← Book details Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 16

Sashe 7

Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turus ya ja ya tsaya, ya kasa gaba ya kasa baya, kallon Saleem da ke shan furar sa yake hankali kwance, bai san ma ana kallonsa ba.

Goggo da ke zaune cikin d'aki ta yi masa magana, sannan ya sami damar k'arasawa ciki.

Kallo d'aya tayi masa ta san cewa har lokacin ransa a 6ace yake.

Yana zaune ya kasa cewa komai har zuwa lokacin da Hafsat ta idar da Sallah ta yi addu'a, ta d'ago tana k'ok'arin gaida shi ya katse ta cewa "Sawunki a likkaga ki tashi ki koma inda kika fito, don bama buk'atarki a cikin gidan nan, yadda kika saka k'afa kika tafi a baya to muma a yanzu bamu da buk'atar……"

"Ba sai kayi haka ba zan san cewa kai ka haifi Hafsi, har yau ban manta ranar da uwarta ta haife ta ba a cikin gidan nan."

Cikin sanyin murya yace "me ya kawo wannan maganar kuma Goggo?"

"Babu Sani, ka yanke duk hukuncin da ka ga ya dace da y'arka babu mai hana ka."

Ganin ran Goggo ya fara 6aci yasa ya fita cikin takaicin yadda Goggon ta hanashi d'aukar mataki akan Hafsat d'in.

Washe gari Goggo ta tara duk y'ay'anta mata da maza, don har Goggo Binta ta zo don tun dare Goggo tasa akai mata waya, cewa ta zo tana son ganinta, bayan duk sun hallara, Goggo ta fara magana da cewa "Dukkaninku nan na tara ku ne anan akan maganar Hafsi, kowa yasan abinda ya faru da ita babu mai buk'atar k'arin bayani, sai dai babban abinda baku sani ba shine, barin Hafsi garin nan ya faru ne bisa umarni na.

Ni ce nan na 6oye ta saboda ku gane kuskurenku na yadda kuka tsangwami yarinyar nan , duk da baku da tabbacin abinda kuke zargi, tun da duk cikinku babu wanda ya tsaurara bincike akan gaskiyar al'amarin.

Kun riga kun san irin tarbiyyar da ta tashi da ita, zai yi wahala ta aikaya irin abinda ake zarginta da shi, amma sai kuka gogawa idanuwanku toka, duk kuka juya mata baya.

Ganin hakan ya tashi hankalinta har ra kai ga matsayin da ko barci bata samu, tsoron kar wani abu ya same ta sai na yanke shawarar raba ta da gidan baki d'aya……

Nan ta kwashe komai da ya faru ta sanar musu, kuma Alhamdulillah, duk sun gamsu da bayananta, sai ta kira Saleem ta nuna musu a matsayin yaron da Hafsi ta ta haifa bayan barin gida.

Kowa yayi farin cikin ganin yaron, kuma nan take babu tantama sun amince d'an Abubakar ne, amma sai Goggo tace bata amince kowa yayi masa maganar Hafsi ko Saleem ba, a rabu da shi akwai lokacin da zai kawo kansa da kansa.

Bayan sun gama da wannan maganar ne kuma ta sanar musu da zancen Aliyu da jiya da daddare Uncle ya sanar mata, lokacin da Hafsat ta had'asu a waya don yi masa godiya kan irin kulawar da suka bawa Hafsin ta,kuma kowa yayi farin ciki da wannan batu.

Bayan gama tattaunawar ne mazan kowa ya kama gabansa, itma Hafsat taci gaba da harkokinta a cikin gidan ba tare da fargabar komai ba.

Washegari tun da hantsi ta shirya ta tafi gidan Sadiya, don gaskiya ba k'arya tayi kewar ta sosai.

Ba k'aramar murna Sadiya tayi ba, ai kuwa yini sukayi suna hira, kamar ba gobe.

A cikin hirar ne ta ke bata labarin Yaya Abubakar, lokacin da ya dawo gida ya ji labarin 6atanta sai da yayi kamar zai ya hauka, kuka sosai ya ke da idanunsa kamar mace, wannan ne ya fara sakawa,mutane zargin anya abinda ya faru babu lauje a cikin nad'i?

Har wata rama ya yi, gaba d'aya an rasa kansa, a lokacin ne takardar shaidar d'aukarsa aiki ta fito daga bankin da ya yi service, saboda yabawa da suka yi da k'wazonsa, da rik'on amana.

Bayan fara aikinsa Innarsu ta dage sai ya yi aure, amma sai da ya shekara baiyi ba sai daga baya ya auri wata k'anwar abokinsa mai shegen girman kan tsiya, don da ta zo su Inna ana ta d'igimi suruka ta zo, amma ko ruwan gidannan k'in sha ta yi, sai wani yatsina take i kyakkyawa a gidan biki.

Ummu Aisha
[7/1, 6:30 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

1⃣6⃣

Murmushi kawai Hafsat ta yi don bata da abin cewa, a gidan ta yini har aka yi sallar magriba, sannan ta tafi gida.

Tun daga nesa ta hango mota tsaye a k'ofar gidansu, amma bata kawo komai ba, ta ci gaba da tafiyarta, ta shiga zaure ne sukai kici6us da Abubakar da ke k'ok'arin fitowa daga cikin gidan, wanda ya zo tun la'asar, sakamakon kiran da Rabi'u k'aninsa yai masa a waya ya sanar da shi zuwan hafsat d'in, shine fa ya taho gida afujajan.

Idanunsa na sauka a kanta ya tsaya cak, ya kasa gaba ya kasa, baya, tana ganin haka ta had'e girar sama da ta k'asa ta zagaye shi ta wuce, har ta shiga cikin gidan ta juya bata ga Saleem da Safiyya da ke biye da ita ba, sai ta juya.

