Sashe 16
Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da ya shigo 6angaren Hafsat a parlour ya same ta zaune da computer a gaban ta, daga dukkan alamu wani abu mai muhimmanci ta ke.
Sai da ya sami wuri ya zauna ta yi masa sannu da zuwa, ba tare da ta d'aga kai ta kalle shi ba, ta ci gaba da abinda ta ke, ta d'auki kimanin mintuna ashirin da wani abu kafin ta gama, zuwa wannan lokacin shi hankalinsa ya yi nisa a program d'in da yake kallo a tashar Arewa.
Ko da ta gama bata tashi a gurin ba, sai dai rufe computer da tai, itama sai ta mai da hankalin ta kan kallon.
Bayan sun gama kallon, da kansa ya shiga kitchen ya d'auko plate da cups, ya juye abinda ya shigo da shi, sannan ya umarce ta da ci.
Da farko kamar K
Kar ta ci, sai dai kuma tana tuno al'kawarin da ta yiwa Goggo, ta tashi, ta shiga kitchen ta wanko hannu ta zo ta zauna suka ci.
Har 'karfe goma suna parlour, sannan suka tashi, kai tsaye toilet ta wuce, don yin wanka da alwala, yayin da shi kuma ya tafi part d'insa don shiryawa.
Bayan ta fito sai da ta tsaya ta shafa bady lotion a jikinta ta shafe jikinta da turare, sannan ta saka rigar bacci, sai ta d'aura zani a Kai tasa hijab don gabatar da shafa'i da wuturi.
Tana tada salla ya shigo, d'akin da sallama a bakinsa, ganin tana salla sai ya sami gefen gado ya zauna, har ta idar, sannan ya tashi ya jagorance su salla raka'a biyu.
Bayan sun kammala addu'o'in su, sai kowanne ya nemi makwanci, a wanna rana, wanna dare abubuwa da yawa sun faru, wanda ban san yadda zan fasalta su ba, sai dai zan bar kowa ya 'kissima a ran sa.
Abubakar har kukan farin ciki yayi, ya da'de da manta cewa ana samun irin wanna farin cikin a cikin aure, sai yau da Allah ya dube shi da idon rahama ya dawo masa da 'yar uwarsa, kuma masoyiyarsa cikin rayuwarsa.
Washe gari da safe duk wani aiki na gida tare suka yi shi, don yana ji a zuciyarsa da akwai hali ko numfashi ba zai bar ta tayi da kan ta ba.
Da kyar ya daure ya fita office, gudun kar ya sami matsala a wurin aikinsa.
Tun daga wannan lokacin suka sami fahimtar juna, su ke zaman lafiya a tsakanin su.
Daga ranar da Zainab ta fahimci sun daidaita ta k'ara tayar da hankalinta, don tana ganin ba ajin ta bane a ce kamarta tana zaune da kishiya.
________________________
Zaman lafiya da kwanciyar hankali ne ya ke gudana a tsakanin Hafsat da Abubakar, a wannan lokacin ne Hafsat ta fahimci ta na da shigar ciki, sai dai ba ta sanar da Abubakar ba.
Har sai da cikin ya kai tsawon watanni uku sannan ya sani sakamakon yawan rashin lafiyar da ta ke yi, har suka dangana da asibiti, anan likita ke sanar da shi batun cikin.
Fad'ar irin farin cikin da yayi ma 6ata baki ne, don sai yake ganin kamar a lokacin ne za'a fara yi masa haihuwa, kasancewar Uncle Tahir ya hana su Saleem, ya ce su yi addu'ar Allah ya Basu nasu, amma wannan na sa ne.
_Ummu Aisha_
[7/1, 6:48 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*DUK KANWAR JA CE*
*Story and Writing by*
*Ummu Aisha*
*ZAMAN AMANA WRITER'S Z.A.W* _(Gidan Zaman lafiya da Amana insha Allah)_🤜🤛
4️⃣4️⃣
____________________________________
Hafsat ta ci gaba da rainon cikinta, tare da kulawar mai gidanta, har watan haihuwarta ya kama, zuwa wannan lokacin sun gama duk sayayyar haihuwa, ranar haihuwar kawai suke jira.
