← Book details Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya jima yana kallonta kafin daga baya ya yi gyaran murya ya fara magana cikin sigar rarrashi "Hafsat duk da nasan cewa ni mutum ne mai tarin laifi a gare ki, hakan bazai sa na kasa sake rak'on alfarmarki a karo na babu adadi ba, Hafsat ki dubi girman zumuncin da ke tsakanin mu da kuma yaronmu ki amince a mai da aurenmu, ni kaina nasan cewa abin da nayi miki a bayan ban kyauta miki ba, amma wani abu da baki sani ba ni kaina da na aikata abin na fi ki jin baqin cikin faruwar hakan, duk abinda ya faru ya faru ne bisa dole ba da son raina ba, kiyi haquri Hafsat ki manta da abin da ya riga ya wuce, nayi miki alk'awarin irin hakan ba zata sake faruwa a gaba ba.

Na tabbatar ko iyayenmu zasu ji dad'in faruwar sake ganinmu a matsayin ma'aurata".

Wani murmushi tayi da ke nuna tsantsar takaici, sannan ta ce "Sau nawa zan gaya maka cewa ka daina tunanin ni Hafsat zan koma gidanka?

Idan ma mafarki kake ya kamata ka farka, har abada ni Hafsat na gama zaman aure da mutum azzalumi irinka, ka fita daga hanya ta, ka daina takura min domin har abada bazan ta6a komawa gidanka ba, a lokacin da ka tashi tazarta ni ai mantawa kayi da zumuncin namu, sai yanzu da kake son sake cuta ta sannan ka tuna cewar ni 'yar uwarka ce?

To don Allah ka fita daga hanyata gidanka dai kam bazan koma ba, ni ka ga tafiya ta sai an jima".

Tana gama fad'ar haka ta juya zuwa cikin gida ta barshi a tsaye yana kallonta cikin takaicin maganganunta.

Babu yadda zaiyi haka ya shiga mota ya tafi, sai dai ya k'udurce a ransa cewa wannan karon duk tsanani ba zai bari ta kubce masa ba.

Lokacin da ta koma cikin gida tayi matuqar qoqari wurin b'oye damuwarta, haka ta ci gaba da harkokin gabanta.

An d'ebi kwanaki da yawa ba a k'ara yi mata maganar aure ba, hakan yasa hankalinta ya kwanta, taci gaba da harkokinta cikin kwanciyar hankali.

A gurin aikinta ma ta mai da hankali sosai don ganin al'umma sun amfana da baiwar ilimin da Allah (S.W.T) ya yi mata.

Sai dai duk da haka tana fama da wasu daga cikin abokan aikinta maza da suke nuna bak'atarsu ta aurenta duk da babu wanda ta bawa fuska a cikinsu.

Shima Abubakar tun ranar da ya zo bai k'ara zuwa gidan ba ma, bare ya dame ta, hakan ba qaramin dad'i yayi mata ba, don har ga Allah ita babu batun aure a tsarin rayuwarta.

―― ―― ――

Ranar wata lahadi tun wajen 9:00 na safe Uncle ya fita daga gida sa6anin kowane lokaci, don idan ranar lahadi ce baya fita sai lokacin sallar azahar, idan ya yi sallah ya dawo ba zai sake fita ba sai la'asar, to kuma ba zai dawo gida ba sai bayan sallar isha'i.

Tun da ya fita bai dawo gidan ba sai bayan azahar.

Da daddare bayan yara sunyi bacci Aunty ta shigo d'akin Hafsat, wadda itama har ta kwanta a lokacin ta ce ta je Uncle d'inta na son yin magana da ita.

Haka kawai ta ji gabanta ya fara fad'uwa duk da bata san dalilin kiran ba, amma sam hankalinta ya kasa kwanciya.

Dogon hijabi har qk'asa ta sa a kan kayan baccin da ke jikinta ta fito domin amsa kiran da akai mata.

Ummu Aisha
[7/1, 6:25 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦

DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zanan lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛

4⃣

Zaune ta same shi, da kofin coffee a hannunsa, ta sami gefe ta zauna tana jiran ya gama abin da ya ke.

Sai da ya gama shan coffee d'in ya ajje cup d'in a kan centre table sannan ya mai da hankalinsa gare ta.

"D'azu Baffanninki Sa'idu da Shehu sun zo, kuma ba akan komai ba sai akan maganar aurenki, Hafsat an baki lokaci iya lokaci don ki fitar da miji amma abin ya gagara.

Abin da ya faru abaya ya riga ya wuce, kuma hakan ba zai zama hujjar da za'a zuba miki ido ki zauna haka babu aure ba.

Shi mutum duk abin da ki ka ga ya faruda shi to dama yana daga cikin qaddararsa, kuma mutum bai isa ya sauya abin da aka qaddaro masa ba.

A yanzu haka mun yanke shawara ranar juma'a idan Allah ya kaimu za'a maida aurenki da Abubakar.

A firgice ta d'ago tana kallonsa saboda yadda maganar ta zo mata a bazata, tuni ta ji kanta ya sara mata wani irin ciwo, idonta ya cika da hawaye sai dai tayi qoqarin hana su zubowa.

Tun daga nan bata k'ara fahimtar abin da yake cewa ba har zuwa lokacin da ya umarce ta da tafiya.

Ai tana shiga d'aki ta fashe da kuka mai cin rai, ba ta dad'e da shigowa d'akin ba Aunty ta shigo itama.

Gefen gado ta samu ta zauna sannan ta umarci Hafsat da ta tashi zasuyi magana, babu musu ta tashi sai dai har lokacin hawaye bai bar zuba daga cikin idanunta ba.

