← Book details Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 16

Sashe 12

Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da ta 'karasa shiryawa sai motar haya ta je ta shiga.

Tun daga wannan ranar bai sake tafiya da ita ba, sai dai ta shiga motar haya.

Gaba d'aya damuwa ta yi mata yawa, don ta kaisu matsyin da Aliyu nuna mata yake kamar akan dole yake zaune da ita.

Har ta manta rabon Aliyu da cin abinci a gidan, idan tayi magana Kuma ya fita fad'a, don haka sai ta zuba masa ido, sai dai bayan kowace Sallah sai ta ro'ki Ubangiji da ya kawo mata d'auki akan halin da take ciki.

Ranar wata lahadi da ta zamo ba'kar rana a ciki tarihin rayuwarta, da misalin biyar da rabi na yamma hafsat na zaune a parlour hannunta ri'ke, da littafin hisnul Muslim tana dubawa ta ji tsaiwar motarsa a harabar gidan, bayan kamar minti hud'u suka shigo, kai tsaye kujera Fareeda ta nufa ta zauna ta d'ora 'kafa d'aya kan d'aya, tana wani yatsina, i kyakkawa a gidan biki.

Duk da ran hafsat ya 6aci amma ko d'ago kai ta kallesu bata yi ba, shi kuwa Aliyu dama fridge ya zarce, ya d'auko mata ruwa lemo ya ajje a gaban ta, fuskarsa d'auke da murmushi yace "bismillah."

"Haba dear ni da nake jin yunwa me ruwa da lemo zai min, kawai kasa a kawo min abinci."

Kallon Hafsat da ke zaune yayi yace "je ki kawo abinci."

Cikin takaici take dubansa, da kyar ta iya daurewa ta ce "ban dafa ba."

"Ko mene ne dalili?"

"Haka kawai" ta bashi amsa cikin halin ko in kula.

'Kwafa kawai yayi, sannan ya kalli Fareeda yace "bari nayi miki takeaway."

"No dear ni gaskiyar bana son takeaway ko noodles ne dai ta dafa min."

Wani kallon mamaki Hafsat tayi mata, sannan tace amma dai akwai ta6i a 'kwa'kwalwar ki ko?

Ina shawartar ki da ki yi saurin dawowa cikin hankalinki, don banyi kama da House maid d'in gidanku ba bare ki sani aiki."

Tana gama fad'a ta mi'ke ta d'auki littafinta ta shigewarta d'aki.

Ummu Aisha
[7/1, 6:41 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

3⃣1⃣

Daga shi har Fareeda da kallo suka bita, har ta shige cikin d'akin ta turo 'kofar.

Fareeda ta juyo tana dubansa cikin yanayin kallon kissa ta 6ata fuska tace "yanzu kana ji matarka tace min ina hauka amma ka kasa d'aukar mataki a kai?

To gaskiya idan bazaka d'auki mataki ba ni zan d'auka, ko kuma a ha'kura da maganar auren nan, Allah ya had'awa kowa da rabonsa, tunda matarka tafi 'karfinka.

"Wa yace miki hafsat tafi 'karfina, ko kuma bazan iya d'aukar mataki akan ta ba? Meyasa daga wannan 'yar maganar sai maganar fasa aure? Ki zaba I kiga abinda zanyi idan ban d'auki mataki ba sai ki fad'i duk abinda kika so."

Yana gama fad'ar haka ya shiga d'akin da hafsat ta shiga, a tsaye ya same ta jingine da bango fuskarta sha6e-sha6e da hawaye.

Wani mugun kallo yake bin ta da shi, cikin alamun 6acin rai yace "me kike nufi da kalamanki? Mene ne dalilin tahowa da kika yi, alhalin ban gama maganar da nake miki ba? Kina nufin ban isa da ke ba kenan ko me? Ko kuwa tsabar rainin wayo ne yasa muna magana da ke kika wani taho kika bar wurin, to bazan d'auki rainin wayo ba, gara ma ki sake tunani, idan Kuma wasu ke zuga ki to tun dare bai miki ba ki tantance abinda ya dace da wanda bai dace ba."

