← Book details Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 16

Sashe 6

Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da result d'insu ya fito ba k'aramin kyau yayi ba, kuma cikin sa'a JAMB d'in tama ta sami point fiye da yadda ake buk'ata, don haka nan da nan aka nema mata admission a A.B.U, kuma cikin hikimar Allah sun bata course d'in da take buri wato medicine.

Bayan anyi registration da duk abinda ya da ce ta fara zuwa d'aukar lacture.

Duk da bata da saurin sabo hakan bai hana ta yin k'awa ba, wata nai suna Afnan, itama sai da ta lura da nutsuwarta sannan suka k'ulla k'awance da ita.

Afnan y'ar Kaduna ce, su biyu iyayensu suka haifa daga ita sai Yayanta Aliyu, wanda shima lecturer ne anan ABU.

Ummu Aisha
[7/1, 6:29 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

1⃣3⃣

Ranar wata litinin da misalin k'arfe goma sha biyu, suka fito daga lecture, suna tafe Afnan ta dubi Hafsat ta ce tana son ta raka ta wurin Yayanta zata kar6i wasu kud'i a hannunsa.

Sai Hafsat d'in ta ce ta je ta dawo tana jiranta, amma fir Afnan ta k'i, sai ma cewa da ta yi "Hafsat ban san me yasa ba kullum na ce ki zo mu je gun Yaya Aliyu sai ki k'i, ko kara ba kya yi min, ko kuma kin ji labarin yana satar mutane ne, ban sani ba."

Hafsat ta kalleta ta ce "ba haka ba ne, kawai……"

"Kawai me za ki ce? Bayan gashi nan a fili kin nuna min cewa yadda na d'auke ki ke ba haka kika d'auke ni ba."

Ganin maganar tana neman yin tsawo yasa Hafsat ta amince ta bita.

Da sallama d'auke a bakinsu suka shiga Office d'in, Afnance a gaba Hafsat na biye da ita, wani daddad'an k'amshi ya ziyarci hancinsu.

Kai tsaye Afnan ta nufi gaban tebir d'in da ke gabansa, ita kuma Hafsat sai ta sami wuri ta tsaya.

Sai da Afnan ta gaida shi sannan Hafsat ma ta gaida shi, ya d'ago idanunsa yana kallon me d'auke da wannan zazzak'ar muryar.

Afnan ta kar6i abinda ya kaita, bata tsaya yin wata magana ba saboda a lokacin yana tsaka da yin aiki, suka fito daga office d'in.

Bayan kwana uku da zuwansu, ita har ta manta ma da batunsa, sai dai idan Afnan ce tayi maganarsa, kwatsam sai Afnan ta same ta da wani batu da ya zamo mata kamar famin abinda ya wuce.

Bayan sun gama lectures d'insu na ranar, suna tafe suna hira, har suka zo inda zasu rabu, don ita Afnan a hostel ta ke, banbanci da Hafsat da ke Staff Quaters.

Afnan ce ta sami jikin wata bishiya ta jingina tana kallon Hafsat, sannan tace "Sak'o aka bani wurinki, duk da ban san yadda zaki d'auki al'amarin ba, amma zan so ki fahimci abinda na zo miki da shi.

Tun ranar monday da muka je office d'in Yaya Aliyu da ke ya ganki, bayan na koma hostel ya kira ni, ya yi min bayanin cewa yana sonki, kuma da aure, ya ce in sanar da ke.

Abinda yasa banyi saurin fad'a miki ba tun ranar ina tsoron yadda zaki d'auki maganar, domin a k'ananan shekaru irin namu, bai kamata ace mun sanya maganar soyayya a gaba ba, musamman idan akai duba da irin course d'in da muke karanta, wanda yake buk'atar nutsuwa, to amma ya shaida min ba wai yana nufin sai anyi auren yanzu ba, zai bari ki k'ara girma nan da kamar shekara biyu haka."

Hafsat na sauraronta har ta gama bayaninta, sannan ta yi murmushi t ce "Kafin nace komai tambaya zan fara miki, shin Yaya Aliyu yana da mata ko ba shi da ita?"

"A'a bai ta6a aure ba" cewar Afnan.

"To idan haka ne ya kamata ke kanki kisan wani abu da baki sani ba akaina, kin ganni nan to na ta6a aure, kuma har ina daro guda d'aya, mun sami matsala ne da maigida na wanda har ta kaimu da rabuwa."

Ummu Aisha
[7/1, 6:29 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

ASSALAMU ALAIKUM

Nasan cewa kun jini shiru, wallahi matsalar waya ta ne sam yanzu ba ta rik'e charge, amma insha Allahu a haka zan lalla6a kafin Allah ya bani ikon sake wata.

1⃣4⃣

Duk da afnan tayi mamakin maganarta, amma sai ta 6oye bata nuna ba, sai ma cewa da "tayi to meye a ciki?

Don kin ta6a aure wannan ba zai zama matsala ba, kuma nasan tun da Yaya Aliyu ya furta yana son ki, to da gaske ya ke yi don, don mun dad'e muna jiran wannan ranar, tun lokacin da wadda zai aura ta rasu ana saura sati d'aya bikinsu bai sake kallon wata mace da sunan soyayya ba, duk da damuwa da Hajiyarmu tayi da maganar aurensa, don Allah Hafsat kar ki bazantar da da soyayyar Yaya Aliyu."

"Baki fahimce ni ba Afnan, da bakinki kin ce min Yaya Aliyu saurayi ne da ko auren fari bai yi ba, kin ga bai kamata ace ya aure ni ba ina matsayin bazawara har da d'a, gaskiya ina ganin idan na aure shi ban yi masa adalci ba."

