Sashe 4
Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kyar ya samu tayi shiru, amma zuciyar ta cike take da tsoron kar a gane abinda ya faru a tsakaninsu don babu irin gargad'in da Goggo bata yi ma ta ba, kuma ta yi k'ok'arin ganin ta fahimtar da shi amma sam yak'i fahimtar ta.
Sai da ruwan yayi zafi sosai sannan ya surka ya saka ta a ciki, bayan ta dad'e ya zubar ya k'ara sirka wani, sai da ya tabbatar ta ji sauk'in ciwon jikin ta sosai sannan ya rakata har d'kin Goggo ta kwanta ya juya ya tafi zuciyarsa cike da farin ciki.
Washe gari da safe haka ta tashi sam bata jin dad'in jikinta sai ta daure don ta na gudun kar a fahimci halin da take ciki, ko lokacin da za ta yi wanka sai da ta cika baho da ruwa mai zafi ta kai ban d'aki sai da ta k'ara gasa jikinta sosai, kuma hakan ya taimaka mata sosai don ba k'aramin dad'in jikinta ta ji ba.
Zuwa bayan sallar la'asar Goggo ta dawo, lokacin tuni Hafsi ta warware kamar babu abun da ya faru.
Tun daga wannan lokacin Abubakar ya sami dama, kusan kullam yana mak'ale da ita, har aka kira su domin tafiya bautar k'asa.
Wani abokinsa ne ya fara sanar da shi cewa Bauchi State akai posting d'in sa, tabbas ya yi farin ciki sosai kasancewar yana Arewa ba a tura shi kudu ba.
Sun shiga camp lafiya sun fito lafiya, haka ya dawo gida ya tattara komatsansa ya tafi, zuciyarsa cike da kewar 'yar amaryarsa.
Bayan sati hud'u da tafiyarsa Hafsat ta fara zazzab'in dare, sai kuma rashi d'and'anon baki, komai ta ci bata jin dad'insa, amma ko Gaggo bata sani ba, don tana da dauriya sosai, kuma zazza6in idan gari ya waye sai ta ji ta warke sai wani daren.
Ranar wata laraba, tun da ta tashi da asuba, ta ji zazza6in ba sauka ba, aikuwa ta na yin salla ta koma ta kwanta ko sharar da take yi wa Goggo bata sami damar yi ba.
Ganin hantsi ya daga sosai tana d'aki a kwance ba ta fito ba sai Goggo ta shiga don ta ji ko lafiya tun da bata saba da kwanciya da dai dai wannan lokacin ba, amma sai ta same ta a k'udundune,da sauri ta k'arasa ta ta6a jikinta, aikuwa da sauri ta d'auke hannunta saboda zafin da ta ji jikin Hafsat d'in ya d'ime da shi.
Nan da nan ta aika yara aka kira Baffan Hafsat d'in daga shagonsa, yana ganin yadda jikinta yake yace a shirya ta su tafi asibiti.
Kai tsaye asibitin Sumaila aka kai ta bayan bincike likita ya sanar da su cewa tana d'auke da shigar ciki na wata biyu da sati d'aya, ya basu magunguna sabida zazza6in da ya ke damunta, bayan sun saya su ka wuce gida.
Kafin wani d'an lokaci labarin cikin hafsat ya kai kunnen kowa da ke gidan, sai d'an k'us-k'us ake wai daga d'aura aure ko tarewa ba ai ba ta kai masa kanta, kai lallai yaran zamani basu da kunya.
Ita kam Hafsat ba ta san me suke ba, don ta kanta ta ke, don sosai cikin ke sa ta laulayi.
Lokacin da labarin cikin ya je kunnen Innar su Abubakar kuwa, ba k'aramin farin ciki ta yi ba, don tana ganin lokaci yayi da zata turawa Sani da matarsa bak'in ciki, kwatankwacin wanda ta ji lokacin da ya k'i auren 'yar uwar ta, da kuma lokacin auren Abubakar da Hafsat .
Goggo ce ta ci gaba da baiwa Hafsat duk wata kulawa da ya kamata, amma fa tana shan mita, a gun Goggo na k'in jin gargad'inta da ta yi, ai yanzu gashi nan ya tafi ya bar ta da ciki, shi yana can yana harkokinsa ita kuma tana ji a jijinta.
Watansa uku da tafiya ya zo zuciyarsa cike da d'okin ganin matarsa da kuma ahalinsa, kai tsaye d'akin mahaifiyarsa ya nufa, sun gaisa cike da kewar juna, nan ta dama masa fura kasancewar lokacin da ya zo abincin rana ya k'are.
Sai da ya sha ya k'oshi, yana shirin tashi ta dakatar da shi da cewa "tsaya akwai maganar da na ke son muyi da kai."
Bai kawo komai a zuciyarsa ba ya koma ya zauna.
Sai da nisa sannan ta fara magana "ko kana da labarin cewa Hafsi tana da ciki?"
Cikin mamaki mai gauraye da tsantsar farin ciki yace "ban sami labari ba Inna."
"To ni yanzu na sanar da kai, kuma mahaifinka da 'yan uwansa suna nan suna jiran dawowarka domin ayi tariyarta, ni kuma abinda ba zan yadda da shi bane shine had'a jini da Sani, don haka ina umartarka da cewa duk juyin da za'ayi karka yarda ka ce cijinka ne, sannan umarnina na k'arshe a gare ka ka yi amfani da wannan damar ka sawwak'e ma ta aurenka, kuma saki uku na ke son kayi mata.
