← Book details Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 16

Sashe 11

Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin murmushin 'karfin hali yace "gani kuwa kina gani na Fareeda, yaushe kika dawo 'kasar ne?"

'Yau sati na d'aya kenan da dawowa, mun same ku lafiya?"

"Lafiya 'kalau" ya bata amsa, ya karatun? Ya sake tambayarta.

"Alhamdulillah" ta bashi amsa a ta'kai ce, tana mi'kewa tsaye.

"Allah ya taimaka."
"Ameen."

Ta amsa tana tafiya, tana cewa "bari na watsa ruwa na fito." Ta shige wani d'an corridor, ko kallon inda Hafsat take batayi ba, bare tasa ran zatayi mata magana, har ta kai su ga gaisawa.

Ummu Aisha
[7/1, 6:38 AM] Wasila Z . A . W: 💃🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

Shafin yau kyauta ne a gareku, kuyi yadda kuke so da shi

Maman Noor
Maman Sapi da Amal
Naga comments d'inku, kuma nagode Allah ya bar 'kauna.

2⃣7⃣

Ranar suna yaro yaci sunan Muhammad. Ba 'karamin shagali akai na sunan ba, anci an sha, masu guzuri sun yi, DUK KANWAR JA CE Fans ma sun halarci taron sunan, don can na hango
su o'o ana tsice naman kan abinci, uhm bari dai nayi shiru 🤭 ba sai na ja suna ba 😜.

Mutanen Rumoh ma da yawa sun halarci taron sunan, don mota guda suka ciko.

Taron suna ya watse kowa ya koma gidansa lafiya,sai fatan Allah ya raya Muhammad.

Sun ci gaba da kula da jaririnsu cikin gata da kulawa, yaron sai 'kara girma yake kamar kazar agric.

A wannan tsakanin ne aka yankewa Ismail hukuncin kisa, bayan tsahon lokaci da aka d'auka ana shari'arsa, bayan kotu ta tabbatar da cewa yana da ruwa da tsaki akan kashe marigayiya Hafsat kamar yadda yayi i'kirari, da bakinsa.

Bayan kammaluwar shari'ar ne da kwana biyu Aliyu yasa hafsat ta shirya, don su je har gida su gaisa da mahaifiyar Hafsat d'in.

Kar6a sosai ta girmamawa akai musu, matar mai kirki kamar ta goya Hafsat, lokacin da ta d'auki Muhammad kuwa sai da ta zubar da hawaye, zuciyar ta na raya mata cewa da yanzu yaron nan d'an Hafsat d'inta ne.

Aliyu ya dinga bata ha'kuri, don yasan ta tuna da 'yarta ne wadda da yanzu ita ce zata kasance mahaifiyar yaron.

Suna nan zaune suka ji tsaiwar mota a harabar gidan, ba'a d'auki dogon lokaci ba, suka jiyo 'karar takun takalmi 'kwas-'kwas, alamun cewa za'a shigo.

Wata kyakkawar budurwa ce ta shigo, jikinta sanye da riga da skirt 'yan kanti, kayan sun bayyana duk wata sura ta jikinta, sai wani 'karamin mayafi da tayi rolling dashi, hannunta ri'ke da jaka kalar takalmim 'kafarta.

Kallon mamaki ta ke yiwa Aliyu, sai kuma ta saki wani lallausan marmushi, daidai lokacin da take 'ko'karin zama a kujerar da ke kusa da wadda yake zaune akai.

"Dama ana ganinka Yaya Aliyu?" Ta jefo masa tambayar ba tare da ta gaida shi ba.

Cikin murmushin 'karfin hali yace "gani kuwa kina gani na Fareeda, yaushe kika dawo 'kasar ne?"

'Yau sati na d'aya kenan da dawowa, mun same ku lafiya?"

"Lafiya 'kalau" ya bata amsa, ya karatun? Ya sake tambayarta.

