Sashe 1
Duk Kanwar Jace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[7/1, 6:23 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE
Story and Writing by
Ummu Aisha
🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛
1⃣
Kyakkyawar matashiya ce 'yar kimanin shekara ashirin da bakwai zuwa da takwas ta shigo parlourn, kallo d'aya zaka yi mata kasan cewa a matuk'ar gajiye ta ke.
Tana shigowa ta ajje jakarta da mayafi akan kujera, ta nemi wuri ta zauna, tana maida numfashi kamar wadda tayi gudun tsere ta gaji.
A hankali ta d'ago tana amsawa Auntynta da ke mata sannu da zuwa, cikin kasalalliyar muryar da ke nuna gajiyawar mai ita.
Ta jima zaune kafin ta miqe tsaye, ta dubi Aunty dake zaune hannunta rik'e da remot ta ce ‘’bari na shiga ciki na d'an watda ruwa ko zan ji dad'in jiki na‘’.
Idanun ta na kan TV ta amsa mata da cewa "To kiyi sauri dai ki fito ki ci abinci, don nasan tun da kika bar gidan nan baki ci komai ba".
Bata ce komai ba sai murmushi da tayi ta wuce zuwa d'aki, tana shiga ta cire kayan jikin ta ta wuce toilet don yin wanka.
Ba ta fi minti goma ba ta fito daure da towel a jikin ta, kai tsaye ta wuce gaban madubi ta ja kujera ta zauna, sai da ta goge ruwan jikinta sannan ta shafa mai da powder, sai lip gloss da ta shafa a le6nta ta miqe ta wuce wardrobe don d'auko kayan da za ta saka.
Doguwar rigar atampha ta saka, wadda tai mata matuqar kyau, sai turare da ta fesa a jikinta, sannan ta fita parlour don bin umarnin Auntynta.
Lokacin da ta fito babu kowa a parlourn, don haka sai ta wuce kitchen ta d'ebo abinci, ta fito ta zauna ta fara ci.
Bata dad'e da zama ba Aunty'n ta fito, bayan ta zauna ta ce "amma Hafsat da alama yau kin sha aiki don duk jikinki ya nuna alamun gajiyawa".
"Ke dai bari Aunty yau patients ne sukai min yawa ga Dr. Sakeena da zata karb'eni bata sami zuwa ba, ta tafi ta'aziyar wani abokin mijinta da ya rasu".
"Allah ya ji k'ansa"
"Ameen"
Bayan ta kammaka cin abincin ta d'auki plate d'in zuwa kitchen, sai da ta wanke sannan ta dawo parlour ta zauna.
A lokacinne Aunty ta tattara hankalinta a kanta bayan ta kashe TV da ke aiki sannan ta kira sunanta cikin nutsuwa.
"Hafsat Magana na ke so mu yi da ke, kamar yadda Uncle d'inki ya umarce ni, duk da maganar ba bak'uwa ba ce a gareki.
A jiya da daddare Yaya Halliru ya kira shi akan maganar aurenki, domin ya ce gaskiya hankalinsu ba zai ta6a kwanciya ba sai sun ganki a d'akin mijinki.
Ki tuna Hafsat duk wani matsayi da zaki taka a rayuwa to martabarki ba za ta ciki ba sai kina da aure, don haka na ke shawartar ki da a cikin masoyanki ki duba ki za6i d'aya ki aura".
Cikin sanyin jiki Hafsat ta d'ago idanuwanta tana kallon ta ta ce "Aunty aure again? Me na tsinta a cikin aure da zan sake marmarin yinsa?
Don Allah na roqe ki kisa baki a daina min maganar aure, nayi alk'awarin insha Allahu zan kame kaina ba zan yi wani abu na ashsha ba.
A yanzu babu maganar da take tayar min da hankali irin maganar aure, wallahi Aunty maza abin tsoro ne, a lokacin da suke son lalla6a mace babu abinda ba za su ce mata ba, amma idan k'addara ta had'a ku zama wuri d'aya a lokacinne zaki gane cewa DUK KANWAR JA CE".
"Kar ki ce haka Hafsat duk da a baya kin shiga matsaloli a dalilin aure kar wannan yasa ki yi wa maza kudin goro, domin ba duk suka taru suka zama d'aya ba".
Shiru Hafsat ta yi ta kasa bata amsa sakamakon sallamar da ta taji ta yara, alamun yaran gidan sun dawo daga islamiyya.
Hafsat ce ta miqe daga inda take zaune ta saka yaran a gaba zuwa d'akinsu, sai da ta tabbatar manyan sun cire unifoam sun saka kayansu, itama ta cirewa k'ananan ta shiryasu sannan ta fito.
Lokacin da ta fito daga d'akin yaran sai ta sami Uncle d'inta ya dawo don haka tana yi mai sannu da zuwa ta wuce kitchen don d'ora girkin abincin dare.
Tuwon alkama tayi miyar busasshiyar kubewa, ana gaf da kiran sallar magriba ta gama, sai da ta tsaya ta gyara kitchen d'in ta fitar da abincin dining area sannan ta wuce zuwa d'akinta, don yin wanka tun da tasan ba yin sallar za tai ba, saboda tana fashin salla.
Bayan sallar isha duk ahalin gidan suka taru a dining table don cin abincin dare, bayan sun gama suka koma parlour kowa yana harkokin gabansa har zuwa 10:00 pm, kowa ya nemi makwancinsa.
