← Book details Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 24

Sashe 18

Girma Ya Fadi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fito fili ya ji ba. Ya yi murmushi kamar bai ji ni ba, ya sake matsowa gareni ya russuna ya dauko min jakata da ta fadi a dalilin karon mu ya miko mani, ya sake cewa, “Kin kwana lafiya Zaynab?” Wannan mugun mutum ne, bani da zabi ban da na daga mishi kai domin ya gama kashe mun jiki da fitinanniyar muryarshi. Ya ce, “Amma ni kin ga ban kwana lafiya ba, Zaynab saboda ke!” Ya ci gaba da mugun murmushin, yana magana ne kasa-kasa yanda in har akwai wani cikin dakin bayan ni dake kusa da shi, duk kasa kunnen shi ba zai ji abin da yake fadi ba. Na kyabe baki na ce, “Allah yai maka magani”. Dariya ya yi ya ce, “Ya yi mana magani baki dayanmu za ki ce Zaynab. Ba gara ni ba, amma ke maganin naki ai mai GIRMA ne, wanda ni kadai ke iya maganta miki, kuma ba zan yin ba, saboda ni mai hankali ne sabanin ke da kuruciya ke dawainiya dake”. Ya sake jifana da mugun murmushin, sannan ya miko min ledar da ke hannunshi, tuni na yi suman tsaye. Wani takaici ya zo ya tokareni a kahon zuci kamar in yi aman zuciya don bakin cikin maganganun da ya yaba mani. Bai kuma bani damar in yi magana ba ya juya yana cewa, “Ki yi maza ki tafi makaranta kin zauna nan kina shirme, tun baki tafasa ba kenan wannan in kika kara shekaru uku a gida ban san me za ki zama ba, gara Abba ya tattaraku da zarar kun kare makarantar nan ya ba wani mai tsautsayin sadakar ku. Balle ke Zaynab irin jarababbun matan nan ne wallahi (nympho), duk wanda ya aure ki ya shiga uku”. Ya juya zai fita yana mun dariyar keta, na ga idan na bari ya fice ban yi wani abu ba na fadi ba nauyi. Idanuna suka ciko da kwalla, bayan kadawa da suka yi suka yi jawur na ce, “IMRAN!” Tunda yake yaran gidan baki dayansu babu wanda ya taba gigin kiran shi da Ya Imran ma balle IMRANAN gabagadi. Iyakacin kowa YA EM, don haka ya hanzarta juyowa cike da mamaki ya dube ni, da na wulwula ledar da ya bani na maka masa, niyyata ta fasa mun wannan bakin dake tozartani, ta illata wannan halittar da ke jan zuciyata ga abin da yake goranta mun a kanshi. Amma sai ya yi saurin dukawa ledar ta wuce ta saman kanshi, kayan shafar da ke ciki kowanne ya yi nasa wuri. Na yi murmushi na ce, “Baka da abin da za ka bani Imran, kamar yadda baka da maganin da zai yi maganin ciwo na, don ‘yan mazan naka da kake tinkaho, bai yi isar da zai isar da jarababbiya kamana ba. Amma ka san ina da surar da in maza dari nake so a rana zan samu, kuma daga yau zan fara, Allah za ka yi nadamar wadannan kalaman da ka gaya min”. Na wuce shi nan dafe da lebban shi yana girgiza kai kamar kadangare yana mamaki na gasken-gaske amma ya kasa magana. Kan mu zo makaranta kiris ya rage in yi kuka a gaban su Azizah, amma na yi kokari na daure na cije ina ta kukan zuci. Hirarrakinsu ko daya ban tsoma baki ba, haka fuskana babu annuri. A cikin aji ana ta aiki, amma ni ban rubuta komai ba, ashe wai har aikin aji (class work) malamin ya bayar suka yi suka gama ni ban sani ba, na yi nisa a tunanin rashin mutuncin da Imran ya yi mani. Malamin yana bin kowa yana sa mishi hannu har ya zo kaina, ya ce, “Ke ina aikin naki?” Na yi firgigit na dube shi, a sannan ne Azizah da Iftihal dake bencin bayana suka shiga zungurina da nasu litattafan, na mika hannu ta karkashin bencin na karbo na fito masa da shi kamar daga jakata na fiddo. Kuskuren da na yi shine, duka biyun na hada masa wato na Azizah da na Iftihal na kuma ba shi ba tare da na duba ba. Ya karba yana dubawa duka biyun, ya daga murya ya ce da ‘yan ajin, “Wace ce Azizah Sa’idu?” Gaba daya aka nuna Azzy da ta yi tsuru-tsuru. Ya sake cewa, “Iftihal Sa’idu Bindawa?” Wata kabila Ngozi ta nuna Ifty. Ya nuna ni ya ce, “Wannan kuma fa ya sunan ta?” Aka ce da shi, “Zaynab Aliyu”. Ya ce, “To ku taso dukkan ku mu isa wurin principal, yau idan uban ku gwamna ne ya daure ni har sai igiya tai rara. Dabbobin banza ni za ku mai da shashasha! Na zo duniyar na kuma je makaranta tun kan ayi cikin uwarku balle ayi tunanin haife ta, shine za ku mai dani sakarai?” Su Azizah suka tsugunna a kasa suna ta ba shi hakuri har da hawayensu, don ba abin da suka tsana a rayuwarsu irin a kai su wurin shugabar makarantar a ce sun yi laifi, don ta san Baba Sa’idu farin sani a take za ta gaya masa. Ni ko ko gezau, don zuciyata