← Book details Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 16

Sashe 10

Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummu Aisha
[7/1, 6:35 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

2⃣4⃣

Kwanankin Hafsat hu'du kenan a hannun 'yan sanda, a iya tsayin kwanakin nan babu irin 'ko'karin da Uncle bai yi ba don ganin an bashi belin hafsat, amma abin ya gagara.

Sanda su ka je asibiti da nufin duba Aliyu kuwa 'kiri-'kiri Hajiya ta hana su ganin sa.

Sai ma wani kallon tsana da ta ke musu, haka suka bar asibitin jiki a sanyaye.

Ranar da Aliyu ya dawo hayyacinsa, ba 'karamin dad'i Hajiya ta ji ba, sai tarairayar sa ta ke kamar 'kwai.

Cikin 'kan'kanin lokaci aka sanar da 'yan sanda, Kamar yadda su ka ba'kata, sun zo sun gudanar da binciken su ta hanyar yi masa tambayoyi, shi kuma ya na amsa musu.

A nan 'yan sandan suka gaskata bayanan da Hafsat ta bayar na cewa Isma'il ne da yaransa suka aikata wannan ta'addancin.

Tun lokacin da Aliyu ya farfad'o bai ga Hafsat a d'akin ba ya ke so ya tambaya, amma sai ya yi shiru.

Bayan tafiyar 'yan sandan ne ya yi 'karfin halin tambayar hajiya ita.

A take hajiya ta sauya fuska, ta ce "me zata yi maka? Yarinyar da ta ke neman rayuwar ka, ka dubi irin halin da ta jefa ka a ciki, ko kuwa neman ta ka ke ta zo ta 'karasa ka?"

Cikin mamaki Aliyu ya dubi Hajiyar ya ce "wane irin neman rayuwa ta Kuma? Don Allah Hajiya kar ki 'kara magana makamanciyar wannan, Hafsat fa mata ta ce, ta Yaya za'ai ta cutar da ni irin haka?"

"Mene ne nufin ka Aliyu, kana son nuna min cewa, duk wannan abinda Hafsat ta yi maka ba ka damu ba ko kuwa? To wallahi tun wuri ka fita daga zancen yarinyar nan tun kafin rai na ya 6aci."

"Kiyi ha'kuri Hajiya, amma wallahi babu ruwan Hafsat a cikin abinda ya same ni, nasan cewa za ki yi mamaki idan ki ka ji cewa Isma'il ne ya yi min wannan aika-aikar."

A tunanin sa Hafsat ta yi tafiya ba ta nan, don na gaya masa zancen tafiyar ta ta,har kud'i ya ba ta ya ce ta yi tsaraba, ashe duk yaudara ta ya ke, yana da abinda ya 'kulle a cikin zuciyar sa.

Babu abinda ya fi ban mamaki da shi sai da ya sanar da ni cewa shine mutumin da ya kashe marigayiya Hafsat".

Nan ya kwashe dukk abinda ya faru a ranar ya sanar da ita, Hajiya ta cika da mamakin abinda ya faru da kuma nadamar abinda ta yi wa Hafsat da iyayen ta.

Ita kuwa Hafsat a ranar 'yan sanda su ka sallame ta bayan sun tabbatar da cewa ba ta aikata laifin da ake tuhumar ta da shi ba.

Ummu Aisha
[7/1, 6:35 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

Sa'kon gaisuwa ta a gare ku 'yan 2006 na G.G.A.S.S SUMAI LA dun inda kuke🙋

2⃣5⃣

Daga police station kai tsaye Hafsat motor park ta nufa, ta hau motar zuwa Zaria, ko kud'in mota bata da shi, sai wata baiwar Allah da suka zauna tare ce ta biya mata.

Lokacin da ta isa gida, Aunty ke sanar mata sun yi sa6ani da Uncle, don shima ya tafi Kaduna zai gano ta, a take ta kira shi a waya ta sanar masa cewa ga Hafsat ta zo gida.