Ummu Aisha
[7/1, 6:27 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE
Story and Writing by
Ummu Aisha
🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛
SADAUKARWA
Wannan shafin naki ne ke kad'ai Aishan Umma, Allah ya k'ara k'auna da zaman tare
9⃣
Nan take ya ji kamar ta watsa masa ruwan zafi a jikinsa, cikin firgici ya ce "A'a Inna kar ki ce haka, idan na aikata abinda kika umarce ni na zalinci Hafsat, kuma nasan Allah ba zai bar ni ba, na rok'e ki don girmab Allah kar k……"
Katse shi tayi da cewa "Me kake son nuna min?So kake kace farin cikin Hafsi ya fi nawa muhimmanci a gurinka?"
Sai ta fashe da kuka "Lallai Saratu tayi nasara a kaina, sai ta je ta biya malaminta, sun shanye ka kaima kamar yadda suka shanye k'anin ubanka, amma ka sani muddin baka aikata abinda na sakaka ba Nono na da ka sha nan yafe ba."
Cike da tashin hankali ya ke kallonta, amma sam babu alamun sassauci akan fuskarta, gabad'aya sai jikinsa yayi sanyi, ya ji nadamar zuwansa gida ta shige shi, tabbas da yasan abinda zai zo ya yarar kenan da gara yai zamansa a can.
Da kyar ya yunk'ura ya tashi ya nufi d'akinsa, duk da k'urar da d'akin yai bai damu ba yana zuwa ya kwanta akan katifarsa, zuciyarsa cike da k'unci da bak'in cikin maganganun mahaifiyarsa.
Zuciyarsa ta ci gaba da raya masa irin yadda mahaifiyarsa ta k'i jinin Baffa Sani, amma bai ta6a tunanin za ta saka shi aikata irin wannan zalincin ba, duba da tun farko ba wani abu shi Baffa Sanin ya yi mata ba, duk dai maganar akan ta so ya auri k'anwar ta ne, kuma Allah bai nufa ba.
Abu d'aya da ya yanke a matsayin masalaha a gare shi shine, da asuba idan yayi sallah zai kama gabansa ya koma inda ya fito.
Tun da ya shiga d'akinsa bai fito ba sai da aka kira sallar magariba, sannan ya fito yayi alwala ya wuce masallaci.
Bai dawo gidan ba sai da akai sallar isha'i, har lokacin zuciyarsa a k'untace take, yana shirin shiga d'akinsa ya ji Baffa shehu yana masa magana daga bayansa.
Juyowa yayi suka gaisa, sai yake ce masa ya same shi a wajensa akwai maganar da yake so suyi.
Nan take yaji gabansa ya yanke ya fad'i, don yasan maganar ba zata wuce akan cikin Hafsat ba.
Jiki a sanyaye ya amsa masa da cewa yana zuwa.
Lokacin da ya je don amsa kiran Baffan nasa a kishingid'e ya same shi a farfajiyar wajen yana sauraron labarai a Radio.
Sai da ya gama jin labaran sannan ya kashe Radion, ya juyo yana fuskantar Abubakar ya fara magana "Wato Baffa k'arami ba komai bane ya sa na buk'aci ganinka sai akan magarku da Hafsi, shin ko kana da masaniyar cewa ka tafi ka bar ta d'auke da ciki?"
Ya yi shiru ya sauraron amsar da zai bashi.
Duk da dukan gudumar da zuciyarsa ta ke yi hakan bai hana shi nuna mamakinsa ba.
Baffa bai kula da halin da ya ke ciki ba yaci gaba da magana "Sakamakon haka mun yanke shawarar duk lokacin da ka dawo za ta tare a d'akinta."
Duk da halin zullumin da yake ciki hakan bai hana shi furta cewa "A gaskiya Baffa nayi mamakin wannan maganar cikin, kuma ni ban san daga ina ta samo shi ba, don Allah Baffa ku tuhume ta ko za ta fad'a muku inda ta samo shi, kuma ni gaskiya bazan iya zama da ita ba, don haka ta je na sake ta saki uku.

🔟
Baffa Shehu ya girgiza sosai da jin furucin Abubakar musamma irin hukuncin da ya yanke, ya zuba masa ido yana kallonsa ya rasa me zai ce, sannan kuma zuciyarsa bata amince da abinda Abubakar d'in ya ce ba saboda sanin halin Hafsat da ya yi, don ita ko yawo ma bai dame ta ba, idan ba aikenta akai ba zai yi wahala ka ganta a waje, bai ta6a ganin ta da wani saurayi a tsaye ba, bare ace wani ne ya yaudare ta ya yi mata ciki.
Duk da ba a da tabbas akan d'an yau, to amma irin tarbiyyar da suka bawa 'ya'yansu zai yi wahala a sami 6ullowar irin wannan al'amarin a cikin gidansu.
To amma ba shi da ta cewa, tun da shi dai bai san gaibu ba, kuma dole al'amarin yana buk'atar bincike.
Da haka ya sallami Abubakar ya tafi ya barshi zuciya cike da tunani.
。 。 。
Koda ya je d'akinsa zama yayi akan katifa, komai ya dagule masa, ya rasa me ke masa dad'i a rayuwarsa ta duniya, ga kuma tunanin halin da ya jefa Hafsat da tarin soyayyarta dake cikin zuciyarsa, shi kan sa yasan ya tafka babbar asarar da ba zai ta6a mayarwa ba, to amma ya ya iya da Innarsa?
Ranar nan kwana Abubakar yayi bai runtsa ba yana karanta wasik'ar jaki😃 (Ni kuwa na ce wa ya ja maka?)🤷🏻♀