Sashe 15
Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Story and Writing by*
*Ummu Aisha*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛_
4️⃣0️⃣
Firgigit ta tashi zaune, kamar dama can bacci take, fuskarta a d'aure take tamau, ta 'ki kallon inda ya ke zaune, shi kuma gaba d'aya hankalinsa na kanta, so yake su had'a ido amma sam ta hana shi damar hakan.
Sun d'an dad'e a zaune ba tare da kowa yayi magana a tsakaninsu ba, shi fargabar yin maganar ma yake, saboda yadda ta d'aure fuska, ta 'ki ko da kallon wurin da yake zaune.
Kamar mai ciwon baki ya fara mata magana "Hafsat har yanzu ba zan gajiya wurin baki ha'kuri ba, domin duk Wanda ka ji ance ya yi ha'kuri to ha'ki'ka an cutar da shi, amma karki manta Ubangiji (S.W.T) yana son bayinsa masu ha'kuri.
Sannan shi ha'kuri halayya ce ta fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W).
Abinda ya faru kuskure ne da ajizanci irin na d'an Adam, amma na yi miki al'kawarin abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba. Ko a baya na tabbatar na fi ki shiga halin 'kunci da damuwa bisa abinda ya faru."
Har ya gama duk maganganun da zai yi ko d'ago kai ba tai ta kallashi ba, bare ta tanka masa, ya kai wajen minti talatin a zaune, ganin shirun ta yi yawa yasa ya mi'ke ya fita, bai dad'e ba ya dawo hannunsa d'auke da plate da cups.
Ledar da ya shigo da ita d'azu ya d'aukko, ya bud'e, wani lafiyayyen balangu ne a ciki, ya juye a cikin plate sai youghurt mai sanyi da ya juye a cikin kofunan, gaba d'aya ya tura gabanta sai kofin youghurt d'aya da ya d'auka ya fara kur6a.
Wani takaicinsa ne ya 'kara kamata, ko kallon plate da cup d'in bata yi ba ta juya tayi kwanciyarta.
Ba irin rarrashin da bai yi mata ba akan ta daure ta ci wani abu, kar ta kwanta da yunwa, amma ko kula shi ba ta yi ba bare ya sa ran zata ci.
Haka ya koma kitchen ya d'auko wani plate d'in ya rufe naman ya fitar parlour ya ajje a cikin fridge.
Sai da ya shiga toilet ya yi brush ya zo ya kwanta a kan gadon daga gefe d'aya.
Ai kuwa kamar wadda ya watsawa wuta ta tashi a fusace, tana yi masa wani irin kallo na 'kas-'kanci ta ce "me ka ke nufi da kwanciya a nan? Kai yanzu ko ni nace ka zo inda na ke ka kwanta ai ka ji kunya ka ce a'a, ko kuwa kana tunanin ban san ciwon Kai na ba?
Tun dare bai maka ba ka kama gaban ka, in kuma kai ba za ka fita ba to ni zan fice in bar maka d'akin.
Ganin yadda ta birkice masa lokaci d'aya, ya sa ya yi mata sai da safe ya fice, ya nufi part d'in sa.
* * * *
Washegari tun asuba ta tashi, bayan ta yi salla bata koma ta kwanta ba, tana gama addu'o'i da Azkhar, gyara gidan ta fara duk da bai yi datti ba, bayan ta gama ta koma d'akin tayi wanka ta shirya, sannan ta fito parlour ta kunna karatu wayar ta ta na sauraro.
Sai wajen 'karfe takwas ta shiga kitchen, ta saka ruwa a kettle, lokaci kad'an ya yi zafi ta juye ya had'a tea ta fito, ta zauna a parlour ta na sha.
Ba ta dad'e da zama ba ya shigo, bakin shi d'auke da sallama, kallo d'aya ta yi masa ta d'auke kai, kamar bata san Allah ya yi ruwan tsirar sa ba.
_Ummu Aisha_
[7/1, 6:46 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*DUK KANWAR JA CE*
*Story and Writing by*
*Ummu Aisha*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S Z.A.W* _(Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)_🤜🤛
4️⃣1️⃣
Duk da cewa bai ji dad'in halin ko in kula d'in da ta nuna masa ba, hakan bai sa ya nuna 6acin rai ba, domin yasan duk abinda Hafsat za tai masa ya can-canci fiye da haka daga gareta.
A kujerar da ke kusa da ita ya zauna, gaba d'aya hankalinsa ya na kanta, cikin taushin murya ya ce "Hafsat an tashi lafiya?"
Maimakon ta amsa, kawai sai ta mi'ke ta nufi kitchen da cup d'in da ta gama shan tea.
Sai da ta d'auraye kofin ta fito, ta yi wucewar ta d'aki tai kwanciyarta.
* * * *
Sati uku kenan da komawar Hafsat gidan Abubakar, amma babu wani abu da ya sauya daga zaman nasu, ya yi iya bakin 'ko'karinsa don ganin sun daidaita amma abin ya fi 'karfinsa, dole ya zuba mata ido.
Damuwa tayi masa yawa, don duk cikin matan nasa babu mai kwantar mai da hankali, har gara ma Hafsat ita magana ce ba tai masa, amma Zainab rashin mutunci kala-kala babu abinda ta manta.
Daga 'karshe dai ganin ya rasa mafita sai ya shirya tafiya Rumoh wurin Goggo , don yasan ita kad'ai ce zata iya taimaka masa a wannan ga6ar.
Ranar lahadi tun safe ya shirya ya tafi, kafin 'karfe tara ya je.
Bayan ya gaisa da 'yan'uwansa ya nufi d'akin mahaifiyar sa, sun dad'e da ita, tana ta 'korafi wai ya nuna mata ba ta isa da shi ba, tun da ya mai da aurensa da Hafsat, da ta isa da shi ai da bai mai da Hafsat ba.