Ranar lahadi tun da ta tashi da asuba ta ke jin alamun ta fara labour, zuwa 'karfe takwas na safe abin ya kankama sosai, nan da nan suka tafi asibiti, cikin ikon Allah ko awa d'aya da zuwa ba su yi ba ta haifi yarinyarta mace, not take Abubakar ya yi wa Aunty waya, ya kira mutanen Rumoh ya sanar da su.
Cikin lokaci 'kalilan sai ga Aunty a asibitin, bakinta kamar gonar audiga don faran ciki.
Zuwa Azahar aka sallame su, don an tabbatar da lafiyarsu ita da baby'n, suka koma gida.
Lokacin da labarin haihuwar ya je gidansu can Rumoh kuwa, Innar su Abubakar cika ta dinga yi tana batsewa, kowa sai da ya fahimci cewa ba ta farin ciki da haihuwar.
_____________________________________
Ba'kin cikin da Zainab ta yi akan haihuwar nan ba d'an kad'an bane, ita a kullum tunaninta yadda za ta raba Hafsat da gidan, ba ta kai ga cimma nasara ba, sai kuma ace Hafsat ta haihu.
A ranar da daddare ta sami Abubakar a d'akinsa zata yi masa hauka, ya dakatar da ita da cewa "saurara Zainab, me ki ka d'auke ni ne? Mahaukaci ko me?
Duk abinda ki ke don kinga ina rabuwa da ke sai aka ce miki ban san ciwon kai na ba?
Ko kin zaci ban san ki na family planning ba? To tun da ke baki shirya Haifa min yara ba Allah ya bani wadda za ta iya meye damuwarki?
Ki fita daga nan ki bani wuri tun kafin ranki ya 6aci."
Ganin yanayin fuskarsa, yasa ta juyawa jiki a sanyaye ta fice, ta na shiga d'akinta ta fad'a akan gado ta fashe da matsanancin kukan ba'kin ciki.
A 6angaren mai jego kuwa suna cikin farin ciki da walwala, ga kulawar ta musamman da suke samu ita da baby'n ta daga 'yan uwa da shi kansa maigidan.
Sati ya zagayowa akai suna, yarinya ta ci sunan Goggo, wato Habiba, ana kiran ta da Muhibba, shagali sosai akai na sunan, anan na had'u da su Maryam wada, Badi'a, Maman twince, Maman Abba, Maman Noor, Salamatu, da duk 'yan *DUK KANWAR JA CE* fans, sun zo da abin arzi'kinsu, ana ta kashe salfie da mai jego.
Taron suna ya tashi lafiya, kowa yana son barka, sai gab da magariba in 'kokarin tafiya na had'u da Rashma, da Princess sun zo wai zaman jiran 🅱️K suke, ganin dare na neman yi musu suka taho, suka barta.
Washegari mutanen Rumoh suka tafi, kowa d'auke da gift d'in da aka raba, na sunan Baby Muhibba.
_Ummu Aisha_
[7/1, 6:49 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦

4️⃣5️⃣
🔚🔚🔚🔚🔚
Hafsat ta ci gaba da rainon 'yar ta cikin kwanciyar hankali, yarinyarta tana ta 'kara girma.
Bayan ta yi arba'in da sati d'aya ta shirya tafiya Rumoh, don gaggaisawa da 'yan uwa, ta had'a tsaraba sosai, Abubakar da kansa ya kaita da nufin bayan kwana uku zai aika a d'auko ta.
Sun sami Inna Kulu kwance babu lafiya, take Abubakar ya d'auke ta zuwa asibiti, bayan gwaje-gwaje, an tabbar da ta na da ciwo suger, nan dai aka basu magunguna, aka fad'a musu irin abincin da ya kamata ta dinga ci.