Cikin 'kunar zuciya tace "zan iya jure duk wani abu da zakai min Aliyu, amma banda akan mace, wallahi babu macen da ta isa ta maida ni kamar baiwa, ko abinda kake min a gidan nan da kaga ina kau da kai ina dalili.

Shi aure ibada ne, kuma ta ita Kuma ibada dole sai mutum ya had'a da ha'kuri.

Duk abinda zakayi ban isa na hana ka ba, kaje kayi, amma girki kam wallahi bazan mata girki ba."

"Ni kuma nace sai kinyi idan ba haka ba kuma wallahi sai na d'auki mummunan mataki akanki."

"Duk matakin da zaka d'auka na shirya masa, amma girki kam ba zan yi ba."

"Tun da ban isa dake ba kije na sakeki, saki d'aya."

Maganar tayi matu'kar girgiza ta, wani hawaye ya sake 6alle mata, Cikin rawar murya tace " Aliyu wannan shine son da ka sha cewa kana yi min? Ashe zaka iya rabuwa dani akan wata mace? Sai yau na fahimci dalilin da idan maza suka fara neman aure wasu matan hankalinsu ke tashi, shikenan Aliyu a yau zan bar maka gidanka, amma ina so kasani idan na bar gidannan na bar shi kenan har abada."

Cikin rashin damuwa yace "da kin kyautawa kanki."

Wanna furuci nasa ba 'karamin ta6a mata zuciya yayi ba, hawaye na 'kara zubowa daga idanunta, zuciyarta na sa'ka mata tambayoyi daban-daban.

Wannan wace irin 'kaddara ce? Ita kuma tata kalar 'kaddarar kenan?

Yaushe ne zata yizaman aure kamar kowace mace?

In

Ummu Aisha
[7/1, 6:42 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

ZAMAN AMANA WRITER'S Ina mi'ka sa'kon gaisuwa a gare ki gabad'ayan

Oganniya (Aisha Umma)
Raheenat M. Abubakar
Bilkisu Z. Ya'u 🅱K
Aisha Isah (Mummy's Friend)
Maman Surayya
Maryama (Ummi Siddiqui)
Princess Rahima
👸Queen BK👸
Sajnah
Mommy'n Areef
Ummu Junnut Jasmeer

3⃣2⃣

Tana hawaye tana komai ta da'uko akwati, sai da ta cika ta da kayan sawarta da duk abinda tasan zata bu'kata, ta rufe, ta d'auki jakarta da mayafi ta fito zuwa d'akin nanny ta kar6i Muhammad ta goya shi, ta fice.

Tun da tabar gidan kuka take har ta isa Zari'a.

Ba 'karamin girgiza su Aunty maganar mutuwar auren hafsat tayi ba, nan take Uncle ya d'auki waya ya kira Aliyu don jin gaskiyar abinda ya faru a tsakaninsu, amma sai ya nuna bashi da lokacin sauraronsa.

Bayan kwana biyu aka je aka kwaso duk wani abu da yake mallakin Hafsat ne, haka ta ci gaba da idda ga kuma karatunta.

Ranar da labarin yaje kunnen Hajiyansu Aliyu, bata ji dad'i ba, aikuwa washegari ta nufi Zari'a don basu ha'kuri.

Lokacin da Aliyu ya same ta agida kuwa ba 'karamin fad'a tayi masa ba, kuma ta umarce shi indai yana son zaman lafiya da ita to ya dawo da matarsa, amma ga mamakinta sai ya nuna bashi da ra'ayin hakan.

Kuma da ta tambaye shi dalilin rabuwar su ya kasa bata 'kwa'k'kwaran dalili.

Tun daga nan tasan dole akwai abinda yake faruwa don banza bata kai zomo kasuwa.

Ko Afnan bata ji dad'in abinda yayan nata yayi ba, don tasan ya tafka babbar asarar mace ta gari irin Hafsat.

