← Book details Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 16

Sashe 5

Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana zaune bai ankara ba yaji masallatai sun fara kiran Salla, nan ya mik'e ya je yai alwala ya tafi masallaci, bayan yayi Raka'atainil fajr, sai ya zauna yayi ta karatun alk'ur ani, har zuwa lokacin assalatu, sai da akai sallar asuba ya fito ya nufi gida da nufin shirin komawa garin da ya fito.

Yana shiga shirin wanka yayi, a band'akinsa da ke daf d'akinsa, bayan ya fito ya shirya tsaf, ya nufi cikin gida don yin sallama da mahaifansa.

'Dakin Innarsu ya fara shiga, ko gaisawa bata bari sun yi ba fara tambayarsa akan batun Hafsi, sai ya kwashe komai da ya faru tsakaninsa da Baffa Shehu ya fad'a mata, ai kuwa ranta ya yi fari tas, ko babu komai ya cika burin ta, sun ci gaba da tattaunawa akan abinda ya shafe su sak'on kira daga iyayensu ya iso gare shi, don haka ya fito don amsa kiransu, amma cikin zuciyarsa ji ya ke kamar ya zura da gudu.

Da sallama ya shiga, d'akin Gogga Habi, inda duka iyayensu maza suke zaman jiransa, ganin kowa a zaune, ya nemi guri nesa kad'an da iyayen ya zauna, yana satar kallon Hafsat da ke zaune can gefe d'aya ta sunkuyar da kanta.

Baffa shehu ne ya fara magana "Kamar yadda kuka sani mun taru anan ne akan maganar Baffa 'Karami da Hafsi gaskiyar magana jiya mun zauna da shi mun yi magana, amma amsar da ya bani ce tayi matuk'ar girgizani, shi yasa nake ganin gara ya fad'i abinda ya ce min a gaban kowa don wak'a a bakin mai ita ta fi dad'i."

Abubakar da jikinsa ya k'ara sanyi ya kasa magana, sai da Baffansa ya ce "kai muke sauraro."

Abin mamaki babu kunya Abubakar ya ce "Jiya Baffa Shehu ya ce da ni wai Hafsat tana da ciki, to gaskiyar magana ba nawa ba ne don ni tun da nake da ita, babu abin da ya ta6a had'ani da ita, sakamakon haka na ce ni bazan iya zama da ita ba, don haka na sake ta saki uku, sai ta nemi uban cikin ta."

Hafsat najin haka ta yanke jiki ta fad'i a gurin da sauri Gogga ta yi kanta, tana dubawa ta ga ai sumewa tayi.

Ummu Aisha
[7/1, 6:28 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

1⃣1⃣

Ganin yadda Goggo ta gigice ya sa duk iyayen sukayo kanta, amma banda Bffa Sani da ya daskare a zaune,sabofa al'ajabin abinda Abubakar ya ce.

A gigice Abubakar ya nufi inda take, sai dai bai kai ga k'arasawa ba Baffa Halliru ya doka masa wata tsawa da ta rud'ar da shi, ya ce "kar ka kuskura ka k'araso inda yarinyar nan take, idan kuma ba haka ba wallahi zaka ga 6acin rai."

Jin haka yasa ya dakata jikinsa sai rawa ya ke, ya kasa aikata komai, yana kallo iyayen nasu suka kinkime ta aka fita da ita waje don kai ta asibiti.

Asibitin da ke cikin garin aka nufa da ita, ganin halin da take ciki yasa mai'aikacin da ke bakin aiki a lokacin ya bar abinda take ya zo gurinta don bata taimakon gaggawa.

Cikin ikon Allah numfashinta ya dawo, nan akai mata allurar Barci dan ana son k'wak'walwarta ta sami hutu.

Ganin babu wata matsala duk kowa ya tafi sai iya Goggo aka bari a wurin, don ance idan allurar barcin ta sake ta zasu koma gida.

Kimanin awanni biyu ta d'auka tana barci kafin ta farka.

Abubuwan da suka faru ne suka dawo cikin k'wak'walwarta, wani irin tashin hankali ya ziyarce ta, a ranar nan Hafsat ta gane cewa kuka ma rahama ne, domin ko d'igon hawaye ta kasa zubarwa, sai wani irin suya da take ji zuciyarta na yi mata, ga wani abu da ya tokare mata k'irji.

Goggo da ke zaune kusa da ita ce ta fahimci halin da ta ke ciki, sai ta dinga rarrashinta da kwantar mata da hankali, har zuwa lokacin da hawaye ya dinga zubowa daga idanunta.

Har aka sallame su suka tafi guda kuka take, ta rasa dalilin da yasa Abubakar ya yi mata haka, wannan wace irin tazartawa ce? kamar ba jininsa ba, idan har son aurenta bayayi ba sai ya sanar da iyayensu gaskiyaba, amma don zalinci sai ya za6i ta 6ata mata suna.

Har dare ta kasa cin komai, in banda kuka babu abinda ta ke, da kyar Goggo ta matsa mata ta sha koko, shima ba mai yawa ba don gaba d'aya ta yi loosen apetite d'inta.

Cikin d'an k'ank'anin lokaci labarin cikin da abinda Abubakar ya ce ya bazu a gidsn da ma cikin garin gaba d'aya, kowa da abinda zai ce, wasu ma laifin mahaifinta suke gani, don da bai dage sai tayi karatun boko ba, da bata je ta kwaso musu abin kunya ba.

Inna kulu kuwa ta sami abin yi kullum cikin yar da magana ta ke a tsakar gida, don sai da ta hana Saratu mahaifiyar Hafsi walwala a gidan.

