← Book details Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 15

Sashe 9

Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tohm naji bazan tafi ba Muhammad ka kwantar da hankalinka, nima faÉ—a kawai nake ba gurin da zan iya tafiya nabarka a cikin wannan halin. cewar Abbu yana goge kwallar da tazubo masa.
Shiru Abba yayi sai ajiyar zuciya da yake saukewa kamar wanda yayi gasar gudu.

Bari naje na duba Ahanaf É—in naga awane hali yake ciki, kafin nasan wane mataki yakamata naÉ—auka akan wannan case É—in.
Abba yace"Ahanaf baya nan fa Yaya ya tafiyarsa, dama na faÉ—a maka yanzu wannan yaron bayajin magana kwata kwata ba wanda ya isa da shi" Abba yafaÉ—a yana yamutsa fuska alamar ko ajikinsa baiji tafiyar ta Ahanaf É—in ba.
Abbu yace Subhanallah "Ahanaf yatafi kuma? ina yatafi? meyasa kuka barshi yatafi?"
Nima bansan tafiyar tasa ba "É—azu ne abokanan Shashancinsa suke faÉ—a muna wai baya nan Suma bayan sun dawo daga Masallaci ne suka nemesa suka rasa" Ni bam ma gama yarda da zancen Nasu ba saboda nasan duk bakinsu É—aya dashi maybe ma da sanin su yatafi.
Amma sunzo suna faÉ—awa Mutane maganar ban....
Tsawa Abbu ya daka masa cikin hargowa yace kasan mai kake faÉ—a kuwa Muhammad "Ahanaf É—in ne baya nan kuma kake nan hankalinka kwance?"
Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un Abbu ya faɗa yana fita daga ɗakin cikin sauri kamar zai tashi sama, direct part ɗin Su Shadow ya nufa ransa a masifar ɓace, ƙofar palon ya tura da ƙarfi ya Shiga ba ko sallama yana kwaɗa kiran Haidar.

Haidar da yake tsaye a tsakiyar palo yana waya da wani abokinsa D.P.O Abdul-Naseer akan wannan case É—in na Shadow.
Da sauri Haidar yajuya dan ganin waye yashigo haka ba ko sallama, kuma yana ta ihun kiran sunansa.
Ido huÉ—u sukayi da Abbu wanda yake cikin matsanan cin tashin hankali.
kallo É—aya Haidar yayi masa ya gane Shine Abbu,
Saboda yana ganin pics É—insa a cikin wayar Shadow kuma ko bayan haka suna matsananciyar kama da Abba.
Ina zuwa D.P.O Haidar ya faÉ—a tare da katse wayar da ya keyi.
Ina wuni Abbu barka da zuwa ya hanya?
Duk a cikin gaisuwar nan da Haidar yakewa Abbu ba wacce ya Amsa,
Saima tambayar da ya jefa masa, yace Haidar ina Ahanaf?

Abbu dan Allah ka zauna mana sai muyi maganar.
Ba musu Abbu ya zauna dan ya ƙagara yaji gaskiyar wannan batun.
Shima Haidar zama yayi a ƙasa kusa da ƙafafun Abbu, ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin nutsuwa ya fara bawa Abbu labarin duk Abunda yafaru jiya bayan sun gama yawa dashi.
Da neman da sukayiwa Shadow basu ganshi ba har izuwa lokacin da sukaje faÉ—awa Abba Abunda yake faruwa da kuma irin koyar da Abban yayi musu.

Iska mai zafi Abbu ya furzar ya É—auki kusan 3min baiyi magana ba, a hankali ya maida kallon akan Haidar yace wane mataki yanzu kuke ganin yakamata a É—auka? ko kuma akwai wanda kuke zargi?

