← Book details Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 15

Sashe 15

Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Batada Wanda zai amsa Mata waÉ—an nan tambayoyin Sai wannan mahaukacin Ahanaf Shadow Amma Taya Kenan?
Wanda Har yanzu Bata Ji Maganar sa ba,
Jin Kanta Yana mata ciwo ne yasa dole ta haÉ—a kayan tamayar dasu cikin jakar Amma Banda takardun da suke É—auke da Zanen Shadow da Norr.

Wayarta ta É—auka ta Danna Kiran Dr Fahad.
Bayan ya É—aga ne take tambayar sa ya jikin Mara lafiyar?
Tohm da sauƙi za'ace Dan wllhy da kyar na samu aka ririƙe shi na sake masa allurar bacci, Amma wannan Karon biyu nayi Masa Saboda na lura Yana da ƙarfin Jini, Idan akayi Masa ɗaya Zai iya farkwa kafin safe, Kuma kinga ba musan me zai iya faruwa cikin Daren ba.
Hakan ma yayi Dr.

Dr amma har yanzu baka yarda wannan mutumen mahaukaci bane ko?
Aa Shabana bawai ban yarda bane na dai faÉ—a miki gaskiyar Abunda bincikena ya nuna min ne a kansa, bashida ko wace cuta a kwakwalwar sa gaskiya, Kuma Duk Inda zaki kaishi a duba shi wannan amsar za'a baki.
Ya Allah to wai mai yake faruwa ne?
Shi ba mahaukaci ba kuma ya dinga jiwa kansa ciwo?
Tabbas wannan lamarin a kwai DUHUN INUWA a ciki wanda ya hana mu gane gaskiyar Hasken sa.
Babbar matsalar ma shine Rashin maganar sa Dr.

Hakane Shabana Amma yanzu mufara ganin yasamu sauƙin raunin da ke jikinsa sannan sai musan me yakamata muyi nan gaba.
Okay nagode Dr anan sukayi sallama ta kashe wayarta.
Gyara kwanciya tayi tare da furzar da Iskar bakinta, tambayoyi ne da yawa a Ranta Amma ta rasa mai amsa mata su.
A haka dai har bacci ɓarawo yayi awon gaba da ita.

Da safe Misalin 9am Zaune take a parlour tana breakfast wayar tace tafara ringing da sauri tayi pickup ganin sunan Dr Fahad ne a kan screen É—in wayarta.
Bayan sun gaisane yace " kizo yanzu Shabana akwai matsala gaskiya" da sauri tasaki fork É—in da yake hannunta tare da cewa matsala kuma Dr mai yafaru? Kawai Idan da Hali kizo yanzu. yana gama faÉ—ar haka ya katse wayar sa.

Ya Ilahi! Ɗakin ta tanufa tafara Shiri cikin sauri, tana gamawa ta fito parlour anan ta Tarar da iyayenta Bayan ta gaidasu ne Ammi take tambayar Ina zuwa haka? Langwaɓar da Kanta tayi tare da cewa asibiti zanje Ammi yanzun nan Dr Fahad ya kirani yace wai nazo akwai matsala.
Matsalar me? Dady ya tambayi Shabana.
Nima bansani ba Dady yace dai sai nazo zanji.
Kai ya gyaÉ—a tare da cewa tashi muje asibitin.
Cikin sauri ta tashi tsaye Cox ta ƙosa ta Gakanta a gaban Dr Fahad.
Sai Mun dawo Hajiya Dady ya faÉ—a yana kallon Ammi.
Murmushi Ammi tayi tare da cewa Allah ya tsare hanya.
Ameen ameen.

Zaune suke a office É—in Dr Fahad, Bayan sun gaisane yafara musu bayani yana duba takardun suke gabansa.

Shakka Babu ban taɓa cikin karo da case ɗin Rashin lafiya irin wannan ba.
Akwai ruÉ—ani sosai a cikin wannan lamarin.
Jiya da Misalin 1am Ina gida a kwance masu kula da wannan mutumen suka kira hankali tashe suke faÉ—amin cewa wai ya farka Sai jifa yake da kaya ya hargitsa Kumi da yake a É—akin.

Cikin sauri nazo asibitin natarar da abunda suka faɗa tabbas hakane, Kuma daga an buɗe ƙofa sai yadaina Abunda yakeyi yasamu guri ya tsaya cak kamar wani Robert.

Hakan tasa nakira Wani abokina Dr Bilal Shi kwarraren likitan brain ne.
A Daren muka tafi dashi asibitin su Dr Bilal suka sake Shiga dashi É—akin na'ura suka Duba Shi.
Amma Kuma kinsan menene Babban abun ban mamakin?

Kai ta girgiza alamar a'a.

Brain ɗinsa lafiya Lau take tamkar taki, tawa, Dama ta sauran mutane Dr ya faɗa yana kallon Shabana da taƙuresa da Ido tana kallonsa tun lokacin da yafara Magana.

Sunkuyar da Kanta tayi ƙasa tama rasa mai zatace..........✍️✍️✍️

Nabeela Binji ce💃💃💃

More comment
More taping 😉😉

Share Fisabilillah 🙏.
Chapter 15 · 0% Book details