* * * *

Hafsat tayi 'ko'kori sosai wajen ganin ta cire damuwar Aliyu daga zuciyarta, musamman ganin yadda Aunty ta damu, kullum burinta shine ta kwantar mata da hankali.

Taci gaba da rainon yaronta, gefe d'aya kuma ta maida hankali sosai akan karatun ta.

Bayan kammala iddarta zawarawa da yawa sun fito da nufin aurenta, sai dai bata da lokacin sauraronsu.

Wani weekend da taje Rumoh, anan suka had'u da Abubakar, har ya sami labarin mutuwar aurenta.

Tun daga lokacin ya fara bibiyarta, wai yana so su maida aurensu.

Ita kuwa hafsat nuna masa tayi bata da lokacin sauraronsa ma.

A wannan tsakanin ya sami mahaifinta da maganar, shi kuma ya sami Goggo, aikuwa ta rufe ido taci mutuncinsa sosai.

Tun da Hafsat ta sami labari ta yiwa kanta fad'a, gara ta tsaida mutum d'aya daga cikin masu sonta ta aura, don yasan da gaske babu abinda zaisa ta sake aurensa.

Ummu Aisha
[7/1, 6:43 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

3️⃣3️⃣

A cikin masu son aurenta akwai wani Alhaji Nasir, shi d'an kano ne d'an asalin Yakasai, amma yana zaune a 'Kofar Nasarawa, yana da mata d'aya da yara hud'u.

Sun had'u da Hafsat ne lokacin da suka zo sunan Aunty Maryam 'kanwar Aunty Salma lokacin da ta haihu.

Tun lokacin da ya ganta ya fara bibiyarta, tun bata sauraronsa har ta fara sauraronsa sama-sama.

Tabbas yanayinsa ya nuna shi d'in mutumin kirki ne.

'Dan kasuwa ne sosai, Kuma Yana Cikin rufin asiri daidai gwargwado.

Duk cikin masu son aurenta shine mutumin da hankalinta yafi kwanciya da shi, cikin 'kan'kanin lokaci ta sanar da Aunty cewa ta tsaida mijin aure.

Bincike sosai Uncle Tahir yayi akansa, kuma Alhamdulillah ba'a sami wata matsala daga gareshi ba.

Cikin lokaci 'kalilan aka gama daidaita magana, aka tsaida ranar da za'a d'aura aure da tariya gabad'aya.

Kuma babban abin farin ciki shine ya amince bayan bikin zata dawo Zari'a, saboda karatunta, inyaso duk weekend sai ta dinga zuwa Kano har zuwa lokacin da zata kammala karatun ta.

An yi biki cikin kwanciyar hankali, wannan Karion a Kano aka d'aura auren, Amarya ta tare a gidanta cike da fatan wannan Karon mutuwa ce zata rabata da mijinta.

Sam Abubakar bashi da labarin auren Hafsat, sai bayan an d'aura auren ne Rabi'u 'kaninsa da aka zo da shi, ya tafi wurin yayan nasa don su gaisa.

Iya tashin hankali a ranar Abubakar ya shige shi lokacin da ya sami labarin aure Hafsat, sosai Rabi'u ya dinga bashi ha'kuri yana kwantar masa da hankali. A ranar kwana yayi da zazza6i, zuciyarsa kuwa in banda tafarfasa babu abinda take.

"Yanzu shikenan na rasa Hafsat?" Wannan ita ce tambayar da yayi ta nanatawa kansa.

Abu d'aya da ya tabbatarwa kansa shine bashi da sa'a, a rayuwa, domin rashin Hafsat ba 'karamar asara ba ce gare shi.

Ummu Aisha
[7/1, 6:43 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

3️⃣4️⃣

Tun bayan bikin sati d'aya kawai tayi a Kano, ta shirya ta koma Zari'a, ba gidan Uncle take da zama ba, musamman Alhaji Nasir ya samar mata gida take zaune a ciki.
Chapter 12 · 0% Book details