"Kada ki ce haka Hafsat, shi fa aure nufin Ubangiji ne, kar ki manta Manzon Allah (S.A.W) da bazawara ya fara, idan har hakan ta faru ai koyi kuka yi da sunna." Ta k'arasa maganar tana duban Hafsat.

"Ban tari numfashin ki ba, amma karki manta ba ke zaki zauna da ni ba shine, idan kuma har bashi da ra'ayin auren bazawara fa?"

"Hhhh, nasan waye Yaya Aliyu Hafsat, tunda ya ce yana sonki, ba yaro d'aya ba ko 'ya'ya goma ne da ke bazai fasa aurenki ba, domin duk abinda yace ya na so, to tabbas da gaske ya ke, sai dai idan ke ce bakya ra'ayinsa to wannan kam dole na hak'ura don ba zan miki dole ba."

Cikin murmushi Hafsat tace "zan amince da maganarki amma bisa sharad'i d'aya."

Wane irin sharad'i ne wannan?"

Ina son ki sanar da Yaya Aliyu da Hajiya abin da na sanar da ke game da rayuwa ta, idan har sun amince to ba ni da matsala nima na amince, amma don Allah idan har kin san akwai matsala kar ki rufe min."

"Wannan abu ne mai sauk'i, kuma insha Allahu babu wani dalili da zai hana aurenki da Yaya Aliyu sai ikon Allah, ki bani nan da gobe ko mai ake ciki za ki ji ."

Nan suka ya sallama kowacce ta kama gabanta.

。 。 。

Washegari suna zuwa ko lacture basu shiga ba, Afnan ke sanar mata cewa sun yi magana da Hajiyarsu kuma ta amince babu matsala, shima Yaya Aliyun ya amince.

Cikin sati biyu wata irin shak'uwa ta shiga tsakanin Hafsat da Aliyu, wata irin soyayya yake nuna mata, wadda ke sata mamaki sosai don ita a ganinta bata kai matsayin da mutum kamar Aliyu zai so haka ba.

A haka ya fara maganar ya kamata iyaye su shiga cikin maganar don da wuri ya ke son ayi auren in ya so ta ci gaba da karatun ta a d'akinta.

Kai tsaye ta sanar da Auntynta, itama ba ta yi k'asa a gwiwa ba ta sanar da Uncle Taheer, shi kuma ya ce yana son ya d'an yi hak'uri don dole sai iyayenta sun san da maganar.

Washegari ya sanar da Hajiyarsa, ita kuma tace lokaci yayi da ya kamata Hafsat ta koma gida don iyayenta su san inda ta ke, in yaso sai ayi maganar auren.

Dole Aliyu ya yi hak'uri har zuwa k'arshen semister.

Sun gama jarrabawa lafiya, sai shirye-shiryen tafiya ta ke, kuma Unxle yace dole ta je da Saleem domin kowa ya ganshi, don kallo d'aya zakai masa in dai kana da hankali zaka san cewa Abubakar ne mahaifinsa, don babu ta inda yaron ya barshi.

Kamar yadda suka tsara ranar Asabar da misalin k'arfe takwas na safe Hafsat ta fito cikin shirin tafiya, shima Saleem an shirya shi sai Safiyya y'ar Aunty Salma, itama da ita za'ayi tafiyar.

Driver ne ya tuk'o su, sai da suka tsaya Kano suka bawa Hajiya sak'o, sai da akai Sallar azahar sannan suja nufi Sumaila.

Tunda suka shiga Sumaila Hafsat take masa kwatance har suka shiga Rumo, sannu-sannu har suka isa k'ofar gidansu, anan driver ya sami wuri ya yi parking.

Cikin nutsuwa dukkansu suka fito, hannunta d'auke da jakarta, Safiyya na rik'e da hannun Saleem suka shiga gidan.

Kusan duka matan gidan suna zaune a gidin babbar bishiyar Dirimin da ke gidan saboda zafin da ake yi a lokacin, kowacce tana sabgar gabanta.

Sallamar ta ce ta jawo hankulansu gare su, gaba d'aya sai aka kama kallon-kallo, kowacce zuciyarta cike da manakin Ganin Hafsin da har anyi nenanta an gaji.

Fuskarta d'auke da murmushi ta k'arasa, tana gaida su, sannan ta wuce zuwa 6angaren Goggo su Saleem na biye da ita.

A lokacin in da za'a tona zuciyar Inna Mero abin Kare ba ya ci ba, don wani bak'in ciki taji ya kama ta ganin yanayin cigaban da ta samu.

Cikin farin ciki Goggo ta tare su bakinta ya k'i rufuwa, idonta akan Saleem, kallo d'aya ta yiwa yaron wani farin ciki ya kama ta, don tasan yanzu ne kowa zai fahmci cewa Abubakar ya yiwa Hafsi abinda yayi ne don ya ci zarafinta.

Cikin d'an k'ank'anin lokaci labarin zuwan Hafsi ya cika gari, yara sai zuwa kallonta suke.

Tuni labari ya kai kunnen mahaifinta, ya kuwa nufo gida a fusace, yana shigowa tun kafin ya k'arasa kewayen Goggo ya fara kwala mata kira, yana shiga idonsa ya sauka akan Saleem, da ke zaune shi da Safiyya suna shan furar da Goggo ta dama musu, ita kuma Hafsat tana cikin d'aki tana Sallar la'asar.

Ummu Aisha
[7/1, 6:30 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

1⃣5⃣
Chapter 6 · 0% Book details