Sai da ta gama duk wani abu da ta saba kafin kwanciya bacci sannan ta hau gado ta kwanta, amma sai dai sam bacci ya gagari idanunta, sai ma tunanin maganar da sukai da Aunty d'azu da ta shiga dawo mata a k'wak'walwar ta, ta runtse ido cikin takaici, a duniya babu abin da ta tsana irin ayi mata maganar aure, amma ta lura iyayenta ba za su mata uzuri ba duk da sun fi kowa sanin irin bak'in ciki da wahalhalun da ta sha a gidajen aurenta.
Babban takaicinta ma shine a shekarunta da basu kai talatin ba a ce tayi aure har sau uku, wannan abin shima yana cin zuciyarta, duk da ta yarda cewa hakan yana ciki k'addarar rayuwarta.
Ta dad'e tana tunani har zuwa lokacin da bacci yayi nasar d'aukarta.
Da asuba ana kiran assalatu ta tashi duk da ba sallar zata yi ba, kasancewar ta riga ta saba da tashi dai dai wannan lokacin, ta shiga toilet ta sake pad d'in jikinta ta yi alwala, ta fito ta zauna tana tasbihi har zuwa lokacin da masallacin unguwar suka idar da sallah, sannan ta fita kitchen don d'ora break fast.
Ummu Aisha
[7/1, 6:24 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦

2⃣
Bata dad'e a kitchen d'in ba Aunty ta shigo suka ci gaba da aikin tare har suka kammala, suka juye komai a warmers, sai ta fita ta fara gyara parlour ta bar Aunty tana gyara wurin da suka 6ata a kitchen, da kuma wanke kwanukan da su kai amfani da su.
Zuwa 7:00am sun kammala komai, don har yaran an tashe su daga bacci, masu girman sunyi wanka, sun yiwa qannensu, duk sun shirya cikin unifoam, kowa ya fito aka karya, Uncle ne ya wuce da yaran zai sauke su a makaranta, Aunty ta tsaya tana gyara wurin da akai break-fast, ita kuma Hafsat ta shiga d'aki don k'arasa shiryawa, ta fito ta wuce wurin aiki.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali da walwala, sai dai a b'angaren Hafsat babu abin da tak'i jini irin ayi mata maganar aure domin tace naji dad'i shine gari ba na saba ba.
Ranar juma'a da misalin 4:30 na yamma Aunty na kitchen tana aiki Hafsat kuma da sauran yaran suna zaune a parlour suna kallon wani indian film, suka ji ana sallama, ai da gudu qananan suka tashi suna murnar Uncle oyoyo, duk suka nufi gurin shi.
Fuskarsa d'auke da murmushi ya qaraso cikin parlourn tare da yaran ya sami wuri ya zauna, Hafsat na zaune, sai da ta bari yaran sun gama gaida shi sannan ta gaida shi, amma ko jira ya amsa batai ba ta mik'e ta shige d'aki, kawai ya bita da kallo har ta shige ta rufo qofar.
Idan da sabo yaci ace Abubakar ya saba da irin wad'annan abubuwan daga Hafsat, amma ya kasa sabawa, don yanzu ma ji yayi zuciyarsa nayi masa zafi.
Ko don zumuncin dake tsakaninsu bai kamata ace tana nuna masa halin ko in kula irin wannan ba, duk da yasan cewa shi mai tarin laifi ne a gare ta amma ai ya bata haquri, kuma ko Ubangiji ma muna masa laifi ya yafe mana bare mu 'yan adam.
Fitowar Aunty daga kitchen ne ya katse masa tunanin sa, sun gaisa cikin mutunci yake tambayarta Uncle Tahir, ta ce ya fita.
Bai dad'e sosai ba yayiwa Aunty sallama, sai ya cewa Mas'ud ya kira masa Hafsat, shi kuma ya fita harabar gidan yana jiranta.
Saqon na isa gareta ta koro d'an aiken, ya fito yana zun6ura baki, Aunty dake qoqarin shiga kitchen ta tambaye shi ya akai?
Sai yace "Koro ni tayi tace karna dame ta".
Umartarsa tayi da ya koma ya zauna, ita kuma ta shiga d'akin ta sami Hafsat zaune tana daddana wayarta, ta ce "Hafsat bake ake kira ba?"
Cikin sanyin jiki ta d'ago kai ta kalle ta, sannan tace "Yanzu tsakani da Allah Aunty me zan masa?Tun tuni na gaya masa ya fita daga cikin rayuwata, ni ko aure zanyi ba aurarsa zanyi ba ya kamata ya shafa min lafiya".
Cikin sigar rarrashi Aunty ta ce "To yanzu dai tashi kije, kinsan wulak'anci bashi da dad'i".
Dole ba dan zuciyarta ta so ba ta miqe ta d'auki hijab ta saka ta fita don bin umarnin Auntyn ta.
Ummu Aisha
[7/1, 6:24 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦
DUK KANWAR JA CE
Story and Writing by
Ummu Aisha
🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana Allah)🤜🤛
3⃣
Lokacin da ta fito tsaye ta same shi ya jingina da jikin motarsa, tun da tayi sallama bata k'ara ce masa komai ba, sam fuskarta babu alamar walwala.