Washegari ita da Aunty suka je Kaduna suka d'ebo kayan sawar ta, da wasu abubuwa na amfanin ta, suka juya gida.

* * * *

Satin Aliyu uku a gadon asibiti aka sallame shi, gaba d'aya hankalinsa a tashe ya ke, sakamakon rashin zuwan Hafsat gare shi da duk wani Wanda ya shafe ta, don hakan yana bashi tabbacin cewa ba 'karamin 6ata musu rai abinda ya faru yayi ba.

Ranar da ya cika sati d'aya da sallamowa daga asibiti, ya shirya zuwa Zari'a, driver ne ya kai shi, don har lokacin jikinsa bai gama warwarewa ba, tafiyar ma don ya dage ne.

Ya sami Uncle yana shirin fita, amma ganin sa sai ya dakatar da fitar.

Bayan sun gaisa ya yi masa ya jiki ne kuma yai shiru yana sauraron abinda ke tafe da shi.

Kai tsaye Aliyu ya ce wa Uncle "dama maganar Hafsat ne Uncle, na ji wasu abubuwa marasa dad'i da suka faru a lokacin da bani da lafiya, kuma nima tabbas ban ji dad'in hakan ba, amma don Allah Ina son ayi ha'kuri, duk abinda ya faru dama Allah ya 'kaddara sai hakan ya faru".

Uncle ya dube shi ya ce " a zahirin gaskiya raina ya 6aci da irin abinda ya faru, yadda mahaifiyar ka ta rufe ido akan maganar nan ko ganin Hafsat ta yi da wu'ka tana sassara ka iyakacin abinda zatai kenan, ta tsaya ta saurare mu ayi magana ta fahimta ma abin ya gagara.

Da muka je duba ka kuwa 'kiri-'kiri ta rufe ido ko ganin ka ma hana mu ta yi, sai haka muka ha'kura muka taho.

Sannan da ace tayi tunani da Hafsat ce tayi yin'kurin kashe ka da ba zata kira a waya don a zo a kaika asibiti ba, bare har a ceto rayuwarka, a yanzu maganar da nake maka Hafsat ko makaranta zata je sai ta saka ni'kab, kuma kusan kullum idan ta je da damuwa take dawowa, akan abinda ya faru, don haka maganar gaskiya ka same ta ku daidaita idan ta amince zata koma gidan ka bani da matsala, iyakaci in bi ku da addu'ar fatan alkhairi, Amma ni dai kam bazan tilasta mata ba".

Shi me ku ke ganin ya kamata? Hafsat ta ci gaba da zama da Aliyu ne ko kuwa?

Ina jiran comments d'inku, kafin na ci gaba.

Ummu Aisha
[7/1, 6:36 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

HAPPY BIRTHDAY TO YOU🎂🎂🎂🎂🎂🎂
Hayat Baba Zubairu Admin of Admins, ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwarka Allah ya 'karo shekaru masu albarka 🎂🎂🎂🎂🎂🎂

🥦DUK KANWAR JA CE🥦 fans naji dad'i da ganin comments d'inku, kuma insha Allahu zan yi 'ko'karin ganin na ci gaba da wannan novel don yanzu ma aka fara😜.

2⃣6⃣

Lokacin da ya sami ganin hafsat, rufe ido tayi ta nuna sam ita bata da bu'katar cigaba da rayuwa da shi,saboda tozarcin da mahaifiyarsa ta yi mata, ankai ruwa rana sosai kafin ta amince ta koma gidansa.

Allah cikin ikonsa,bata dad'e da komawa ba sai ta fara rashin lafiya, ana zuwa asibiti bayan bincike, likita ya tabbatar musu da cewa tana da shigar ciki.

Wannan lokacin Hajiya kamar ta maida Hafsat ciki saboda tattali, kusan kullum tana hanyar gidan don duba ta.