Iya tashin hankali Hafsat tana ganinsa, don a wannan lokacin mahaifin ta ko gaida shi tayi baya amsawa, kuma k'arin takaicinsa yadda Goggo ta kasa ta tsare ta hana kowa ya yiwa Hafsi magana, domin ta ce ita dai tasan wace ce Hafsin ta, ba zata aikata wannan kaifin ba, shiri ne kawai don a tozarta ta.

Gaba d'aya Hafsat ta rame ta fita daga kamanninta, duk gidan babu mai tausayinta sai Goggo.

Ganin yadda rayuwarta ta fara lalacewa yasa Goggo ta fara tunanin mafita.

。 。 。

Ranar laraba da hantsi ta shirya zuwa Sumaila, Kai tsaye gidan Binta, y'ar ta ce da ke aure a Sumaila.

Bayan sun gaisa tai mata vayanin abinda ke tafe da ita akan maganar Hafsi, da irin taimakon da ta ke so tai mata, Goggo Binta ba jayayya ta amince da abinda mahaifiyarta ta saka ta, don itama zuciyarta ta bata akwai lauje cikin nad'i akan wannan naganar amma lokaci ne zai nuna.

Bayan sun gama shirya abinda zasu yi Goggo Habi ta koma gida.

Sai da daddare tayiwa Hafsat bayanin komai, kuma ta k'ara kwantar mata hankali, sosai.

Ummu Aisha
[7/1, 6:28 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE

Story and Writing by
Ummu Aisha

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

1⃣2⃣

Bayan kwana biyu Goggo Habi ta shirya zuwa Gani duba wani k'aninta da bashi da lafiya, tun asuba suka tafi ita da Baffa Sani da zai kai ta akan Babur.

Suna barin gidan itama ta fito d'auke da jakar kayanta da ta had'a tun dare ta fita daga gidan, cikin sa'a kuma babu wanda ya ga fitar ta.

Bata yi nisa da gida ba ta sami mota, irin direbobin nan masu sammako, ta hau, a tashar kuka ta sauka, ta nufi gidan Goggonta.

Lokacin da ta je itama Goggo Binta ta gama shiryawa, ko zama bata yi ba suka fice, suka koma tasha, suka hau motar da zata kai su Kano.

'Karfe takwas na safe a cikin Kano tayi musu, sun je gidan Goggo A'i, wadda ta kasance yaya ga Goggo Habi, cikinsu d'aya, ita a Kano take aure, yanzu ma ba mijin tuni ya rasu, sai y'ay'a, duk sun zama wasu abu, masu aikin gomnati na yi, masu kasuwannci na yi.

An kar6e su sosai cikin mutunci, don dama ita mace ce mai son zumunci, bayan sun karya aka sake gaisawa sannan ta yi mata bayanin duk abinda ya faru da Hafsi d'in tun daga batun aurensu da Abubakar, cikin jikinta har zuwa sakin da ya yi mata, da yanda kowa ya tsangwame ta, da kuma hukuncin da Goggo ta yanke na barinta garin ba tare da sanin kowa ba, har zuwa lokacin da gaskiya za ta yi halinta.

Ita kanta Goggo A'i ta yarda da hukuncin da y'ar uwarta ta yanke, don a take ta kira d'anta 'Dahiru da ke aiki a Zari'a,Lacturer ne a A.B.U, bayan sun gaisa tayi masa bayanin abinda ya faru, kuma ta sanar da shi cewa tana so ta sa a rako Hafsat gidansa.

Babu jayayya ya yi na'am da umarnin mahaifiyarsa.

A ranar kuwa aka sa driver ya kai ta, ita ma Goggo Binta a ranar ta juya gida.

Kar6a sosai matarsa tai mata, aka d'auki kayanta aka shigar wani d'aki,ta umarce ta da taje daga ciki ta yi wanka sai ta fito ta ci abinci ta huta.

。 。 。

Cikin kwanaki kad'an sabo ya shiga tsakaninsu, don Aunty Salma akwai kirki da sanin darajar d'an Adam.

Satinta biyu a gidan aka samar mata malamin da zai d'inga yi mata lesson, kuma ta mai da hankali sosai.

A can Rumo kuwa lokacin da Goggo ta dawo daga Gani ba ta ga Hafsat ba, sai da ta d'agawa kowa na gidan hankali, akai ta nemanta Hankali tashe, amma shiru babu labarinta, ita kuwa Goggo ta yi bulunbuk'wai, kai ka ce bata san ina ta ke ba.🤣

Hafsat ta ci gaba da rainon cikinta gefe d'aya kuma ga karatun ta da ta riga ta fitar da rai da shi.

Kafin lokacin haihuwar ta ya yi Uncle Tahir da Aunty Salma sun tanadi komai, sai jiran lokaci.

Ranar wata Talata da yamma Hafsat ta haifi yaronta Namiji, bayan yini da tayi tana faman Nak'uda, don tun asuba take fama.

Bayan sati d'aya yaro ya ci suna Muhammad Saleem, anyi shagali Sosai, duk da babu wanda ya sani a cikin dangin su, sai dai abokan arzik'in Aunty sunyi musu kara sosai.

Ta ci gaba da rainon d'anta k'ark'ashin kulawar Aunty, har yaron yayi wayo.

Watan Saleem biyar Hafsat ta shiga makaranta,wata privet ce a nan kusa da su, SS 3 aka sata bayan interview da akai mata, kuma Alhamdulillahi ta ci.

A shekarar ta zana S.S.C.E, da JAMB.

Har wannan lokacin babu wanda yasan ina take, don ko Kano suka je to a Gadon 'Kaya ake sauke ta gidansu Aunty Salma.
Chapter 5 · 0% Book details