← Book details Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 24

Sashe 24

Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

ko ya nake ba zan iya barwa Mami shi ba. Amma a dole washegari na shiga tirsasa zuciyar da ta fidda Imran da duk wani al’amarin shi a cikin ta. Ina nuna mata beke da illar dake cikin hakan, ina nuna mata Imran ba alkhairi bane a tare da ita, ina nusarsheta da cewa a kul, Zaynabu! Igiyar rakumi… ta yi nesa da kasa, tsira da mutunci…. ya fi tsira da kudi, abu mai yiwuwa shi ake yi ba mara yiwuwa ba, yaro tsaya matsayinka…. kada zancen ‘yan duniya ya rude ka, kai zai kai nya baro. Amma wallahi zuciyar nan mai laushi da kafiya (delicate but strong) ta ki amincewa, ita dai Imranan nan shi kadai take so by all means. Babu abin da ya dame ta da hujjoji na, ba ta san su ba, IMRAN kawai ta sani. Cewa take Zaynabu-Abu luv, have no boundaries….. A kwanakin biyun da suka biyo baya, duk rabin hirar su ta Mami ce da kirkin ta. Idan na ji ba zan iya jurewa ba, sai in tafi daki na ci kuka na ya isheni, in sa sabulu in wanke fuska. Kamar wata zautacciya, in saka wannan in kunce da wancan. Daga karshe na alkawarta ma raina ko Imran din nan ne autan maza na hakura da shi, don tsira da mutuncina da na iyayena. Duk wanda ka ga Hajiya Sa’a ta tashi ta rako gate da kafafunta, to tabbata ya isa, ta san shi din wani ne, za kuma ta samu wani abu a jikinsa, duk da babu abun da Allah bai mata ba ita da mijinta da ‘ya’yanta, ba ta da godiyar Allah ko kadan. Ko a jiya Imran ya aiko mata da sabuwar mota (Hummer Jeep) da gaba dayan albashinsa na wata da watanni, dama ya ci alwashin ita ne za ta fara cin gajiyar iliminsa, amma a yadda take nan-nan da Mami, sai ka rantse ba ta taba mallakar kwandalar kanta ba. A kwanakin da suka biyo baya ban kara yardarma zuciyata ta tuna Imran ba, na tattarasu shi da Mamin da al’amarinsu na zuba a kwandon shara. A yau muka fara zana WAEC da practical Biology, bamu muka fito ba sai karfe hudu na yamma. Kwakwalwata ta yi zafi, kaina ya yi zafi rau, ga yunwa, gajiya da nannauyan barci a kaina, wanda ban samu na yi ba a daren jiya muna ta karatu. Don haka mun shigo gida a gajiye lis, muna tafe muna hada hanya, ban lura da bakuwar motar da muka samu ba a harabar gidan. Muka isa falo kowacce na ‘wash-wash’, ni ko dafe nake da goshina, idanuwana a rufe nake tafiya a cikin falon. Ban ankara ba na ji na yi karo da mutum, kamin wani lafiyayyen kamshin turaren nan na (Boss-Intense) ya bakunci hancina. Na yi hanzarin bude idanuna da suka yi ciki sosai saboda yunwa da wahala, na dube shi yana murmushin nan nasa mai cike da ginshira, a hankali ya ce, “Ya… ‘yan makaranta ba a gani ne?” Wallahi sauran kadan in fadi a tsakiyar falon sakamakon kafafuna da suka kasa daukar nauyin jikina, saboda yadda Imran ya koma, in da dare ne ba za ki gane shi ba. Ya zama kato, ya zama ‘giant’ ya kara kyau na ban mamaki. Tsayayyun kafadun nan nashi ‘pysique’ na barazanar gabje maza biyar a lokaci daya saboda yadda suka kara habaka har da doro na musamman, na kasaitattun