A ranar ya juya, ita kuma Hafsat ta zauna, washegari ta dinga ziyartar 'yan'uwa, kowa ta je da abin alkhairin da zata ba shi, kowa yana san barka da ita.
Ranar da zata tafi, dagewa tayi sai ta tafi da Inna Kulu don tana bu'katar kulawa ta musamman, da farko Innar ta ce babu inda zata, amma sai Saude babbar 'yar ta a mata dake kula da ita ta ce su je, shine ta amince, amma a ranta ta 'kudurce ba zata zauna a wurin Hafsat d'in ba.
Babu yadda Abubakar bai yi ba akan su sauka a 6andaren Hafsat, amma Inna Kulu ta 'ke'kashe 'kasa ta ce ba zata zauna a wurin ta ba.
Dole suka sauka a part d'in Zainab, ita kuma sai ba ta so hakan ba, don dai babu yadda ta iya ne.
Washegari da wuri suka fita asibiti bisa jagorancin Zainab, bayan ta shirya musu abin karyawa ta kai musu, abin mamaki a lokacin Zainab ko fitowa bata yi daga d'akinta ba bare a sa ran za ta girka wani abu, ko don marar lafiyar.
Asibitin Nasarawa aka kai ta, bayan binciken likitoci aka bata gado.
Kwanata biyar a asibiti aka sallameta, bayan sallamar ne Abubakar ya ce ba zasu tafi ba, sai jikinta ya 'kara murmurewa.
A wannan lokacin ne Zainab ta nuna musu asalin rashin mutuncin ta, dai-dai da abincin da Inna Kulu za ta ci 'kiri-'kiri ta ce ba zata iya girkawa ba, kasancewar an hana ta cin kowane abinci, saboda larurarta.
Idan kuwa suka fito parlor ta yi ta mita kenan an 6ata mata wuri, babu girma babu arzi'ki suka tattara suka koma gun Hafsat.
A nan suka ga kulawa ta sosai, haka tayi ta tattalin Inna, kamar ta raba ta da ciwon.
Bayan an tabbatar da samuwar lafiyar Inna suka koma gida, cike da takaicin abubuwan da Zainab ta yi musu.
Shi kuwa Abubakar ashe dama zuba ido ya yi yaga iya gudun ruwanta, aikuwa washegarin ranar da su Inna suka tafi, ya dan'ka mata takardar saki, don yace ba'a haifi matar da zata wula'kanta masa uwa ya zauna da ita ba ko wacece ita.
________________________________________
*Bayan wasu shekaru*
Zuwa wannan lokaci abubuwa da yawa sun faru, wasu na dad'i, wasu akasin haka.
Tuni Hafsat ta fara aiki a asibitin Abdullahi Wase, tun kammala bautar 'kasarta suka rik'e ta, zuwa wannan lokacin ta haifi yara biyu bayan Muhibba, akwai Fatima sai kuma Musaddiq, da Abubakar ya yiwa kansa takwara.
Tuni Inna Kulu ta zubar da makaman ya'kin ta, don duk yadda taso takurawa rayuwar Hafsat Abubakar ya 'ki bata dama, dole ta ha'kura, ga kuma arzi'kin Hafsat d'in da ta ke ci, don kwata-kwata bata da 'kyashi.
Kusan duk lokacin da aka sami hutun makaranta ana Kawo Muhammad ya yi hutu, shima Saleem yana zuwa, wani lokacin har weekend ya ke zuwa.
Soyayya mai tsabta suke gwadawa junansu, sannan suna kula sosai da tarbiyyar yaransu.
Tsakaninsu da iyaye da 'yan uwansu na Rumoh kuwa sai san barka, suna iya 'ko'karisu wurin kyautata musu.
*Alhamdulillah*
_Anan na kawo 'karshen wannan littafi, kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min._
_*Sai kun jini a cikin wani sabon novel d'in da yaddar Allah,*_