← Book details Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 15

Sashe 1

Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

♣️DUHUN UNUWA ♣️

TAPING......📲📲📲

STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJ

BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM

PAGE

0️⃣1️⃣

Misalin karfe 5:30 na yamma wasu masoya ne zaune a kan fararen kujerun roba, fira suke cikin farin ciki da Nishaɗi. kallo ɗaya za kayi musu ka fahimci suna matuƙar so da ƙaunar junan su, saboda ba abunda kake gani akan fiskukin su sai yalwa taccen murmushi mai matuƙar ƙayatarwa.

Saurayin ne ya kalli budurwar tasa cikin sakin fuska yace my noor tambayarki fa nakeyi kinyi shuru, nace wane event ne Kika shirya za kiyi.

Sunkuyar dakai tayi tare da saka hannuwan ta ta rufe fuskarta alamar kunya.

ɓata fuska yayi kamar zaiyi kuka yace haba my Noor wai meyasa kike min irin haka ne? a duk lokacin da nake miki maganar auren mu sai ki dinga nuna min jin kunya. gaskiya ni bana so ai idan da sabo mun zama ɗaya, ƴan kwanaki ƙalilan ne fa suka rage mana muyi aure, idan bamuyi shiri tun yanzu ba sai yaushe kenan?

Ɗan muskutawa tayi ta gyra zaman ta tare da sunkuyar da kanta kasa, a hankali cikin sanyin muryar tace kayi haƙuri my Shadow, ba wai ban damu da shirin bikin nan bane wallahi matuƙar kunyarka nakeji musamman ma da bikin nan yayi gab, sai na keji duk abubuwa suna sauyamin ba kamar da ba.

Murmushi yayi mai cike da nishaÉ—i yace wllhy kina bani mamaki my Noor, sai nakeji a raina kamar baki damu dani yadda na damu da ke bane.

Dasauri ta ɗago ta kalle shi ta shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka ta ce haka dai kake gani, but na damu da kai fin yadda ka damu dani, kuma lokaci yana zuwa zaka gani.

Murmushi yayi mai sauti tare da tashi tsaye yace tohm zan tafi ranki ya daɗe, dama na faɗa miki akwai gurin da zanje, amma sai naji ba zan iya zuwa ba ba tare da nazo naga Haskena ba. Ya ƙarisa maganar yana murmushi.
Ita ma murmushin tayi tace nagode Sosai my Shadow.

Ba godiya a tsakaninmu my Noor fatana kawai shine idan munyi aure karki zamar min DUHUN INUWA ki riƙe amanata Noor ni mutum ne wanda ke son magana ta gaskiya da gaskiya, bana son ɓoye ɓoye akan komi duk abunda zaki faɗa yaza mana gaskiya ne, koda ace naji zafin abunda kikayi tohm zanfi jin farin ciki idan kin faɗa min gaskiya akan kiyi min ƙarya, idan kin kiyaye wannan tohm ni bana da wata matsala Noor.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da kallonsa tace na daɗe da sanin wannan my Shadow. kuma insha Allah zan zama mai kiyayewa akan duk abunda baka so, sanin kan kane ba abunda nake ɓoye maka a rayuwa, kuma insha Allah ba abunda zan ɓoye maka nan gaba.

Allah ya yarda Noor,,,

Ameen ya Allah Mijina,,,

Salama yayi mata tare da hawa machine É—insa ya ta dashi yatafi. saida taga fitarsa daga gidan sannan ita ma tashiga gida tana murmushin jin daÉ—i.

Bayan sati biyu da faruwar haka shirye shiryen É—aurin aure ya kan kama saboda duk wani event da akeyi kamin É—aurin Aure an riga da an gabatar dasu.
Sai Diner da za'a gabatar gobe idan an É—aura aure.

Amarya Noor ansha kyau ta ko ina ta gibta sai tashin ƙamshi kakeji na mussamman.