maza. Ya kara haske ba can ba ‘chocolate’, ya kuma kara murjewa, da gani za ka san naira ce ta zauna da gindinta. Lafiyayyen agogon ‘switch-blustery’ sai walkiya yake cikin lallausar fatar hannun shi, yana sanye da farar shadda kal kamar takarda, dinkin mazan Maiduguri. Na yi gaggawar ba shi hanya, ya yin da shawarar Anti Rose ta zo min cikin kaina kamar karatun sallah. Cikin halin ko in kula na ce, “Sorry plz, ban ganka bane na gaji ne sosai. Muna barka da zuwa”. Da daddare muna falo muna ta hirar pepermu ta yau, ya shigo yana balle links din hannun shi yana tambayar Mama ina abincinsa. Gaba daya muka rude mai da labarin zuwan Mami, muryata ta fi ta kowa karadi, ina kara kuranta kyawun Mami da kurzanta kirkin ta, duk sai ya sha kunu ya bi ya daure lallausar fuskar nan tam, alamun ba wargi. Amma bamu fasa ba, kamar ma zuga mu yake. Hajiya na gefe tana ta murmushin jin dadi, ta ce, “To kai ka ji ‘yan kannen naka ma sun yaba da ita”. Ya dago fuskar nan a murtuke kamar hadari, ya kulu iyaka. Ya hade giran sama da na kasa a take ya koma (previous IMRAN) mai gigita kannensa. Na yi mamaki da bai daka mana tsawa ba. Ya zube min manyan idanun shi a mamakance, ya ce cikin gatse da wata murya mai kama da ta mai ciwon makogaro, “Har da ke Zaynab, kema kin yaba da Mami?” Da sauri na gyada kai ina dariyar nan da Malam Bahaushe ke kira (yake), na ce, “Wallahi kuwa Ya Im na yaba, a very simple lady, ba ta da girman kai”. Ya sakar min hararar da ta kada min ‘ya’yan hanji, ya ce, “Tunda haka ne ki hadata da Faruq man, kin ga shima baya da girman kan, amma ni ta yi mun tsufa sai yarinya (sweet 16) zan dauka, yadda nake (fresh) din nan in na auri kaman Mami ‘yar (28) ai na ci baya……” Iftihal ta toshe baki kada dariyar da ta zo mata ta fito, Azizah da Hajiya suka daure fuska wato sun ga samu suna neman ganin rashi. Ni ko na yi tsuru-tsuru don duk maganar nan da yake idanunshi a kaina yake yin su, kamar da ni kadai yake magana a falon. Ya ci gaba da cewa, “Shin ma wai ita Mamin da ta zo ne ta ce muku na ce ina sonta? ‘Yar ajin su Faruq ce fa, daga kawai tana gani na ina zuwa wajen sa ta like min kamar kaska, amma ni wallahi bana ra’ayin bakar mace a rayuwata, ni baki ita baka, muyi ta haifar bakaken ‘ya’ya me aka yi kenan? Ko Annabi (S.A.W) ya ce in kai baki ne ka auri fara, in kai fari ne ka auri baka, sai ku haifi ‘ya’ya masu kyau. To kin ga shi Faruq fari ne sol, watakila za ya iya maneji da ita su jera kafada, ko ya ya Hajiyata?” Ta dunkule hannu ta sakar masa dakuwa, ta ce, “Ungo nan, babban banza kawai, ka tsaya kana irin wannan maganar da kannen bayanka ko kunya baka ji, sahorami, shashasha, kada ka auretan mana wa ya yi asara? Ka san dai ba za ta rasa mai so ba, don ba ta yi kama da ‘yan kananan gida ba”. Ya yi dariya ya ce, “Allah yasa Obasanjo ne Babanta ba Abdulhadi ba, barawon dukiyar al’umma, tunda ya hau kujerar Sokoto ko kwatami bai yiwa al’ummarmu ba, sai baitil malin mu da yake ta handamewa yana kaiwa kasar waje. Ku saurara nan da sati za ku ji shi a hannun EFCC. Don haka sai ku