← Book details Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 15

Sashe 6

Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duka fa Abba ya tambaya cike da masifa, Kai jakine da zai dakeka haka? Ah lallai wannan Yaron Dani yake zance, ai bakai yakamata yasamu yadaka ba, Ni yakamata yadaka Nida Na É—aura auren. Ina Ahanaf É—in yake yatambaya cikin faÉ—a.

Gyaran murya Kamal yayi cikin girmamawa yace Yana ɗaki Abba, Kuma gaskiya Ina tunanin Kamar bashida lafiya saboda Yana can Sai faman farfasa Kaya yake a part ɗinsu Kamar Wani Wanda yasami taɓuwar hankali,
shine nace Ko zakuzo muje kuga halinda yake ci...

Dan Allah da kata Abba ya faɗa Rai a ɓace, ba Wani taɓuwar hankali da yasamu tsabar rainin hankali ne da yayi Masa yawa.
Kuma tinda Har Ahanaf ya nuna ban Isa dashi ba kuma ban isa nasaka doka yabita ba, tohm kusani daga yau ba ruwana da lamarin rayuwar sa yaje yayi duk Abunda yake ga yafi Masa a rayuwa Abba ya faÉ—a cikin sound Na gaskiya da gaskiya.

Kamal da Ayiya mutuwar tsaye sukayi saboda tsabar mamakin wannan lamarin Na Abba.

Janyo Ƙaseem Abba yayi kusa dashi tare da cewa Allah yayi Maka Albarka Ƙaseem naji daɗi sosai Kuma nagode da kamun biyayya akan Abunda Na umarce ka.

Ita ma Kanta matar taka ta amince da kai a matsayin mijinta, É—azu mahaifinta ya kirani a waya yake gayamin, kaga yanzu Sai kaje kayi duk Wani Shiri da zakayi katafi gidanka saboda natura motocin É—aukar amarya tun É—azu.

Cike da matsancin farin ciki Ƙaseem ya rungume Abba Yana dariyar murna yace nagode sosai Abba Allah yasaka Maka da mafificin Al khairi, Amma Abba wane gida za'a kaita.

Gidan da wancan shashan Yaron yagina Mana Ƙaseem, ai tinda daman dan ita Norr ɗin aka Gina Shi tohm shakka Babu a ciki zata zauna.

Wallahi wannan Kam ƙarya ne Alh ai wannan Zalunci yayi yawa da wanne zaiji? "Budurwarsa, Sadakinsa, gidansa? Bazan bar haka tafaru ba Alh Yaron Nan fa Shima ɗanka ne Kuma jininka, ko menene ya aikata Maka Bai cancanci wannan mummunan hukuncin daga gareka ba" Idan ma ka Hana Shi auren yarinyar Nan kamata yayi kabar Masa duk Wani Abu da yake mallakinsa.

Bazanyi haka ba Shuwa, "ba fa kece Mai mulkina ba nine Nan nake mulkinki, Ni nakeda hakki akan ki Dama yaran naki gabaki daya Dan haka Na gama yanke hukunci Akan kaseem zai tare a gidan da Ahanaf ya Gina saboda ana iyayen yarinyar suka Saka kayan Yar su, kinga Kuwa ba Inda yakamata su zauna sama da can.

Bazan musamaka ba Alh saboda nasan Kaine mahaifin Ahanaf Kuma Kaine mahaifin Al kaseem, Amma Abunda nake so kasani shine bazan zauna Nan gidan ba, Zan bar Maka gidan ka, Kuma Zan tafi da Ahanaf gidanmu Naci gaba da kulawa dashi acan Amma alfarma daya nake rokonka shine kamanta damu arayuwarka Dan Allah tafada tana hada hannayenta guri daya alamar roko hawaye Sai zarya suke akan kumatun ta.

Ba Inda zakije Shuwa kina gidan nan Insha Allah, Amma Shi duk gurin da zaije yaje Bani da matsala da haka, ya faÉ—a cikin nuna halin Ko in kula Akan ÆŠan nasa, Wanda ada yake mutuwar so da kauna saboda shine É—ansa Na farko aduniya.

Wannan Kuma kayi kaÉ—an Muhammad dole nabar Maka gdnka tunda ka nuna Ni ban isan nasan Abunda kake shiryawa ba, ban Isa nasan dalilin wannan hukuncin da ka yanke ba, tohm menene an fanina agurinka ai kaga gwara Kawai natafi.