Cikin sigar rarrashi Aunty ta ce "haba Hafsat a tunanina kuka ba shine mafita ysnzu a gare ki ba, ya kamata ki dage da addu'ar Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gare ki, karki manta wad'anda suka zartar da wannan hukuncin iyayenki ne, kuma kinsan ba za su ta6a aikata wani abu a gareki da nufin cutarwa ba, sannan ko ba komai Abubakar d'an uwanki ne, duk wani miji da zaki aura ba zai fi shi sanin ciwonki ba.

Kar ki duba abinda ya faru a baya a tsakanin ku, ke kanki kin san halin mahaifiyarsa, kuma ko babu komai ai gaskiya ta bayyana cewa shima ba a son ransa hakan ta faru ba, sai don babu yadda zai yi ya aikata bisa tursasawar mahaifiyarsa".
Babban abinda na ke so da ke shine ki kwantar da hankalinki, kuma ki dage da addu'a Allah ya ku6utar da ke daga sharrin duk wani mai sharri.

Tabbas abubuwa marasa dad'i sun faru a rayuwar aurenki amma ki sani Allah yana jarraba Bayinsa muminai ta hanyoyi da yawa, don haka nake shawartar ki da ki daure ki ci wannan jarrabawar.

Ta dad'e tana kwantar mata hankali, har sai da taga ta daina kuka sannan ta tafi ta kwanta.

Gabad'aya tsawon daren bacci ya qauracewa idanunta, don haka ta tashi tayo alwala tazo ta fara gabatar da nafila don kai kukanta ga Rabbissamawati.

Wai shin wacece Hafsat?
Mene ne matsayin Abubakar a wurin ta?
Mene ne dalilinta na qin aure?

Duk wannan amsar tana gareni, kuci gaba da biyoni domin jin yadda za ta kasance.

Comments d'inku shi zai qara min qarfin gwiwa wurin cigaba da rubuta labarin.

Ummu Aisha
[7/1, 6:25 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦

DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛

5⃣

ASALIN LABARIN

Garin Rumoh da ke k'aramar hukumar Sumaila gari ne da ya ya had'a al'ummar Fulani da kuma maguzawa, Allah yayiwa mazauna garin albarkar noma, da kiwo.

Malam Buba asalin mutumin garin ne tun iyaye da kakanni, yana zaune a cikin garin da matarsa mai suna Goggo Habi da 'ya'yansu.

Malam Buba bafulatani ne usul, kuma makiyayi ne domin Allah yayi masa arzik'in shanu da awaki, sannan duk da haka idan lokacin noman damina yayi nanma ba'a barshi a baya ba.

Babban d'ansa shine Halliru yana da mata biyu Inna Kulu da Goggo Maryo, sai mai bi masa Shehu shima matansa biyu, sai Sa'idu yana da mace d'aya sannan sai qaraminsu Sani shima tarsa d'aya, sai mata guda biyu, kowacce tana gidan mijinta.

Duk mazan kowa a cikin gidan yake zaune da iyalansa, kowa b'angarensa da ban.

Duk 'ya'yan malam Buba kowa ya tashi da irin sana'ar Baffansu wato noma da kiwo, sa6anin Sani da tun yana qarami yake da sha'awar kasuwanci, don tun yana da shekaru goma sha biyar ya kafa tireda a qofar gidansu, kuma Allah cikin ikonsa sai ya kawo masa bud'i cikin sana'arsa, don har ta kai ya mallaki babban shago a cikin garin, kuma duk da haka yana had'awa da kiwo, don haka sai ya zama zakaran gwajin dafi a cikin gidansu.

Ya fara soyayya da wata 'yar maqoftansu mai suba Sa'a, amma sai dai su ba fulani bane kanawa ne, wannan ne ya tashi gankalin Inna Kulu domin ita burinta ya auri qanwarta mai suna Ma'u.

Tayi iyaka qoqarinta wajen ganin maigidanta ya shiga maganar amma fur ya k'i, yace ba shi zai zaunawa Sani da matarsa ba, kuma tun da iyayensu basu hana shi auren wadda ransa yake so ba, to shima bashi da hurumin tursasa shi ya auri macen da ba ya ra'ayi.

Dole ba don ta so ba ta hak'ura, saboda babu yadda za ta yi, amma ta k'ullaci wannan auren na Sani sosai a ranta, don ta so ace k'anwarta ce aci arzik'i da su ganin yadda harka ta bud'e masa sosai.

Wannan dalilin ne yasa tun daga lokacin da akai auren Sani da Sa'a ta d'ora mata karan tsana, don ma ita Sa'an mace ce mai matuk'ar hak 'uri da kawaici, duk abinda za ta yi mata baza ta d'aga kai ta dube ta ba, bare ta tanka mata.

Shekaru biyu da yin bikinsu Sa'a ta haifi yaro namiji aka saka nasa suna Ibrahim, bayan shekaru uku ta haifi mace aka sa nata Hafsat amma suna kiranta Hafsi, daga nan sai Maryam sai Usman.

Tun lokacin da aka yaye Hafsi rik'onta ya koma hannun kakarta wato Goggo Habi.

Kuma tun Hafsi na da shekaru biyar a duniya Goggo ta sanar da 'ya'yanta ko bayan ranta Hafsi bata da miji sai Abubakar d'an wajen baffa Halliru.

Wannan magana ta so tada fitina a gidan don Inna kulu mahaifiyarsa cewa tayi bata amince ba.

Amma da yake Baffa Halliru jajirtacce ne dole ta hak'ura don babu yadda za ta yi.
Chapter 2 · 0% Book details