Ta same su a zauren yana rik'e da hannun Saleem,ya tsugunna ya zubawa yaron idanu, ko magana ba tayi ba ta sa hannu ta janyo yaron suka wuce ciki, Safiyya na biye da su.

Gaba d'aya sai ya ji jikinsa ya yi sanyi, tabbas kallo d'aya da ya yiwa yaron ya ji ya shiga zuciyarsa, kuma tabbas zai kar6i abinsa, don bai ji a zuciyarsa cewa zai iya hak'ura da shi ba.

Ita kam Hafsat ya kar6i k'addararsa ta rabuwa da ita, tun da ya san babu yadda za'ayi ta koma hannunsa bayan, saki ukun da ya yi mata, amma ko ba komai Saleem zai d'ebe masa kewar mahaifiyarsa, to amma inda Gizo ya ke sak'a shine ta yaya zai iya tunkarar iyayensu da maganar cewa Saleem d'ansa ne alhali da bakinsa ya tabbatar mu su da cewa babu wani abu na auratayya da ya ta6a shiga tsakaninsa da Hafsat.

Tuna hakan da ya yi sai jikinsa yai sanyi, a haka ya fice daga zauren.

Da daddare da ya shiga cikin gidan ya so ya shiga 6angaren Goggo ko don ya k'ara ganin Hafsat da d'ansa amma sam Innarsu ta kasa ta tsare ta hanashi, don ba ta son dalilin da zai had'a su da Hafsi, tunda ta fahimci har yanzu zuciyarsa na matuk'ar begen ta.

Ita kuwa Hafsat suna shiga gida ta ci gaba da harkokinta, ta ma manta da batun wani Abubakar.

Kwananta hud'u a garin Iyayen Aliyu suka zo don neman aure, kuma cikin ikon Allah basu tafi ba sai da aka sanya ranar biki sati uku masu zuwa.

Satin ta biyu ta koma Zari'a d'auke da tsaraba sosai.

Ai kuwa tana zuwa Aunty ta sa aka fara yi mata gyaran jiki, gefe d'aya kuma ana ta sayayyar abinda ya dace.

A tsakanin ne kuma Baffa Halliru ya aiko da kud'i masu yawa a matsayin gudunmawarsu, amma Uncle yace ba zai kar6a ba, ai ko bai rik'e Hafsat ba shi mai yi mata kayan d'aki ne, shi kuma baffa Halliru ya dage, ai gudunmawa ce, da kyar ya kar6a.

Ummu Aisha
[7/1, 6:31 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

1⃣7⃣

Shirin biki ake sosai daga kowanne 6angare kamar bikin budurwa.

Tun ranar laraba su Hafsat suka dira a Rumoh, gabaki d'ayansu, iya Uncle kawsuka bari, a Zari'a, shi sai ranar Juma'a zai zo Kano, ranar Asabar kuma sai yaje d'aurin auren.

Komai da suka san zasu buk'ata game da sha'anin bikin Aunty ta taho da shi, hatta kayan abinci sun taho da shi.

Ganin irin shirin da ake ba k'aramin k'ona ran Inna Kulu yayi ba, zuciyarta kamar ta fashe don bak'in ciki, da ta san haka Hafsi zata sami d'aukaka da ba ta sa Baffa k'arami ya sake ta ba.

Ranar Alhamis akai walima, Juma'a akai yini, kuma Alhamdulillahi yanin ya tara jama'a sosai.

Da daddare bayan kowa ya watse sai iya bak'i masu kwana, Inna Kulu ta sami Baffa Halliru har d'akinsa a kan maganar Saleem.

Bayan ta sami guri ta zauna ne tace "Malam da magana na zo."

Ya d'aga kai yana kallonta sannan yace "ina sauraronki."

"Dama akan maganar yaron nan ne d'an wajen Hafsi, sai nake ganin me zai hana mu kar6e shi, tun da kaga aure za ta yi, kuma bai kamata ace ta tafi da shi gidan wani da sunan agolanci ba, tun da mahaifinsa ba gazawa zai yi da kula da shi ba."

Ba tare da dube ta ba yace "Au kin san mahainfin nasa kenan."

"Wannan wace irin magana ce?

Ai ko makaho ya shafa fuskar yaron nan ya san d'an gidan Baffa k'arami ne."

Cikin yanayin da ke nuna tsantsar takaici ya ce "Shi Baffa k'aramin ne ya turo ki gurina da wannan maganar?"

Tace "A'a nice dai naga dacewar hakan."

Girgiza kansa ya yi sannan yace "ki fita daga idona na rufe Kulu, idan haka ba kuma ranki zai 6aci, ji nake a gidan sai da kika hana Saratu fitowa waje?

Ke kenan kiran y'arta ta kwaso abin kunya za ta lik'awa d'anki, yaron da kike kira da shege marar asali ne yanzu kuma ya zama jikanki?"

"To banda abinka Malam mene ne na tayar da maganar da ta wuce?

Yaron nan dai mutum ko ba'a fad'a ba ya ganshi yasan na Baffa k'arami ne."

"Tashi ki fita daga d'akin nan Kulu tan raina bai gama 6aci da ke ba, idan ba haka ba kuwa ranki in yayi dubu sai ya 6aci."

Ummu Aisha
[7/1, 6:31 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

★Assalamu alaikum

Bayan dogon lokaci da aka dauka ba ba tare da kun Jini ba, sakamakon matsalar waya da na samu, Alhamdulillahi a yau Allah ya nufe ni da ci gaba da rubutawa.

Jinjina ga ZAMAN AMANA WRITER'S

1⃣8⃣
Chapter 7 · 0% Book details