"Alhamdulillah" ta bashi amsa a ta'kai ce, tana mi'kewa tsaye.

"Allah ya taimaka."
"Ameen."

Ta amsa tana tafiya, tana cewa "bari na watsa ruwa na fito." Ta shige wani d'an corridor, ko kallon inda Hafsat take batayi ba, bare tasa ran zatayi mata magana, har ta kai su ga gaisawa.

Ummu Aisha
[7/1, 6:38 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

2⃣8⃣

Bata da dad'e da shigewa ciki ba Aliyu yace su tashi su tafi.

Shatara ta arzi'ki Mommy'n ta had'awa hafsat, don taji dad'in ziyarar da suka kawo mata sosai.

Tun da suka shiga mota babu wanda yayi magana, har suka bar unguwar, zuciyar Hafsat cike tunanin budurwar da ta gani a gidan, wadda taji Aliyu ya kirata da suna fareeda.

Haka kawai taji har zuciyar sam bata kwanta mata ba.

Bayan sun koma gida yake mata bayani akan Fareedar, cewa ita d'in 'kanwar Hafsat ce, a Egypt tayo karatun ta, yarinyar nada rawar kai ba kamar 'yar'uwarta ba."

Murmushi kawai Hafsat tayi ba tare da tace komai ba.

* * * *

Yau kwana uku kenen da zuwan su gidan su marigayiya Hafsat da misalin Tara da rabi na dare suna zaune hankalin Hafsat na kan Muhammad da yake shan nono, shi kuma Aliyu yana kallon Network news a NTA, wayarsa ce ta fara ringing, ya d'auka ya duba, ganin ba'kuwar number yasa bai d'aga ba har ta katse.

Ganin an sake kiransa ne yasa shi d'agawa duk da bai san waye mai kiran ba, da sallama ya fara, kamar yadda yake al'adarsa idan an kira shi, ko ya kira. Muryar mace yaji tana cewa "ya Aliyu ya kake?"

Bai amsa tambayar da akai masa ba sai ya 'kara yin sallama, ganin cewa ba zai saurare ta ba sai ta amsa sallamar, sannan yake tambayar da wa yake magana.

Kai tsaye ta sanar masa wace ce, yayi mamakin inda ta sami number sa, kamar tasan tunanin da yake sai take sanar da shi a wayar mummy ta sami number sa ta d'auka.

Tun daga ranar kusan kullum sai ta kira shi, duk da ba wani sakewa yake da ita ba, Amma Yana d'agawa ko don darajar mahaifiyarta.

Tun Hafsat bata damuwa da yawan wayar da suke har abin ya soma damunta, don Fareeda bata da takamaimai lokacin kira kowane lokaci ma kiransa take.

Lokacin da ta sanar da Aliyu burinta na aurensa abin ya bashi mamaki, Amma sai ya bata ha'kuri yace shi bashi da burin 'kara aure iya matarsa ta isheshi rayuwa.

Hankalinta ya tashi sosai don tana ganin babu wani d'a namiji da ya dace da ita kamar Aliyun.

Ummu Aisha
[7/1, 6:40 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

2⃣9⃣

Tsab ta shirya, ta fito, kai tsaye gidan 'kanwar mahaifinta Aunty Maimuna ta nufa, don tasan ita kad'aice zata iya taimaka mata har ta kai ga samun abinda ranta yake so.

Don kuwa tana ganin ko za'a hau sama a rikito ba zata iya ha'kura da Aliyu ba, kamar yadda ba zata iya sharing d'insa da kowace mace ba.

Bayan sun gaisa batai 'kasa a gwiwa ba ta sanar da ita damuwarta, kan irin son da takewa Aliyu da yadda yadda yadda ke nuna mata halin ko in kula.

Murmushi ta saki tana cewa "ki kwantar da hankalinki, tun da kika zo gurina, ni kuma zan yi duk mai yiwuwa don ganin na share hawayenki.