Ta ɓangaren shadow kam ba dama yau gaba ki ɗaya ya kasa samun zama saboda baƙine suke zuwa na nesa wanda idan sukace sai gobe ne zasu zo tohm fa ba shakka baza su samu halartar ɗaurin auren ba.

Yanzu haka ma wasu Abokanan sa ne ya tarbo wa ƴan da sukayi Bautar ƙasa tare dasu a gombe.
daya ke su Æ´an asalin gomben ne, kuma sunyi zaman mutunci sosai da Shadow hakanne ma yasa su kaci Alwashin zuwa sokoto idan aurensa ya yazo.

Fira suke mai cike da nishaɗi da kewar juna. ɗaya daga cikinsu ne mai Suna Kamal ya kalli Shadow cike da tsokana yace angon Noor, wannan Noor ɗin da ace baka sameta ba da (maybe) gidan mahaukata ne kawai zai iya ɗaukarka, cox ban taɓa ganin wanda ya sadaukar da lokacinsa da kumai nasa akan soyayya ba kamar kai. (sometime's) fa har tausayi kake bani cox nasan halin mata basu da tabbas sun ƙware agurin karya zuciyar mutum wllhy.

Dariya Shadow yayi sannan yace kai Kamal ai ko matan ma suna suka tara, ni nan na yarda da Noor kuma na yarda da tarbiyar gidansu na yarda da soyayyar ta agareni ta gaskiya da gaskiya ce. wannan dalilin yasa bana saka Noor acikin Æ´an matan wannan zamanin, har abada ina da (confidence) a kanta, ita É—in ta musamman ce a rayuwata.

Kamal mai yasa ka cika biyar diddiƙi ne wai? ka ɗauka ko wace yarinya kalar Sadey beb ɗinka ce? wace tasan kan yaudara da karya zuciyar samari.
Haidar ya faɗa yana bushewa da wata irin dariyar ƙeta da son
Ƙufulal da Kamal ɗin.

Ai kuwa yayi nasarar haka dan nan take Kamal ya fara hauhawa kamar farashi.
ya murtuƙe fuska kamar ba Kamal ba mai son wasa da dariya,
ya kalli Haidar rai a ɓace yace wai Boss bana faɗa maka mun rabu da wannan yarinyar ba.
kuma na faɗa maka bana son maganarta, but kai na lura duk lokacin da kayi nufin baƙanta min rai sai ka dinga min maganar ta ko?
ya faɗa yana ɗauke kansa gefe ɗaya irin shi a dole an ɓata masa rai ɗin nan.

Shadow ne yakashe fitinar ta hanyar bawa Kamal haƙuri yana dariya yace kai amma kuwa Sadey beb bata kyauta mana ba.
Ni nazata idan ba kai bazata iya rayuwa ba. a dai yadda take nuna damuwarta akan ka gaskiya banyi zaton kwanton ɓauna tamaka ba kamal.

Tsaki kamal yayi yace wallahi ashe ga baki ɗaya ƙarya da yaudara ne a cikin kalaman ta.
Amma ai tayiwa kanta dan ita ce tayi rashi bani ba yafaÉ—a yana shafa sajen da ke kwance akan dogowar fuskarsa. shi a dole mai kyau ne.
yace maybe ma anan nasamu Wata mai sa'a tayi wuf dani, dan naji ance Æ´an matan garin nan akwai soyayyar gaskia da iya kula da saurayi ko? ya faÉ—a yana kallon Shadow.
Dariya sukayi ga baki É—ayan su.

fira suke cikin nishaÉ—i
A haka har suka ƙarasa gidan su Shadow da ke a unguwar Minannata.

RANA BATA ƘARYA.😞😞

Ayau 15/12/2021 dan dazon jama'a suka taru domin shaida É—aurin auren
Ahanaf Muhammad Imran (Shadow) da
Noriya Mukhtar Salah (Norr).

Kamar yadda aka Saba idan anzo É—aura aure dole sai mutane sun haÉ—u dangin ango dana amarya bayan kowa ya hallarane aka zauna domin gabatar da abunda yatarasu agurin.