Abba yarasa abinda yasa Aduk lokacin da Haj Shuwa ta furta cewa zata tafi ta bar Masa gidansa Sai yaji Wani matsancin ɓacin Rai da fargaba sun dirar masa a zuciya.

Ba Inda zakije Shuwa cewar Abba, wallahi muddin Kika fita daga gidan Nan to fa kisani bakin aurenki.
Yana gama Faɗin haka yaja hannu Al ƙaseem suka bar ɗakin cikin sauri Kamar wa ƴanda zasu Tashi Sama.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un ita ce Kalmar da Kamal keta nanatawa, cikin tashin hankali da Al ajabin wannan lamarin shidai tinda yake arayuwa Bai taɓa Jin makamancin wannan abun ba, Ko a film Ko a novel Amma a yanzu ga abun yana faruwa agabansa Yana kallo.

Gurin Ayiya Kamal ya ƙarasa Kamar Wanda kwai yafashewa a ciki, tare da Kama hannayenta ya zaunar da ita a gefen gado yace ki daina wannan kukan Dan Allah Ayiya,
kuka fa bashine mafita ba a wannan halin, Kawai Neman mafita shine Abunda ya kamata muyi,
Yanzu kitashi mutafi gurin Ahanaf ɗin kiga halinda yake ciki saboda lamarin Sana Sai ƙara ta'azzara yake.

Bazan iya ba Kamal bazan iya kallon Ahanaf acikin halinda bazan iya taimakonsa ba Kawai kuje kuyi Masa Abunda yadace, Idan ma asibiti zaku Kaisa kukai sa Dan Allah Kamal.

Cike da mamaki Kamal yake kallonta duk da yaga Kamar da ya nayin tausayawa a fuskar ta tayi maganar, Amma Bai kamata tace Wai bazata iya Zuwa taga a wane hali ÆŠan nata yake ciki ba. Har zai buÉ—e baki yayi Magana kome yatuna Sai kuma ya rufe bakinsa, tare da Tashi yabar É—akin ransa bace.

Tabbas wannan jarabawar bama tabuwar hankali yakama a ce Shadow ya samu ba, kamata ma yayi ya mutu Ko zai Sami salama a rayuwa, haba wannan Bala'in Har Ina cewar Kamal hawaye nabin fuskar sa.

Koda ya Koma É—akin a yadda ya barsu a haka yasame su, Shadow Sai zuba zanensa yake a Bango, Kuma babban abun mamakin shine duk da Baya cikin hankalinsa zanensa yake Kamar yadda yasaba, cikin kwarewa irin ta kwararren ÆŠan Zane.

Kamal ya kalli Haidar yace Dan Allah É—an zo Kaji, ba musu Haidar yabi Bayan Kamal tare da rufe k
Ƙofar gudun Kar Shadow ya fito.

Bayan sun dawo Palo ne sun zauna Kamal ya kwashe duk Abunda yafaru Bayan fitar sa daga dakin da sunan Kiran Ayiya ya fadawa Haidar.

Tirkashi shine Abunda Haidar yasami damar furtawa Yana goge zufan da ya zubo daga goshin sa,

Sun dauki lokaci Mai tsawo ba Wanda ya iya cewa Kala a cikin su, kowa da tunanin da yake a cikin zuciyar sa.

Haidar ne ya dago ya kalli Kamal yace Kamal yanzu ya zamuyi Dan ganin mun taimaki Shadow?

Nima tunanin da nake Kenan Haidar Amma duk iya tunanina nakasa samu Mana mafita.
Dukan su shiru sukayi Suna tunani.
Sai can Kamal ya dago ya kalli Haidar yace Na samu mana mafita Haidar
Ciki zakuwa Haidar yace Mai Cece mafitar Kamal?

Gayara Zama Kamal yayi tare da cewa Abbu, tabbas Abbu Shi kaɗai ne mafitar mu,. saboda nasan duk Wanda Abun da yake faruwa bashida masaniya Akai Shi Kawai yakamata mukira mugaya Masa Abunda yake faruwa Insha Allah Shadow zai Sami a dalci.........✍️✍️✍️

Wane ne Abbu?

Shin waye Abbu agurin shadow?