Me akai akayi wani Aliyu? Daga shi har matar tasa a tafin hannu na suke, kuma sai sun game kuren su. Yanzu idan da kud'i ki kawo abinda yake hannunki, ni kuma nayi miki al'kawari nan da kwana uku da kanki zaki kira ni ki bani kabari."

Jiki na rawa ta zazzage kaf kud'in dake jakarta ta bata, har cikin zuciyarta tayi amanna da abinda tace, don tun da suka taso suke ji da ganin shi'umancin Aunty'n tasu.

* * * *

Washegari da wuri Aunty Maimuna ta shirya ta fita gidajen malamanta, don nemowa y'ar yayan nata sa'a, sai dai babbar matsalar da ta fuskanta ita ce, sai da ta je wurin mutum uku, amma kowa ce mata yake aure a tsakanin Aliyu da Fareeda ba zai yiwu ba.

Ba haka taso ba, amma duk da haka tace tana so ita Fareedar ta mallake shi ta yadda ko uwar da ta haife shi baza ta fita juya shi ba.

Kud'i sosai ta bayar don bata so a Sami matsala a aikin.

Da ta koma gida Bata sanar da Fareeda gaskiyar batu ba sai ta nuna mata cewa an gama aiki, ta saurari sakamako.

* * * *

Matsala ta farko da Hafsat ta fara fuskanta da Aliyu itace, wayar dare, saiya d'auki dogon lokaci yana waya, kuma tabbas tasan da mace ne, da tayi magana sai yace ta fiye zafin kishi tana nufin don kar ranta ya 6aci bazai yi waya da kowace mace ba, haka zaiyi ta fad'a, don haka ta daina tankawa, ta zuba masa ido.

Ummu Aisha
[7/1, 6:41 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

Dominku
Badi'a Ahmad
Maryam wada
Maman Sapi da Amal

3⃣0⃣

Wani sabon salo kuma da ya tsira shine, kullum idan ya dawo daga wurin aiki, yaci abinci, ko hutawa bai zaiyi ba zai d'auki wanka ya fice, ba shi zai dawo gida ba sai kwanciyar bacci.

Wanna abu ba 'karamin ciwa Hafsat tuwo a 'kwarya yake ba.

Ranar wata laraba tun dare Muhammad yake ta faman koke-koke, sakamakon zazza6in da ya tashi da shi. Bayan ya gama shiryawa zasu fita, don tare suke fita idan sun je Zari'a sai ya sauke ta a asibiti, don tuni sun fito asibiti, sai a bar Muhammad tare da nanny'n shi a gidan. fita Hafsat ta nemi da suyi da shi da nanny sai su tsaya a asibiti likita ya duba yaron, in ya so sai nanny ta dawo da shi gida.

Fur ya 'ki amincewa, sai ma yace zata 'ka'kalowa yaro ciwon 'karya don tana son ta walar da shi, to shi babu inda zai tsaya, idan zata tafi ta wuce su tafi idan kuma ba zata ba ta zauna shi yayi tafiyarsa.

Ganin ba zata iya wucewa tabar yaron a haka ba yasa ta ha'kura da fitar, tace ya je kawai zata zauna da yaron.

Magunguna ta rubuta ta bayar aka je aka sayo mata ta bashi, cikin ikon Allah kafin yamma jikin yaron yayi sau'ki sosai.

Bai dawo gidanba sai dare, da ta kawo masa abinci ko kallonsa bai yi ba yace ya 'koshi, ya bar mata kayanta, yayi wanka ya fice, bai sake dawowa ba sai kwanciyar bacci.

Washegari jikin Muhammad yayi sau'ki sosai, don haka ta shirya fita, abin mamaki kafin ta 'karasa shiryawa Aliyu yayi ficewarsa, ko karyawa bai tsaya yayi ba, bare ya jira ta.
Chapter 11 · 0% Book details