Gaskiya ba wanda muke zargi Abbu.
Amma kuma akwai wani Abu da yayi matuƙar ɗaure muna kai, bayan mun duba ko ina bamuga Ahanaf sai muka ga wata ƙofa ta baya
bayan mun bi hanyar sai muka ɓulla ta gurin garden, muna dudduba gurin sai mukaga key ajikin ƙofar ɗakin ta baya tohm a nan ne muka tabbar lallai wani ne ya buɗe ƙofar ta baya Ahanaf yafita.
Yanzu ma haka key ɗin yana nan na aje muna su ayi bincike akansa dan gano zanen hannun waye akan key ɗin, Yanzu ma da kaga ina waya magana nake da wani abokinmu, shi ɗan sanda ne babba da ya ƙware agurin harka bincike.
Yanzu ma haka yana hanya zaizo nan gidan saboda a É—auki zanen hannu duk wanda yake gidan nan har masu aiki domin gano waye mai wannan laifi, kuma menene dalilin da yasa ya buÉ—e Ahanaf. Haidar ya faÉ—a cikin nutsuwa.

Tabbas wannan tunanin naka abune mai kyau Haidar,
Ba Shakka ku friends ne Nagari kuntsaya tsayin daka dumin abokin Ku.
Ba kutafi kun barsa ba duk da Abunda mahaifinsa ya Muku.
Banida Abunda Zan Saka Muku dashi Allah yayi Muku Albarka Kuma ya kare Ku Aduk Inda kuka Shiga.
Ameen Abbu Mun gode.
Wayar Haidar ce tafara ringing Yana dubawa yaga D.P.O ne Ke Kiransa, maybe ma ya karaso Haidar yaÉ—ada Yana Kara wayar a kunnensa.
Okey jirani agurin ina zuwa Haidar ya faɗa yana tashi tsaye, ya kalli Abbu yace Abbu muje D.P.O ya ƙaraso yana waje.
Tashi Abbu yayi yabi bayan Haidar suka fita tare.

ƙara gaisawa Sukayi da D.P.O
Sannan D.P.O yace yakamata muyi Abunda ya kamata saboda inada meeting anjima kaÉ—an Insha Allah.

Abbu ya kalli Haidar yace ina wannan Abokin naka da kake magana?
yana gurin wanka Amma zai fito yanzu insha Allah.

Duk wani Mahaluki da yake
Rayuwa agidan ya Hallara a babban palon Alh Muhammad Imran.

Cike da mamaki Abba yake bin kowa na falon da kallo, kafin daga ƙarshe ya maida kallonsa akan Abbu
yace mai yake faruwa haka ne? menene dalilin duk wannan taron yaya? zaka kasani yanzu Abbu yafaÉ—a yana maida kallonsa akan D.P.O Abdul Naseer.
Yace zaka iya fara aikinka D.P.O.

Bayan an gamawa kowa a kazo kan Abba amma fafir yace shi baisan zancen, ba bazai bayar da hannunsa ba.

Wallahi wannan ne kuma baka isa ba Muhammad........ ✍️✍️✍️

Taya akayi Shadow ya zama Amanar Abba?

Raɗaɗin mutuwar waye yasa Abba ya ɗauki Alƙawarin rike amanar Shadow?

Tohm waye ya Bawa Abba Amanar Shadow?
Bayan Alh Muhammad Imran ( Abba) Shine mahaifin Ahanaf (Shadow).

Tabbas akwai wata ƙullalliya a ƙasa😥

Nabeela Binji ce💃💃💃

Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610

More comment
More taping 😉😉

Share Fisabilillah 🙏.

♣️DUHUN INUWA ♣️

TAPING......📲📲📲

STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI

PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM

PAGE

0️⃣9️⃣

Wallahi wannan ne kuma baka isa ba Muhammad............

________________Yazama dole ayi bincike a kanka Kamar yadda a kayiwa Kowa, "Idan har Kuma kace baza ka Bari ayi ba tohm ba shakka Kaine ka buɗe wannan ƙofar kuma ka kori Ahanaf daga gidan nan.
Idan har hasashena gaskiya ne wllhy Muhammad sai ka fuskanci mummunan hukunci daga gareni.
Kuma kasani idan har hakan yazama gaskiya Wllhy bani ba kai har abada.

Muhammad kasan wanene Aliyu idan na faɗi magana koda mutuwa ce zata gifta a gabana bazan canza ra'ayina ba. cewar Abbu cikin matsancin ɓacin Rai.