Kuma wane matsayi yake dashi agurin Abba da Har su Kamal suke tunanin Kai ƙarar Abba agurinsa?

Kuma Idan sun Kai Masa ƙarar zasu samu Abunda suke so?

Nabeela Binji ce💃💃💃

Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610

More comment
More taping 😉😉

Share Fisabilillah 🙏

♣️DUHUN INUWA ♣️

TAPING......📲📲📲

STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI

PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM

Page

0️⃣6️⃣

________________Haidar ne ya ciro wayar Shadow daga cikin aljihunsa yace bara mugwada Kira muga Ko zata Shiga.

Cikin Sa'a wayar tafara ringing shiru sukayi Suna jiran ya É—auka, Amma har ta tsinke ba'a É—auka ba sake Danna Kiran Haidar yayi Sai da suka Kira sau ukku kafin suji an É—aga tare da sallama,
Amsa sallamar Haidar yayi tare da gaida Shi,
Amsa gaisuwar Abbu yayi tare da cewa Yan samari lafiya Dai Ina Ahanaf?

Gyaran murya Haidar yayi sannan yace gaskiya Dai Kam ba lafiya ba Abbu, saboda........ Nan Haidar ya gayawa Abbu duk Abunda yake faruwa.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un Abbu ya faÉ—a cikin tashin hankali, ruÉ—u da Kuma Al ajabi.
Abbu Yace yaro ka tabbar Abunda kake faÉ—amin gaskiya ne Kuwa?

Wallahi gaskiya Na faÉ—a Maka Abbu,
Ai wannan lamarin yafi ƙarfin ayi Wasa da Shi, yanzu ma haka maganar da nake Maka shine an kai Norr agidan da Ahanaf ya Gina, a matsayin matar ƙaseem. Haidar yafaɗa cikin ƙunar Rai.

Subhanallah Lallai shigowa Nigeria ya Kamani gobe, zanzo insha Allah naji menene dalilin da yasa Muhammad ya yanke wannan mummun hukuncin, tabbas Idan har Bai gayamin dalili ba Toh wallahi ransa Sai yafi nakowa ɓaci.

Sosai Haidar yaji daÉ—in furucin Abbu, Allah yakawo ka lafiya Abbu Haidar yafaÉ—a Yana É—an murmushi saboda yasan Insha Allah Shadow zai Sami Æ´an cin kansa.

Ameen ya Allah yaro ya sunanka? Abbu ya tambayi Haidar.
Haidar ne Sunana Abbu, Masha Allah Allah yayi Maka Albarka Haidar,
Dan Allah kaciga da Kula da abokin Naka insha Allah gobe Zan zo.
Tohm Insha Allah Abbu Allah Dai ya kawoka lafiya.
Ameen ya Allah cewar Abbu Yana kashe wayar.

Haidar ya kalli kamal cikin sakin fuska yace insha Allah kumai zai Zama tarihi abokina.
Murmushi Kamal yayi yace Allah ya yadda Boss,
Ameen ya Allah.

Ɓangaren Abbu Kuwa yakasa koma wa bacci Sai Safa da Marwa yake Yana tunanin wannan lamarin, tabbas yasan Irrin son da Muhammad yakewa Ahanaf, baya Son Wani Abu ya same Shi ko kaɗan, harma Takai ga baya iya ɓoye son da yakeyi masa agaban Koma waye.
Iska Mai zafi ya furzar Tabbas ba banza ba Abbu yafurta a Zahiri.

Kai da waye Kuma cikin wannan tsohon Daren? Cewar Hajiya Mama wacce ta kasance Mata agurin Abbu.

kusa da ita yaje ya zauna Yana dafe kansa yace Haj Ina ga gobe zamuje gida Nigeria,

Nigeria Kuma tafaÉ—a cike da mamakin sa, saboda ita dai tasan ba yadda batayi dashi ba Akan yabarsu su tafi bikin Ahanaf ita da Yara,
Amma Sai yace a'a tinda Shima Bai samu zuwa ba to ba Wanda zaije, dalilin da yasa yace haka kuwa shine saura kwana biyar ya su Koma gida Nigeria gabaki daya,
a cewar sa Idan sunje Sai suga amaryar.

Amma Kuma shine yanzu yake cewa zaije Nigeria gobe.
Chapter 6 · 0% Book details