← Book details Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 16

Sashe 14

Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau da asuba bayan na tabbatar da fitar Alhaji masallaci na je d'akin, sai da na tabbatar tana cikin toilet na shiga na d'auko jakar da nufin na shigar da ita d'akinta, kinga idan ya nema ya rasa, zai tuhume ta idan ya ganta a d'akinta daga ranar mutuncinta zai zube a idonsa.

Amma abin takaici ina zuwa sai na tarar da d'akin a rufe da makulli, sai na dawo da niyyar mayar da jakar inda na d'auka, na tarar ta fito daga band'akin, na rasa yadda zanyi da jakar kud'in yadda Alhaji ba zai zarge ni ba.

Yanzu haka zancen da nake miki Hafsat na police station tun safe, ni kuma ga jakar kud'in a hannuna na rasa yadda zanyi da ita, shi yasa nake son ki bani shawarar yadda zanyi."

Sai da Naja'atu ta nisa sannan ta ce "a gaskiya banji dad'in abinda kika aikata ba, ki sani manzon Allah (S.A.W) yace imanin d'ayanku baya cika har sai ya sowa d'an uwansa abinda ya so wa kansa.

Na tabbar ba ke akan kanki ba ko ni da nake 'yar uwarki baza ki so ayimin irin wannan sharrin ba, me yasa zaki biyewa rud'in zuciya?

Ni tun da aka auro Hafsat d'in nan banga wata matsala daga gareta ba, bare kuma matar da ba tare kuke zaune wuri d'aya ba, sai dai ta zo ta koma.

A gaskiya Aunty Hadiza ba ki kyauta ba, ita fa kishiya abokiyar zama ce, musamman idan Allah ya had'a mutum da ta gari, ni yan......."

Kasa 'karasa maganar tayi sakamako ganin Alhaji Nasir da ya shigo ya na bin Hadiza da wani irin kallo mai dauke da tuhuma.

Nan take jikin Hadiza ya d'auki rawa, cikin rawar murya ta ce "lafiya Alhaji, ko wani abin ne ya ke faruwa?"

Ya dube ta cike da takaici ya ce "kin bani mamaki Hadiza, kin ci amanar yardar da nayi miki, amma ina so ki sani wannan abin da ki ka aikata bani ko Hafsat ki ka cuta ba, kanki ki ka cuta, don kin zubar da mutuncin ki a ido na, kuma tashi ki d'auko min kud'i na."

Jiki a sanyaye ta tashi ta shiga d'akinta, jim kad'an sai gata ta fito hannunta ri'ke da jakar ta mi'ka masa.

Yana kar6a ko kallonta baiyi ba ya shige d'aki da jakar, yana ajjewa ya juya ya fita, kai tsaye police station ya nufa.

Bai wani sha wahala ba aka fito da Hafsat, wadda cikin kwana d'aya tayi wata irin rama, ko kallonsa bata yi ba ta nemi hanyar ficewa daga cikin wurin.

Da sauri ya taradda ita, yana yi mata magana, ita kuwa ko saurarensa bata yi ba, ta ci gaba da tafiyarta, zuwa ya yi ya shiga motarsa ya zo gabanta ya tsaya yana cewa "Hafsat shigo mu tafi "

Sai sannan ta juya ta kalle shi, ta ce "in shigo mu tafi Ina fa?"

Ya bata amsa da cewa "gida mana."

Wani irin murmushi na takaici tayi, ba tare da ta ce masa komai ba tayi gaba, tana zuwa titi ta tari adaidaita, ta shige.

Ummu Aisha
[7/1, 6:45 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

Page d'in yau naku ne

Aisha Ibrahim (Maman twins)
Maman Noor

Allah ya ba 'kauma

3️⃣8️⃣

Mai adaidaita bai sauke ta ko Ina ba sai a sharad'a 'kofar gidan Goggo A'i, sai da ta shiga ciki tayiwa Goggo bayani, aka aiko masa da kud'insa.

Duk wanda ya danganci Hafsat wannan abinda ya faru bai masa dad'i ba, ganin yadda Alhaji Nasir ya rufe ido, ya nuna ba sani ba sabo.

Tun bayan abin yake sintirin ba da ha'kuri amma Hafsat ta 'ke'kasa 'kasa ta ce ta gama zaman aure da shi, kuma babu wanda ya takura mata, tunda shi ya jawa kansa.

Ranar da ya kira ta a waya, da farko kamar kar ta d'auka, sai kuma dai ta d'auka, ha'kuri ya fara bata yana cewa "duk da nasan ni mai laifi ne a wajenki amma na ro'ke ki don girman Allah kiyi ha'kuri.

Ni kaina daga baya na fahimci cewa abinda nai miki ban yi miki adalci ba, ina so ki sake bani dama, nayi miki al'kawari irin hakan ba zata 'kara faruwa ba, ki yi ha'kuri ki dawo d'akinki."

Ciki n takaici Hafsat ta ce "ai in dai nice na bar gidanka kenan har abada, domin a duk lokacin da na bud'e ido na ganka zuciya ta ba zata daina jin zafin abinda ka aikata min ba, kuma dama na gaya maka, akwai ranar da zaka ka yi nadamar abinda ka aikata min, to gashi ta zo.

Abu d'aya da nake bu'kata daga gareka a yanzu shine shaidar saki don wallahi na gama zaman aure da kai."

Duk nacin Alhaji Nasir dole ba don ya so ba sai da ya saki Hafsat. Tun bayan kammala iddarta ta 'ki sauraron kowa a masu zuwa suna son ta, don tace ita kam ta gama aure har abada.