Shi kuma sai ha'kuri ya ke bata, har ya samu zuciyarta ta yi sanyi.
Bai sami shiga wurin Goggo ba sai bayan Azahar, sosai tayi murnar ganin jikan nata, bayan sun gaisa ta ke tambayarsa iyalansa da fatan dai suna zaman lafiya?
Ganin an zo ga6ar da ya ke so baiyi 'kwauron baki ba, ya fayyace wa Goggo irin halin da suke ciki da Hafsat, daga 'karshe ya nemi taimakon ta akan ta yiwa Hafsat magana ko zata sassauta masa su daidaita.
Aikuwa nan Goggo ta hau fad'a, Kamar ta ari baki, sai bata ha'kuri ya ke, ya na nuna mata shifa so ya ke ta yi mata nasiha, har ta sakko.
A lokacin Goggo ta shirya tafiya Kano, don ta ce baza ta iya barin Hafsin ta na aikata rashin hankali ba.
Ana fitowa daga masallacin sallar la'asar suka d'auki hanya ita da shi a cikin motarsa.
_Ummu Aisha_
[7/1, 6:47 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*DUK KANWAR JA CE*
*Story and Writing by*
*Ummu Aisha*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS Z.A.W* _(Gidan Zaman lafiya da Amana insha Allah)_🤜🤛
*Sadaukarwa ga*
_Maman Abba_
_Maman Noor_
*Nagode da irin 'kwarin gwiwar da kuke bani Allah ya bar 'kauna, in yinku irin sosai d'innan 🤸🏻♀️*
4️⃣2️⃣
Ba 'karamin farin ciki Hafsat ta yi da ganin Goggo ba, ta rasa inda za ta sata saboda farin cikin ganin ta.
Sai shige da fice ta ke tsakanin parlour da kitchen, bayan kayan motsa bakin da ta ajje mata, girki ta d'ora na musamman duk da Goggon ta sanar mata cewa a 'koshe ta ke.
Duk yadda Goggon ta kai da kakkaucewa sai da ta ci ta sha ta 'koshi, sannan ta fuskanci Hafsat da maganar da ke tafe da ita.
"Hafsi wace magana na ke ji daga wajen d'an uwanki? Haba Hafsi, idan ki kai haka sai naga kamar baki godewa ni'imar da ubangiji ya yi miki ba.
Idan kin nutsu kin fahimci abinda ya faru a baya ba yin kan sa bane, duk abinda ya aikata ya yi ne busa umarnin mahaifiyarsa, wadda ita kuma ba komai ne ya sa tayi hakan ba sai tsaba hassada da 'kyashi.
Kar ki manta cewa mai sunan Malam d'an uwanki ne, kuma da gan-gan ba zai yi abinda yasan zai cutar da ke ba, ko a lokacin da abin ya faru, daga yanayin tashin hankalin da ya shiga zai tabbatar miki da irin nadamar da yayi.
Nafi kowa farin cikin daidaitawarku da shi, domin nasan duk wanda zaki aura a fad'in duniya ba zai san darajar ki da 'kimarki kamar shi ba, kar ki bari a sami 6araka daga 6angarenki Hafsi don ba zan ji dad'in hakan ba ko kad'an.
Kar ki manta abinda ya faru shine ya zama tsani na duk wani matsayi da ki ka taka.
Duk wani abu da ki ka ga faru a ruyuwar bawa, dama yana rubuce a cikin littan 'kaddarar sa.
Idan ma wanna matakin da ki ka d'auka horo ne, to ki janye shi haka, zuwa yanzu ya Yi horuwar da ko wa'ka za'a saka masa a ma'kogaro ba zai you abu makamancin wanna ba. Lokaci ya yi da zaki yi rayuwar aure kamar kowace mace. Ki yi ha'kuri da duk wani abu da ya faru a baya, ki zauna da mijinki da zuciya d'aya, don ya zame miki tafarkin shiga aljanna."
Duk maganganun da Goggo take Hafsat na zaune tana sauraronta, ba ta ce komai ba, har ta kai 'karshe.
Ta d'auki lokaci mai tsayi tana bata misalai har zuwa lokacin da Hafsat d'i n ta tabbatar mata da cewa komai ya wuce.
Daga nan suka ci gaba da hirar da ta shafi dangi, har lokacin sallar magariba ya yi.
Sai bayansa an yi sallar Isha sannan Abubakar ya shigo, ko zama bai yi ba Goggo ta ce ya zo ya kaita gidan 'yar uwarta.
Hafsat ta dage sai Goggo ta kwana a gidan, ai kuwa tace ba za'ai wanna abin kunyar da itaba, dole ba don sun so ba ya kai ta.
Zuciyarsa fal da zumud'i ya dawo gidan, don da ya sauke Goggo ko cooking gidan bai shiga ba, babban burinsa ya ganshi da Hafsat cikin farin ciki.
_Ummu Aisha_
[7/1, 6:48 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*DUK KANWAR JA CE*
*Story and Writing by*
*Ummu Aisha*
*ZAMAN AMANA WRITER'S Z.A.W* _(Gidan Zaman lafiya da Amana insha Allah)_🤜🤛
4️⃣3️⃣
Bai 'karaso gida ba, sai da ya tsaya wani wajen masu gashin kaji mai rai da lafiya yai yi musu tsaraba.
Sai da ya fara zuwa wurin Zainab, duk da har lokacin ko maganar arzi'ki bata had'a su, don ita tana ganin babban cin mutuncin da zai mata a rayuwarta shine ya had'a ta zama da wata.
Abin kunya ne a gare ta a gan ta da kishiya, bayan du irin soyayyar da ta ke masa.