ilimin da ke cikin su. Ba a fiya son mace mai kamun kai ta fiya sanya idanun ta sosai a kan maza irin Imran ba, domin ba wuya za a aikata zinar ido. Wanda kuma shi abin ya zo ne da halittar shi ba wai da gangan yake yi ba.
Yana da yawan amfani da karamin gilashi (medicated) ba don lalura ba sai don kara karkon idanu, haka nan Imran baka raba shi da cin biskit din nan na alkama (hob-nobs), yana da fada sosai kamar barkono, amma in ka fahimce shi ya fi ruwan sha saukin sha, raini ne baya so.
Shine babban da a ‘ya’yan Farfesa, sun haife shi a kasar England zamanin da shi Farfesa yake karatu, inda ya samu ilimin firamare da sakandire. Don haka ne in yana lallausar Turancin sa ba za ka so ya daina ba. Sai bayan haihuwar shi da kimanin shekaru goma, sannan aka haifi Hassan, Rufa’i ya biyo baya sannan Jauhar da dan karamin su Aliyu da Baban ya sanyawa sunan Malam Ali, suna kiran shi Haidar.
Sai da ya fara aiki a UDUS ne ya auri Azumi, wadda take basakkwata usul, kuma diyar wani abokin shi Farfesa a nan Sokoto wai shi Dr. Isma’ila Taura, ya ganta ne ranar ba da shaidar (Degree) ga daliban shekararsu da matsayin da ta fito da shi ne (best overall student in MBBS) na shekarar su baki daya.
Yana daukar lasifika abin da ya bude baki ya ce a filin taron shine, “Idan Azumi ba ta da aure shi V.C zai aure ta, wannan kawai shine kyautar da yake jin zai ba ta ya nuna kwazonta a duniya. Ba kuma tare da ya ganta ba, tsohuwa ce ko yarinya ce?”
Gaba daya filin taron rudewa ya yi da sowa, masu ihu na yi, masu kabbara na yi da sanyawa abun albarka. Babanta ne ya shige mai gaba ya ba shi auren ta. Ita kanta ta san ba karamar sa’a ta yi a rayuwar ta ba.
Imran da Faruk na tare tun daga farkon karatunsu na Jami’a, wato tun dawowar Faruq Sokoto, sun shaku sun kuma amince da juna, domin halayensu duk kusan daya ne, daman an ce wai sai hali ya zo daya ake abuta, wannan haka yake. Halayensu duk kusan daya ne, nutsuwar Imran daban take da ta sauran ‘ya’yan Farfesa, mutum ne da ya san ciwon kansa kwarai, yana adawa sosai da aqidun Malam Bature, yanayin rayuwar shi na Sokkotawan usli ne ziryan, hakan yanayin sutturarshi shadda ne, caftan ko babban riga a kullum, kai ka ce wani magidanci ne, da wuya ka ganshi da wani kaya ba shadda da hula ba, ra’ayinshi kenan.
Bayan kammala karatun su sun samu an yi posting din su gari daya yin bautar kasa, wato jahar Abia, duk da ba fanni daya suka yi karatu ba, shi Imran ‘civil engineer’ ne.
Sanda na kai aji hudu a sakandire duk wasu alamomin girma na ‘ya mace sun soma bayyana a jikina, da yake ban fara karatun sakandire da wuri ba, ni kaina na san na sauya wane shekarun baya. Abin nufi, halittar jiki da tsarin rayuwa. Zan iya kimanta shekaruna goma sha biyar a lokacin, mun yi sabo sosai da Imran duk da cewa ba zaman gidan suke ba suna fafutukar neman aiki.
Ba zan manta da yadda sunan “Abu” ya bace min a shekarar ba, ta dalilin Imran. Ya dauko mu ne daga makaranta yana tuki ina gaban mota, ya ce, “Shin wai ke ya sunan ki ne?” Na dube shi galala! Baki a bude ciki da mamakin wai duk kiran nan da ake Abu-Abu bai san sunana ba? Wannan ai rainin hankali ne, don haka na juyar da kai ban amsa ba.
Daga bayanmu Iftihal ta ce, “Kai Ya Im, da gaske baka san sunan ta ba?” Ya ce, “Gaskiya ban sani ba, na ji dai kuna cewa wani abu wai “ABU”, ni ko na san kyakkyawar yarinyar kamar wannan kallo daya za ayi mata a san ba sunanta Abu ba”.
Gaba daya suka tintsire da dariya, ni ko na yi murmushi kawai. Ya kafa mun ido kamin ya mai da hankalin shi a titi cikin son karantar karbar da na yiwa zancensa. Na kalli can wani gefen daban, cikin raina ina cewa, gaskiyan Iftihal ne, gaskiya ne ba mutun irin Yayan ta! Komi nashi mai ban sha’awa ne, hatta furucinsa. Azizah ta ce, “A school ma ba a ce da ita Abu sai Zainab”. Ya ce, “That is good, ZAYNAB, daga yau cikin ku kada wanda ya sake ce da ZAYNAB (ABU)”.
Wannan shine mafarin al’amarin. (Takori).
****