Lokacin da Aliyu ya sami labarin mutuwar aurenta, shima baiyi 'kasa a gwiwa ba, sai da ya dawo, don su mai da aurensu, duk da shima lokacin ya yi wani auren, amma fur ta 'ki.

Sai ta nuna masa cewa ita a yanzu babu maganar aure a tsarin rayuwarta.

Shima Abubakar bai yi sanya ba, kuma ya yiwa kansa al'kawarin wannan karon duk rintsi duk wuya, ba zai ha'kura da ita ba, ba zai yiwu yana kallo wani ya sake d'auke ta ba.

Ummu Aisha
[7/1, 6:46 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

3️⃣9️⃣

A haka harta kammala karatunta, tayi house manship ta gama, a yanzu haka service take a Abdullahi wase specialist hospital.

Shima Uncle Taheer tuni ya sami transfer, ya dawo BUK da aiki, don haka yanzu a Kano suke da zama.

AN DAWO LABARI

Bayan gama dogon tunanin abubuwan da suka faru a rayuwar ta, ta dinga share hawaye, wannan ranar duk iya satar bacci ya kasa sace Hafsat, daga 'karshe da taga damuwa ba zata barta ta yi barci ba, sai ta shiga toilet ta d'auro alwala, haka ta kwana tana sallar nafila da kuma karatun Qur'an.

Washe gari sukuku ta tashi, ba walwala, zuciyarta a cinkushe, da tasan irin hukuncin da iyayenta za su yanke mata kenan tun farko da ta sami wani a masu sonta ta aura, domin kaf mazan da ta aura babu wanda abinda abinda yayi mata ya fi tsaya mata a rai irinsa.

Aunty kuwa tun bayan da ta kammala duk wani abu da tasan zata yi, ta d'auko paper da biro ta fara rubuta abubuwan da suka kamata a saya na auren Hafsat d'in.

Tana kallon Aunty tana ta harkokinta cikin farin ciki, wannan ya 'kara 'kuntata zuciyarta, don tasan ko tayi magana babu mai fahimtar ta.

Ranar juma'a bayan sallar juma'a jama'a suka shaida d'aurin auren Abubakar Halliru Buba da Hafsat Sani Buba.

Ranar Hafsat tayi kuka kamar ba gobe, shi kuwa angon yana can cikin farin ciki da walwala.

Aunty ta ro'ki a bari sai bayan sati biyu ta tare, saboda abin ya zo musu a 'kurarren lokaci, basu gama shirye-shiryen da ya kamata ba.

* * * *

Shi kuwa angon ba 'karamin d'auki ba dad'i sukai da matarsa ba, lokacin da ta sami labarin auren, tamkar sabon kamun hauka haka ta dawo masa, ta tayar da hankalinta sosai, shima kuma ta tayar masa, don sai da ta kai ga ya kira yayanta ya tsawatar mata, sannan ya sami sau'kin abin.

Daga gefe kuma ga mahaifiyarsa da ta sa shi a gaba, don itama bata so aka maida aurensa da Hafsat ba don so tayi ya auro 'yar 'kanwarta, shi kuma ya 'ki.

Wanna abu ya 6ata mata rai, ganin babu yadda za ta yi yasa ta h'akurin dole, don Baffa Halliru yayi mata takara sosai, akan idan ta sake ya ji abinda bai gamsar da shi ba, to ta sani sai ranta ya 6aci.

Wuyar abu sai dai in ba'a saka masa rana ba, sannu a hankali har ranar tarewar Hafsat a gidan Abubakar ta yi.

Duk da fushin da take hakan bai hana Aunty shirya 'kayatacciyar walima ba. Wannan karon ma mutanen Rumoh da yawa sun sami halartar bikin.

Da misalin 'karfe biyar na yamma aka kawo motoci d'aukar amarya, ba 6ata lokaci, aka fito da ita aka raka ta gidan mijinta da ke Court road.

Gida ne ginin zamani mai d'auke da part biyu, sai wani da bai kai sauran girma ba daga can bayan su wanda mutum zai iya shiga d'aga kowane part.

Gidan amarya Hafsat yayi kyau sosai, ga shi ya sha gyara, ita kanta Hafsat da ta ga yadda aka 'kawata mata gidan bata san lokacin da hawaye ya dinga zuba daga idanuwa ta ba, don ba karamin 'ko'kari su Aunty su kai ba, ita kam ba ta san da me za ta saka musu tarin alkhairansu a gare ta ba.

Haka 'yan rakiyar amarya sukai ta zaga gidan, suna sakawa wurin albarkacin.

Kafin wani lokaci duk an watse, sai iya amaryar ita kad'ai aka bari zaune cike da takaicin dawowa gidan Abubakar a matsayin matarsa.

Tana zaune a inda aka barta har lokacin da aka Kira sallar magriba, ta tashi ta d'auro alwala, ta gabatar da tata sallar, bayan ta gama addu'o'n da zata yi, tayi azkar, ta tashi tasa makulli ta kulle part d'inta, don bata Abubakar ya ce zai shigo mata, saboda a yanzu babu mutumin da ta tsana sama da shi a rayuwarta.

* * *

Misalin goma da rabi na dare Hafsat na kwance akan gadonta, duk da ba barci take ba, ga mamakin ta sai ji tayi an turo 'kofar d'akin an shigo, tana duba gurin Abubakar ta gani yana tunkaro wurin da take jikinsa sanye da kayan bacci, milk colour, yana ri'ke da leda mai tambarin Yahuza Suya a hannunsa.

Kai tsaye gefen gadon ya nufa, ya so wuri ya zauna, idanuwansa a kanta yana kallonta.

Ummu Aisha
[7/1, 6:46 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*DUK KANWAR JA CE*
Chapter 14 · 0% Book details