Sashe 8
Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jiki a sanyaye ta fice daga dakin zuciyarta cike da bakin cikin rashin nasarar da bata samu ba.
Washegari Asabar aka daura auren Hafsat da Aliyu, Wanda d'umbin jama'a Suka shaida.
Bayan watsewar 'yan daurin aure masu zuwa rakiyar Amarya suka shirya suka dauki hanya.
Sun isa garin Kaduna lafiya, Kai tsaye gidan iyayen Aliyu aka wuce da su, Kuma Alhamdulillahi sun Sami taro na mutunci, sai da kowacce ta ci ta k'oshi, su Kai sallah, Suka huta, sannan aka ce su fito a Kai su gidan amarya su gani.
Duk wanda ya ga gidan nan sai ya yaba don ba k'aramin tsaruwa ya yi ba, da gani ba kananan kudi aka kashewa gidan ba, Uncle Tahir da Aunty Salma ba karamin kokari su Kai ba.
Masu kaunar Hafsat na ta taya ta murna, masu hassada kuwa zuciyar nan bakikkirin, bayan sun gama gani aka kwashe su zuwa masaukin su.
'Karfe takwas saura aka fara kwasar mutane zuwa wurin dinner da aka shirya a kayataccen hotel, Amarya da Ango sunyi shiga ta alfarma, kowa ya gansu sai sun birge shi.
Anci ansha masu guzuri sun yi, zan so kuga mutanen Rumoh a wurin nan sun zuba kauyanci son ransu.
Daga wurin dinner kai tsaye aka zarce da amarya gidanta mutanen Rumoh kuma aka mai da su masaukin.
Washegari da misalin goma na safe duk 'yan rakiya sun gama shiryawa, bayan kowacce ta karya akace su fito za'a kai su gidan amarya suyi sallama daga Nan a mai da su gida.
Kwanakin ta biyar a gidan ya ce ta shirya zai Kai ta ta gaida Hajiyarsa.
Ta shirya cikin shiga ta Kamala suka tafi.
Ranar Hafsat taga tarairaya kamar Hajiya zata mai da ita cikin don so.
Komai ta dauko ta ce na Hafsat ne Afnan sai tsokanar Hafsat ta ke, wai ta kar6e mata fada, it's Kuma Hafsat ta kasa sakewa.
Sai dare suka koma gida zuciyar Hafsat cike da farin cikin irin tar6ar da ta samu daga surukarta.
Ummu Aisha
[7/1, 6:32 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE
Story and Writing by
Ummu Aisha
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛
1⃣9⃣
Zama suke na soyayya da girmama juna, cikin sati biyu sun yi wata irin sha'kuwa, kowanne a cikinsu bai son abinda zai sa ya yi nesa da d'an uwansa.
Bayan bikinsu da sati biyu ya koma baking aikinsa, ita kuma ta koma makaranta, Kuma Alhamdulillahi yana ba ta gudunmawa sosai akan karatun ta.
Cikin wani weekend suka shirya tafiya Rumoh don ya je ya gaida iyayenta, tare da Afnan aka shirya tafiyar.
Da wuri suka d'auki hanya, Aliyu ne ke jan motar Hafsat na zaune a gefensa, sai Afnan da ke zaune ita d'aya a baya.
Misalin sha biyu saura kwata su ka shiga garin Rumoh, Hafsat na ta nuna masa hanya har suka isa 'kofar gidan, ya sami wuri ya yi parking.
Lokaci d'aya su ka fito daga cikin motar, Hafsat da Afnan suka shiga gidan bakinsu d'auke da sallama.
Duk wanda ke gidan ya yi murna da ganin Hafsat, don duk wanda ya kalle ta ya san ta sami kwanciyar hankali da ci gaba a rayuwarta.
Goggo don murna kamar ta goya Hafsin ta, ranar Uncle Taheer da Aunty Salma sun sha albarka, don sune tsani ga duk wani ci gaba da Hafsat ta samu a rayuwarta.
Inna Kulu kamar ta fashe don ba'kin cikin, don duk 'ya'yan ta mata babu wadda ta kama 'kafar Hafsat.
Har cikin gida Goggo ta sa aka shiga da shi, bayan ya ci abinci ya kora da fura nono ya 'koshi, sannan ya bi ya gaida duk matan gidan cikin girmamawa, kuma kowanne waje ya shiga sai ya bi su da alkhairi, kowa sai sam barka yake.
'Karfe uku na yamma suka fito da shirin tafiya, Hafsat kamar kar ta bi su, amma ba yadda za ta yi dole ta bi su ko don karatun.
Sai dare suka koma gida duk sun gaji kamar anyi musu duka .
Kwanansu biyu da dawo wa daga Rumoh wani abokin Aliyu mai suna Isma'il ya kawo musu ziyara, don lokacin da akai bikin baya 'kasar ya yi tafiya.
Sun gaisa da Hafsat cikin mutunci da garmamawa, lokacin da ya so tafiya ya yi mata kyauta ta girma, Hafsat sai mamaki ta ke, amma sai Aliyu ya nuna mata wannan ba komai bane daga halin Isma'il d'in.
Ummu Aisha
[7/1, 6:33 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦

🤦♀🙆ILLAR RI'KO*
('yar RI'KO)
Na Aisha Isah (Mummy's Friend)
Congratulations, ina taya ki murnar kammala novel d'inki Mai ilmantarwa, Allah ya sa mu amfana da darrusan da suke cikin sa, kura-kuran da su ke ciki Kuma Allah ya yafe. Sai mun ji ki a sabon novel.
2⃣0⃣
A kwana a tashi babu wuya, yau gashi har an yi wata hud'u da auren Hafsat, kuma Alhamdulillah, Suna zaune lafiya, babu wata matsala a tsakaninsu.