Shi kuwa oga kwat-kwata wato Aliyu ba'a maganarsa, don numfashi ma idan da hali yi mata zai yi.

* * * *

Hafsat na cigaba da rainon cikinta, wanda zuwa yanzu yayi girmama sosai don kowane lokaci zata iya haihuwa.

Duk wani abu da maijego da jariri zasuyi amfanin da shi Aliyu ya tanade shi haihuwa kawai ake jira.

Ranar wata alhamis tun safe Hafsat ta fara jin alamomin ciwon naq'kuda amma ta daure bata gayawa Aliyu ba, sai wajen 'karfe uku na yamma ta ji abin ya zama serious, sai ta yiwa Hajiyansu Aliyu waya ta sanar da ita halin da take ciki, to kuma cikin hukuncin Ubangiji kafin Hajiyar ta 'karaso gidan anyi haihuwar, ta haifi yaron ta namiji 'katoto da shi, ganin ban sha'awa.

Fad'ar irin murnar da Aliyu da 'yan uwansa suka muna ma 6ata baki ne, Hafsat da jariri ta sun ga kulawa da tattali sosai.

Ummu Aisha
[7/1, 6:37 AM] Wasila Z . A . W: 💃🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

Shafin yau kyauta ne a gareku, kuyi yadda kuke so da shi

Maman Noor
Maman Sapi da Amal
Naga comments d'inku, kuma nagode Allah ya bar 'kauna.

2⃣7⃣

Ranar suna yaro yaci sunan Muhammad. Ba 'karamin shagali akai na sunan ba, anci an sha, masu guzuri sun yi, DUK KANWAR JA CE Fans ma sun halarci taron sunan, don can na hango
su o'o ana tsice naman kan abinci, uhm bari dai nayi shiru 🤭 ba sai na ja suna ba 😜.

Mutanen Rumoh ma da yawa sun halarci taron sunan, don mota guda suka ciko.

Taron suna ya watse kowa ya koma gidansa lafiya,sai fatan Allah ya raya Muhammad.

Sun ci gaba da kula da jaririnsu cikin gata da kulawa, yaron sai 'kara girma yake kamar kazar agric.

A wannan tsakanin ne aka yankewa Ismail hukuncin kisa, bayan tsahon lokaci da aka d'auka ana shari'arsa, bayan kotu ta tabbatar da cewa yana da ruwa da tsaki akan kashe marigayiya Hafsat kamar yadda yayi i'kirari, da bakinsa.

Bayan kammaluwar shari'ar ne da kwana biyu Aliyu yasa hafsat ta shirya, don su je har gida su gaisa da mahaifiyar Hafsat d'in.

Kar6a sosai ta girmamawa akai musu, matar mai kirki kamar ta goya Hafsat, lokacin da ta d'auki Muhammad kuwa sai da ta zubar da hawaye, zuciyar ta na raya mata cewa da yanzu yaron nan d'an Hafsat d'inta ne.

Aliyu ya dinga bata ha'kuri, don yasan ta tuna da 'yarta ne wadda da yanzu ita ce zata kasance mahaifiyar yaron.

Suna nan zaune suka ji tsaiwar mota a harabar gidan, ba'a d'auki dogon lokaci ba, suka jiyo 'karar takun takalmi 'kwas-'kwas, alamun cewa za'a shigo.

Wata kyakkawar budurwa ce ta shigo, jikinta sanye da riga da skirt 'yan kanti, kayan sun bayyana duk wata sura ta jikinta, sai wani 'karamin mayafi da tayi rolling dashi, hannunta ri'ke da jaka kalar takalmim 'kafarta.

Kallon mamaki ta ke yiwa Aliyu, sai kuma ta saki wani lallausan marmushi, daidai lokacin da take 'ko'karin zama a kujerar da ke kusa da wadda yake zaune akai.

"Dama ana ganinka Yaya Aliyu?" Ta jefo masa tambayar ba tare da ta gaida shi ba.
Chapter 10 · 0% Book details