← Book details Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 16

Sashe 9

Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafsat ta amsa mai da cewa "ni fa ba 'kin kar6a na yi ba, kawai dai ba ba son na d'ora masa d'awainiya ne, alhalin kuma kai baka gaza min da komai ba".

"Kar ki ce min haka Hafsat, ba tun yanzu ba na gane cewa duk lokacin da Isma'il ya zo gidan nan kamar yanayin ki yana sauyawa, ko zan san mene ne dalili?"

Cakin sassanyar muryar ta tace "a gaskiya idan nace maka ga dalili 'karya nake, amma duk lokacin da na gan shi sai na ji hankali na bai kwanta da shi ba, amma don Allah idan maganata ta 6ata maka rai ka yi ha'kuri".

"Ba'ki 6ata min rai ba Hafsat, sai dai ina so na sanar dake cewa Isma'il mutumin kirki ne, tun da na ke tare da shi tun a secondary ban ta6a ganin wani abu na ashsha a tare da shi ba, don haka ki kwantar da hankalinki, ba zai cutar da mu ba".

Murmushi Hafsat ta Yi ta ce "insha Allahu zan kiyaye".

Ya ce "haka nake so".

Sun dad'e suna hira a lokacin kafin suyi addu'ar bacci.

Misalin karfe biyu na dare suna tsaka da bacci Aliyu ya farka, ya dinga jiyo motsin mutune daga can harabar gidan , cikin sauri ya tashi Hafsat da ke ta sharar baccinta.

Tana farkawa ya ce mata "Hafsat 6arayi sun shigo gidan nan, tashi maza ki 6uya, ba zan so wani abu ya same ki ba, gara duk abinda zai faru ya faru a kai na ni kad'ai".

"A'a Aliyu ba zan iya bari su yi maka wani abu ba,don Allah ka barni, duk abinda za su yi su yi mana tare".

Ba tare da Aliyu ya saurare ta ba ya nufi wardrobe d'insa ya bud'e ya na cewa "ba mu da lokacin jayayya Hafsat, zo ki shiga cikin nan kuma na ro'ke ki duk abin da zai faru Kar ki you motsin da zai nuna alamar akwai mutum a cikin d'akin nan bayan ni".

Ba ta 'kara yi masa jayayya ba ta shige cikin wardrobe d'in, cikin sauri ya tura 'kofar ba tare da ya murd'a key ba, ya koma saman gadonsa ya kwanta ya ja bargo ya rufa, daidai lokacin da aka turo ,'kofar d'akin aka shigo.

Ummu Aisha
[7/1, 6:34 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

2⃣2⃣

Duk da tashin hankalin da ya ke ciki a lokacin hakan bai sa ya motsa ko ya tashi daga inda ya ke a kwance ba, har suka 'karaso bakin gadon suka zagaye shi.

'Daya daga cikinsu ne ya sa hannu ya d'aka masa duka, cikin sauri ya tashi zaune ya na kallon su.

Su biyar ne, dukkansu sanye da ba'ka'ken kaya, fuskar su sanye da mask.

Ganin babu yadda za'ayi ya iya gane ko mutum d'aya daga cikinsu, ya sa shi yin 'karfin halin ce musu "su waye ku? Me kuke nema a gidan nan da za ku shigo a irin wannan lokacin?"

'Daya daga cikinsu ya amsa masa da cewa "au tambayarmu ma ka ke? To rayiwar ka muka zo nema, ba wani abu ba."

Cikin 'karfin hali ya ce "idan kud'i ku ke so ku fad'i ko nawa ku ke so zan baku amma don Allah kar ku kashe ni.

Gaba d'ayan su dariya su ka sanya sannan wanda ya yi magana da farko yace "ba neman kud'i ne ya kawo mu ba kamar yadda ka ji na ce, mu rayuwarka kawai muka zo nema, don haka bama bu'katar kud'in ka abinda muka zo yi kawai shi muka zo aiwatarwa".

Kafin ya ce wani abu d'aya daga cikin 'yan ta'addar ya soka masa wu'ka a gefen cikinsa.

Wani zazzafan ciwo ya ratsa shi, cikin 'karfin hali ya dinga furta innalillahi wa Inna ilaihir raji'un, hannunsa na da fe da gurin.

Bai ankara ba ya sake jin wani sukan, Hafsat da ke 6oye a cikin wardrobe ta sa hannu ta toshe ba'kin ta idan banda rawa babu abinda jikin ta yake.

'Daya ne daga cikin mutanen ya tashi, ya je gaban Aliyu dake dafe da wuraren da aka soka masa wu'ka, ya tsaya, sai da ya 'karewa Aliyu kallo sannan ya cire mask d'in da ya rufe fuskarsa cikin al'ajabi Aliyu ya dinga kallonsa.

Bakin sa yana rawa da kyar ya iya furta "Isma'il!"

Cikin dakakkiyar murya ya furta "kayi mamaki ko? To ka kwantar da hankalinka, yau zan sanar da kai abinda baka sani ba, shin ko kana da masaniyar ni ne na kashe Hafsat tsohuwar budurwar da za ka aura?

Tun lokacin da idanuwa na suka fara ganin ta sai na ji nan duniya babu wata 'ya mace da na ke so sama da ita, a lokacin da na sanar da ita maimakon ta kar6i tayin soyayya ta sai ta watsa min 'kasa a ido.

Da farko na yi tunanin na ha'kura, amma daga baya sai naga zuciya ta ba zata iya jure ganin Hafsat da Kai a matsyin ma'aurata ba, wannan ne dalilin da ya sa naga dacewar na d'auki matakin hana faruwar hakan.