★ ★ ★ ★
Shi kuwa Abubakar tun bayan da ya saki Hafsat ya koma sai ya rasa kwanciyar hankali, damuwa ta yi masa yawa, kullum Yana cikin tunani da ba'kin cikin rabuwa da abu mafi soyuwa a gare shi.
Haka ya ci gaba da rayuwa cikin 'kunci da damuwa har zuwa lokacin da su ka kammala service d'insu.
Ba 'karamin tashin hankali ya shiga ba lokacin da ya dawo gida ya sami labarin 6acewar Hafsat.
Sai da kowa na gidan ya fahimci akwai abinda ya ke damunsa, ya rame sosai, yayi ba'ki.
Da haka ya had'a takardunsa ya fara fafutukar neman aiki, cikin hukuncin ubangiji ya sami aiki a Zenith bank.
Cikin watanni uku da samun aikinsa hankalinsa ya fara kwanciya, duk da cewa har lokacin akwai damuwar 6atan Hafsat a 'kasan ransa, musamman idan ya tuna cewa shine sanadi.
Cikin wanna lokacin ne kuma, iyayensu suka fara matsa masa da maganar aure.
Da farko hankalinsa ya tashi da maganar, amma lokacin da ya sami wani abokinsa mai suna Ahmad da maganar nan take ya share masa hawayensa ta hanyar bashi 'kanwarsa mai suna Zainab. Duk da zuciyarsa bata yi na'am da ita ba haka ya amince, Don ba zai iya watsawa Ahmad 'kasa a ido ba.
Ahmad abokinsa ne da sukai karatu tare a BUK, akwai sha'kuwa sosai a tsakaninsu. Tun farkon samun aikin Abubakar ya je har gida don gaida mahaifiyar Ahmad, don tuni dama ta san shi, tun suna makaranta wani lokacin suna zuwa gidan, to fa anan Zainab ta gan shi ta haukace akan son sa, shi kuma Ahmad yace bazai fad'a masa ba, don shi ba yaron aiken ta ba ne.
Har lokacin ba ta daina damun sa da maganar ba, sai kuma katsam Abubakar d'in ya same shi da maganar an matsa masa da maganar aure a gida, shi kuma har yanzu bai sami yarinyar da ya ke so ba, to fa shine ya gwada sa'arsa don ganin ko zai iya samawa 'kanwarsa farin cikinta.
Cikin sa'a sai Allah ya sa ya amince, cikin lokaci kad'an Suka daidaita kansu har iyaye suka shiga maganar.
Cikin watanni shida da akai komai aka gama, ta tare a gidansa da ke Zoo road.
Lokacin da ake zancen bikin Inna Kulu sai rawar Kai ake, ita dole d'anta zai auri macen da ta dace da shi, kuma 'yar birni.
Biki akai sosai, amma tun kafin 'yan biki su dawo gida aka fara samun matsala, don Zainab irin mutanen nan ce da basa son 'yan 'kauye.
Don da suka je yi musu sallama sama-sama ta kar6e su babu wata fara'a a fuskar ta, haka suka gaji da zaman kurame, su kai mata sallama suka tafi.

SADAUKARWA GA
RAHEENAT M. ABUBAKAR
(My Heenat)
2⃣1⃣
Lokacin da suka koma gida, kowa sai fad'ar albarkacin bakinsa yake game da amaryar ta Abubakar, da irin kar6ar da ta yi musu
Suna zaune babu wata matsala a tsakaninsu in ban da ta 'kin danginsa da suka kasance 'yan 'kauye, sai dai abin da bai sani ba tana family planning a 6oye saboda tana ganin cewa idan ta haihu a wannan lokacin za ta iya samun matsala da karatun ta, wanda ita kuma ba ta fatan hakan.
Duk da zaman lafiyar da ke tsakanin sa da matar sa amma hakan bai sa ya dena tunanin Hafsat ba.
Kuma a kullum babban burinsa bai wuce ace ga Hafsat ta bayyana ba.
Lokacin da Raba'u 'kaninsa ya yi masa waya ya sanar masa da bayyanar Hafsat, ba 'karamin farin ciki ya yi ba, domin ko ba komai a yanzu ya san iyeyenta za su sami kwanciyar hankali, musamman lokacin da ya ganta, kuma ya ji a inda ta ke, sai hankalinsa ya 'kara kwanciyar.
★ ★ ★ ★
Tun bayan zuwan Isma'il na farko gidan ya sami gurin zuwa, ya na yawan kai musu ziyara, sai dai haka kawai Hafsat ta ji bai kwanta mata a zuciya ba, duk da irin amintar da ke tsakaninsa da mijin ta kuwa.
Lokacin da aka sami hutun session ne Hafsat ta shirya tafiya Rumoh da nufin yin kwanaki don ta gaggaisa da dangin ta.
Driver'n Hajiyansu aliyu ne zai kai ta, sai d'okin tafiyar ta ke. Lokacin da Isma'il ya ji zan cen tafiyar, shima sai da ya bata kud'i masu kauri don ta sayi tsaraba.
Hafsat ta so ta 'ki kar6ar kud'in amma sai Aliyu ya ce ta kar6a, haka dai ta kar6a ba don zuciyarta na son kar6ar ba.
Ranar asabar aka sa za'ai tafiyar, cikin hukuncin Allah kuma sai tafiyar ba ta yiwu ba sakamakon zazza6in da driver'n ya tashi da shi a ranar dole aka d'aga tafiyar sai washegarin ranar.
Da daddare bayan sun gama komai sun kwanta, suka dinga hira, har Aliyu ke tambayar Hafsat yake cewa "ni kuwa Hafsat me yasa idan Isma'il ya yi miki kyauta bakya son kar6a?"