Hankalin Shadow ya koma kan abokansa da suketa faman zolayarsa.

Saiji yayi Gurin yakaraɗe da muryar wani ba banbaɗe. inda yake cewa Alhmdllh an ɗaura auren NORIYA MUKHTAR SALAH da angonta AL-ƘASEEM MUHAMMAD IMRAN akan sadaki naira dubu ɗari cif lakadan ba ajalanba.

Shadow ne ya tashi da sauri har Yana tangadi ya kalli abban sa yace Abba kunyi kuskure fa sunana Ahanaf Muhammad Imran ba Al ƙaseem Muhammad Imran ba. Abba da Al ƙaseem aka daura auren Nan bani ba? Dan Allah Abba kagaya musu wannan sunan ƙanina ne ba nawa ba.

Abba me yake faruwa ne? Dan Allah agyara sunan nan Abba, Shadow ya faÉ—a cike da ruÉ—ewa da firgici kwallah fal idanunsa.

Wanda yaketa faman Kira da Abban ne yakama hannunsa yace Ahanaf muje gida sai nayi maka bayani kaji.

Dasauri ya kwace hannunsa daga na mahaifin nasa.
Cikin murya Mai Amo da nuna zallar bacin Rai yace Abba baxan bar Nan gurin ba har sai kun gyara wannan Rikitaccen Al amarin da kuka kulla.
Dan girman Allah Abba kugyarashi tunkan hankalin mutane yadawo Nan su fahimci halinda ake ciki.

Abba Norr fa da Al kaseem? Me nayi muku ne haKa Mai zafi da har zaku dauki fansa ta wannan hanyar?
Abba idan har laifi na maka kayi min komai Amma Banda hanani auren Norr dan Allah, wllhy Abba Ina sonta Kuma bazan iya rayuwa ba idan har Bata.
Abba karka jefa rayuwar É—an ka a cikin DUHUN INUWA plxx.
Abba ko dai ba kaine mahaifin... Kafin ya rufe bakinsa sai jin wani zazzafan Mari yayi tasssssssssss a kumatunsa.

Ɗagowa yayi da sauri ya kalli mahaifin nasa cike da matuƙar mamaki.
Yau shine Abba ya mara Kuma akan gaskiyar sa?

Abba da ko faɗa baya bari ayi masa bare a ɓata masa rai saboda Yana da sunan mahaifin sa.
Amma yau har da Mari.
Shin kodai mafarki nakeyi ne? Shadow ya tambayi kansa cike da rudani.

Ba mafarki kake ba Ahanaf wannan zahiri ne cewar Abba dake ta faman sauke nunfashi cike da ɓacin rai.

Abba ya ƙara da cewa Ni mahaifin ka Muhammad Imran na ɗaura auren Noriya Mukhtar Salah da na Al ɗaseem Muhammad Imr..... Ai kafin ma ya rufe bakin sa Nan take Shadow ya zube ƙasa ba alamar Numfashi a tare dashi.

TIR ƘASHI🙆🙆🙆

Taya hakan tafaru?

A Ina matsalar take?

Menene dalilin da yasa su Abba sukayiwa Shadow hakan?

Anya kuwa Norr zata yadda da Ƙaseem a matsayin miji?

Shima Ƙaseem Zai karɓi Norr a matsayin mata duk da yasan irin son da yayan sa yake mata?

Ko dai Shadow yanada wata matsala ne?

Ku dai ku kasance tare Dani Nabeelah Shehu Binji Dan jin yadda wannan Al amarin Mai matukar sarƙaƙiya zai kasance.

Nabila binji☎️☎️
09064314811
09161107610

More comment
More taping 😉😉

Share Fisabilillah 🙏🙏🙏

♣️ DUHUN INUWAH ♣️

STORY

AND

WRITING ✍️✍️✍️

BY

NABILA S BINJI

PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

Hadiths of imam An-Nawawi
Chapter 1 · 0% Book details