Tun daga lokacin na shiga tunanin hanyar da ya kamata na bi don ganin na hana yiwuwar wannan auren, har zuwa lokacin da na sami mafita.

Lokacin da Hafsat ta shigo hannuma, bayan na raba ta da abinda kowacce mace ke alfahari da shi, na yi tunanin rabuwa da ita, amma sai naga hakan zai iya zama tonon asiri a gare ni, don haka sai na gama da ita.

A tunani na shikenan matsala ta 'kare, amma ranar da na zo gidan ka naga matarka Hafsat ta yanzu, daga nan tunani na ya sauya, don ina ji a jiki na bazan iya ha'kura da ita ba, don haka masalaha d'aya ita ce a kawar da kai daga doron duniyar gaba d'aya, hakan zai taimaka min wurin samun cikir buri na.

Na yi amfani da wannan lokacin ne saboda na san kai d'aya ne a gidan ita Hafsat ta riga ta yi tafiya.

Kaga daga baya sai in zagaya in auri Hafsat bayan ta gama yi maka takaba, don haka yanzu zamu gama da kai".

Yana gama fad'ar haka ya bawa yaransa damar su yi abinda ya kawo su, Aliyu yana kallo 'kiri-'kiri suka dinga soka masa wu'ka a jikinsa, sai da suka ga ya daina 'kwa'k'kwaran motsi suka yar da shi a cikin jini suka fice.

Ummu Aisha
[7/1, 6:34 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

2⃣3⃣

Kimanin minti goma da fitar su Hafsat ta turo 'kofar wardrobe d'in da ta ke 6oye a ciki ta fito, jikin ta in banda rawa babu abinda ya ke, ba 'karamin tashi hankalin ta ya yi ba sakamakon yanayin da ta ga Aliyu a ciki, jikin ta na rawa ta d'auki wayarta ta kira Hajiya mahaifiyar Aliyu.

Lokacin da Hajiya taga kiran da Hafsat ta ke mata, sai da gaban ta ya fad'i, don tasan haka kawai babu dalili ba za ta kira ta a irin wannan lokacin ba, cikin 'karfin hali ta d'aga, ko sallama ba ta sami damar yi ba Hafsat ta ce "ya mutu Hajiya, wallahi ya mutu".

Cikin 'karfin hali Hajiya ta ce "waye ya mutu?"

Hafsat na kuka ta ba ta amsa da cewa "Aliyu".

Nan da nan Hajiya ta 'kara gigicewa, a lokacin ta fito ta taso Afnan, suka kira Hashim, d'an wani 'kanin Hajiyar ne da ke zaune a gidan, su ka tafi gidan Aliyun.

Lokacin da su ka ga halin da Aliyu yake ciki ba 'karamin firgita su kai ba, don kwata-kwata ba ya cikin hayyacin sa.

Cikin sauri su ka nufi asibiti da shi, ganin yanayin da aka kawo shi a ciki likitocin su ka ce sai an kira 'yan sanda kafin su ta6a shi.

A lokacin Hashim ya je police station mafi kusa ya samo 'yan sanda, nan da nan likitoci suka rufu a kan sa, don ceto rayuwarsa.

Gabad'ayan su suna cikin tashin hankali, duk sun rud'e sai kuka suke. Lokacin da 'yan sanda suka nemi sanin abinda ya same shi, Hajiya ta nuna Hafsat, ta na cewa "gata nan ita ce ta ke yun'kurin kashe shi".

Ba Hafsat ba har Afnan sai da ta gigita da jin abinda Hajiya ta ce, ta ci gaba da cewa "ku kama ta ita ce ta ke son ta kashe min d'a na".

Nan ta ke 'yan sanda suka kama Hafsat suka wuce police station da ita.

★ ★ ★ ★

Gari na wayewa labari ya fara yawo cewar Hafsat ta yi yun'kurin kashe mijin ta, labari har gidajen TV, nan da man abu ya yad'u kamar wutar daji.

Lokacin da labarin yaje kunnen su Uncle ba 'karamin tashin hankali su ka shiga ba, ba su tsaya sauraron komai ba suka wuce Kaduna.

Lokacin da aka je da Hafsat police station aka fara bincikar ta akan zargin da ake ma ta.

Ta fad'i iya gaskiyar abinda ta sani, don haka 'yan sanda ba su yi 'kasa a gwiwa ba su ka bazama neman Isma'il,duk da cewa itama ba'a sake ta ba saboda case d'in yin'kurin kisan kai ba 'karami ba ne.

Lokacin da Isma'il ya sami labarin cewar Aliyu yana gadon asibiti ba 'karamin tashin hankali ya shiga ba, don yasan tabbas Aliyu ya warke to shi kuma tasa ta 'kare.

Bai 6ata lokaci ba ya bazama asibiti, don gane wa idonsa gaskiyar al'amari, daga nan ya d'auki duk matakin da ya kamata, don ganin ya kawar da rayuwar Aliyun.

Lokacin da ya shiga asibitin bai sami ganin Aliyu ba saboda matakan tsaro da akasa mai, duk nacin sa haka ya ha'kura ya juya gida, zuciyar sa cike da mamakin abinda Hajiyar Aliyu ta gaya masa na cewa Hafsat ce ta yi yun'kurin kashe shi, bayan shi a iya saninsa Hafsat ba ta gari, kuma har suka shiga gidan suka gama abinda ya kai su ko alamar motsin mutum su ji ba bare su gan ta.

A hanyarsa ta komawa gida kuma 'yan sanda su ka cafke shi.
Chapter 9 · 0% Book details