Duk wanda yake a Palon yashiga tashin hankali da jin furucin Abbu.
Shida kasansa Abba ya ruÉ—e sosai yajima baiga yayan nasa acikin irin wannan fushin ba.
yaya dan Allah k.. É—aga masa hannu Abbu yayi tare da cewa bana son jin komai daga bakin ka Muhammad, Wallahi dole ne kayi É—aya daga cikin biyun Nan, kodai kabari ayi bincike akanka Kamar Kowa Ko Kuma ka gayamin gaskiyar Abunda yafaru da Ahanaf a Daren jiya.

Maganar gaskiya bansan Abunda ya faru da Ahanaf ba a Daren jiya, Kuma wllhy Yaya bani na Buɗe ƙofa yafita ba.
Hasalima Ni ban yadda cewa yasamu taɓuwar hankali ba, Kawai ya tafiyar sane Saboda Abunda yafaru, su kuma su kazo da nufin tayar Mana da hankali, Amma Idan har wannan binciken zaisa kadaina zargina Kuma kajanye wancan zance Na cewa Zaka tafi kabarni Na Har abada tohm Na yadda ayi Koma Menene Yaya,
Abba yafaɗa cikin ɗacin Rai tare da ƙarajin tsanar Ɗan nasa Ahanaf, saboda gabaki daya Abba yadauki laifin komai yadaurashi Akan Ahanaf Wanda Idan aka saka shigaba akace ya faɗi dalilin Tsanar da yake yiwa Ahanaf Tabbas ba Wani dalili Dan Shi da kansa Bai San dalilin ba.
Kallon d.p.o Abbu yayi yace Zaka iya Fara akinka Kamar yadda kayi Akan Kowa domin goge zargi.

Bayan d.p.o yagama duk Wani binciken da zaiyine ya Koma Kan ɗaya daga cikin kujerun palon ya zauna tare da zare glass din idonsa ya kalli Abbu yace tabbas akwai sarƙaƙiya acikin wannan case ɗin Ranka yadaɗe.
Mai aikata wannan laifin yanada matuƙar wayau da basira,
saboda ba ta inda yabar wata shaidar da za'a iya kamasa,
Tabbas Bai kwaɓar ba
A Ko Ina ya kiyaye Akan abun harinsa da Kuma goge duk wata hujjar da zata nunasa, Yana aiki da kwakwalwar sa yayin da mu yake Mana Wasa da tamu kwakwalwar
D.p.o yafaÉ—a Yana gyaÉ—a Kai cikin mamaki sai kuma yasaki murmushin da shine KaÉ—ai yasan dalilin yinsa.

Kallonsa ya Maida Kan Abbu yace tabbas Koma waye yake aikata wannan laifin ya iya takonsa sosai ranka yadade,
Amma hausawa sukance Karen Bana shine maganin zomon Bana,
Mai laifi har yake da kwarin gwiwa ayayin da yake cikin ganiyar aikata laifinsa tohm Taya Mai bincike zai Sare agurin gano mai laifin?
Yanzu za'a Fara wannan wasar, tabbas Sai an ban bance tsakanin Ƙarya da gaskiya.
ka kwantar da hankaliki Alh Zanyi iya bakin ƙoƙarina dan ganin Na Nemo Maka Ahanaf tare da binciko Maka Mai laifin a duk inda yake a faɗin duniya insha Allah, d.p.o Abdul naseer yafaɗa cike da tabbatarwa.

Gyara Zama Abbu yayi tare da cewa nagode sosai yaro Allah yayi Muku Albarka, sanna duk Wani Abu da kake bukata Na dangane da bincikenka Zaka iya tuntuɓar su Haidar saboda nasan bazasu ɓoye Maka komai ba insha Allah.

Sannan a duk lokacin da kake son kayi bincike Ko Kuma kayiwa Wani wata tambayar Ni Nan nabaka damar shigowa gidan Nan Kai tsaye Domin gabatar da aikinka yadda yadace.
Chapter 9 · 0% Book details