ta riga ta kekashe da bakin cikin Imran da ya yiwa zuciyata katutu, don haka don an duke ni gani nake dukan ba zai shiga jikina ba ko da kuwa da bulalar karfe ne. Ya ga ni ban ba da hakuri ba, karewa ma wani gefen daban nake kallo kai ka ce ba dani ake case din ba, kuma dama shine (discipline master) din makarantar baki daya, kowa ya san Malam GG watu Garba Gumel a wurin mugunta babu na biyun shi duk fadin makarantar. Ya ce, “Su Azizah su koma su zauna, ni kuma in taso in biyo shi”. Ban yi musu ba na karkade rigata na bishi a baya, Iftihal ta biyo ni tana ta ba shi hakuri ya daka mata tsawa ya ce ta koma mazauninta, ya kuma sanya monitar ajin Suhaila ta yi mai gadinsu, idan suka fito ta kira shi a waya ta gaya masa. Tafi-tafi ina bin shi kamar jela, ina gayawa kaina na cancanci a hora ni, wauta ce tun farko ta hanani gane Imran ai ba tsarana bane da zan kallafa zuciyata a kansa, don haka kome GG da Imran suka yi min dai-dain su ne. Wani kazamin (student toilet) ya sani in wanke kana tafiya kana karo da busasshen kashi, zarni kuwa ba a magana. Hankalina ya tashi, na soma hawaye amma GG in ban da narka min zagi ba abin da yake. Cewa yake, “So nake in ga matsayin ubanki a garin nan, in tabbatar da cikar ki ‘yar masu kudi. Allah yasa ‘Yar Aduwa ne ya haife ki, da kike wannan bunkasar. Kin ganni nan duk kyawun mace da farar fatarta ba ta burgeni, ko da kuwa ta hurul-eeni ce. Ko dai ta yi karatu ko in bautar da ita, bautar da uwarta da ubanta basu taba yi mata ba. Ke ni ko a aljannah bana fatan Allah ya hadani da mace, ba don komi ba sai don cewa ita ba komi bace face fitina a doron kasa, balle irin ku masu narka-narkan…….sai ku lalata mutum in ba ana wulakanta ku ba….” Na daga idona a hanzarce da hawayena suka kafe karaf, na dubi GG din nan na ‘yan dakikai don ji nake kamar Imran ne yake gaya mun hakan. Ashe dalilin Ya Im kenan na wulakanta ni, kada in lalata shi? Dalilin shi kenan na gaya mun abin da zai bata mun rai in ji har abada bana son mu hada hanya? Sai na ji GG ya yi gaskiya, na shiga kada kai ina mai gasgata kowacce kalma dake fita bakinsa. Na duka na soma ture busassun kashi da tsintsiya, da wani amai ya taho min gabagadi sai na kwararo shi a kafafun GG kore shar da shi kamar atini, don rabona da abinci tun na safiyar jiya. Ji nake kamar hanjina nake amayarwa. Ya daka tsalle ya yi gefe yana kara zagina, ya ce, “Wallahi ba amai ba ko hantarki za ki amayar sai kin wanke toilet din nan fes, kamar tuwo na ya fadi in dauka, in ya so gobe a sallameni daga aikin gwamnati. Wannan ba abun damuwa bane ina da makekiyar gonar gado a Gumel, sai in koma gida in cimma sana’ar Uwa da Uba watau (noma)”. Ya kira wasu dalibai da za su wuce ya ce su dauko mai kujera, ya girkata can gefe daga nesa ya zauna yasa hankici ya toshe hancinsa, lokaci guda kuma yana wanke kafarsa da ruwa a gwangwani da na kwararawa amai. Haka ba yadda na iya na zage na wanke toilets dai-dai har guda shida, na kuma kwashe busasshen kashi na zuba a dustbin, sannan ya sani a gaba muka nufo ajinmu. Lokacin karfe sha biyu da rabi na rana ya rage awa daya a tashi. Na dauka shi kenan GG zai kyale ni, amma me? Ina sa kai zan shiga ajin ya juyo ya dakatar dani ya ce, “Haka za ki shiga musu aji kina warin kashi? Koma ki shanya kanki a rana har sai warin ya gushe tukunna, kneel down”. Na koma cikin rana na zube gwiwoyina idanuna a rufe. Tsayin awa guda da rabi sannan aka kada kararrawar tashi. Su Azizah suka rugo da gudu suka rungume ni suna tattabani suna tambayar abin da ya yi mini, ban ce musu komi ba illa hawaye da nake ta sharewa ina fyace hancina da ya toshe don azaba, suka tabbatar ba za su ji kalma ko daya a bakina ba sai suka hakura suka kyale ni. Muka zo gindin bishiyar dalbejiya inda muke tsayawa Shehu direba ya zo ya dauke mu, shiru-shiru bai zo ba har dalibai suka fara karewa. Su Azizah suka kulu matuka, ni kuwa ta kaina nake da kuguna da ya rike kamar zai balle saboda durkuson da na yi na awoyi da dama. Sai misalin karfe uku na yamma sannan muka hango hancin motar Abba (Vanquish), muka shiga ware ido cike da mamakin yau Abba da kanshi ya zo daukar mu, to ina Shehun? Ashe dan duniyar ne ka janye da motar da Faruq a kujerar mai zaman banza. Suka saki baki suna kallon ikon Allah, don ni har zuwa lokacin kaina a durkushe yake, tunda na yi musu kallo daya
Chapter 18 · 0% Book details