samo min ‘yar sabon Gwamna, tunda ku ke da idon zaben mata ni bani da shi. Amma wannan bana yi, bana so a kai kasuwa, kada nima ina kwance ina shan amarci na ga sammacin Farida….” Ta dauki filet din da ta gama cin gasasshen nama a ciki ta maka masa, ya kauce ya fice da gudu-gudun sa yana kara gaya mata, “Ko da yake Hajiya ki yiwa Hassan din ki kamun ta, gashi nan ya dauko tsawo kwanan nan zamu yi kafada da shi, in har da gaske surukuta kike so da ita”. Da haka Imran ya kashe zancen Mami a gidan amma ban da a zuciyata. Kullum Mami tana nan like cikin raina har mafarkinta nake anyi musu aure da Imran, sai dai ko alama ba wanda na bari ya gane halin da nake ciki. A wannan zuwan da Imran ya yi, gaba daya ya canza mana, ya dawo YA IM din sa, mai son kannensa da son kula su, ko da yake ma mu yanzu bama zaman gidan, kullum safe da yamma muna makaranta. Ni kuwa in na shige daki tun karfe shida na yamma bana kara fitowa balle mu hadu a hirar falo, zan fiddo littafina in tisa karatu sai gobe kuma, in sha lemo in ci biskit in yi kwanciya ta zuciyata kal babu wani Imran a ciki. Na danganta canzawar shi da dadewa da ya yi bai ganmu ba. Ya dauki annual-leave din shi ne na watanni uku. Allah-Allah nake mu kare jarrabawar in yi gidan ubana in huta da wahalar rayuwa, zancen zuwa jami’a da su Azizah ke yi babu shi a wajena, sam bana ra’ayi. A can falo Imran cike yake da mamakin rashin ganina a gidan, ya damu su Azizah da tambaye me nake yi a daki ni kadai, sai su ce a takaice “Karatu”. Ya ce, “Ku bakwa karatun?” Su ce, “Muna yi mana, amma bama iya irin nata. In ta yi (seat) dinmu daya muna kwafe”. Don haushi ya rasa mai zai ce musu, ya dade yana kallon su kamin ya mike ya rufe ido ya balbale su da fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, wai zai kai su ga hukumar makarantar ayi musu daurin shekaru biyar na (malpractice). Sai Azizah ta mere baki ta ce, “Wallahi Ya Im yadda ka je haka za ka dawo, don kuwa duk (invigilators) din samarin ta ne, har wajen zaman mu suke kawo mana amsa, ita ce dai ba ta karba, amma wallahi har principal saurayin ta ne. shima GG da ya sata wankin kashi yanzu in zai rabu da duk abin da ya mallaka zai yarda, in har Zaynab za ta daga ido ta kalle shi…..” Allah sarki, ba ta san yadda zuciyar shi ke tafasa da kalamanta ba da ko kusa ba ta fara ba, da wannan sabon abu da yake ji game da rayuwar Zaynab. Ya ga ba ta da alamun yin shiru balle tunanin dasa aya, idanunsa a rufe gam, ya nuna mata kofa cikin kakkausar murya ya ce, “Ku wuce ku bani wuri mutanen banza kawai tambadaddu, jakai, dabbobi da basu san ciwon kansu ba….” Ya kware ya shiga tari ba

kakkautawa saboda takaicinsu da ya kasa amayarwa, suka fita suna yi mai dariyar kwarewar da ya yi, wai masifarsa ce ta kwarar da shi. Amma Iftihal gorar ruwan (eva) mai sanyi ta dauka a firij ta koma ta kai masa, daga nesa-nesa ta ajiye mai ta zura da gudu. Suka zo suna kyankyasa min yadda su kai, na ce, “Kan ku kuka tonawa asiri, idan ya gayawa Abba fa?” Mu karasa a littafi na 2 Takori
Chapter 24 · 0% Book details