← Book details Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 15

Sashe 3

Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin mamaki ya Kalle ta yau Shuwa da Fadin sunansa ba kunya ko Kara? Abunda Bai tabaji ba Kenan a tsawon rayuwar sa da ita, murmushi yayi yace lallai kuwa kin Isa Shuwa Kuma Nagode sosai da tsayayya.

Zagayeta yayi da nufin fita daga ɗakin tayi saurin riƙo rigarsa tana cewa Ina Zaka tafi kabar mu a cikin DUHU? tabbass bazaka fita daga ɗakin Nan ba har Sai ka.... Wani wawan Mari taji a kumatun Wanda ya razana ta tare da yin baya kamar zata Faɗi.

Dasauri Shadow yatare ta tafaɗa jikinsa ya rungeme ta ajikin sa Yana Jin Wani irin baƙin ciki Wanda tun zuwansa Duniya Bai taɓa cin karo da makamancinsa ba.
Idonsa yadÉ—ago wa Æ´anda sukayi ja kamar garwashi ya zubasu akan fuskar mahaifinsa,
Wanda izuwa yanzu ya kejin baya ma ƙaunar ganinsa gabaki ɗaya,
Tabbass da a ce ba mahaifinsa bane yataɓa masa Ayiya da ko waye sai ya ɗanɗana kuɗarsa. hannunta yakama yakaita bakin gado ya zaunar da ita.

Shikuwa Abba ficewa yayi daga É—akin
Ransa a matuƙar ɓace.

Shadow Juyawa yayi ya kalli Al ƙaseem cikin murya wace take nuna tsantsan damuwa yace karka kuskura ka musawa Abba akan duk wani abunda kaga zai aikita, kuma karka kuskura sakin Noor idan dai bashine yayi maka umarni da hakan ba.

Buɗe baki yayi da nufin magana Shadow ya ɗaga masa hannu yace bana son jin komai daga bakin ka dan Allah Ƙaseem.
juyawa Ƙaseem yayi fuuuuh yabar ɗakin kamar zai tashi sama saboda tsananin ɓacin rai.

Gurin Ayiya ya nufa wace take zaune tun É—azu a inda ya ajiye ta kamar wata butun butumi.
Zubewa yayi ƙasa akan gwiwoyinsa ya kamu hannayen ta yace Ayiya dan Allah ki saurari abunda zan faɗa miki, kar kiyi wani abu wanda zaisa mutanen da ke gidan nan susan Halinda muke ciki.
koma menene kibari har mutane su watse dan Allah Ayiya yafaÉ—a tare da matse hannayen ta sosai acikin nasa.

Zare hannayenta tayi cikin nasa cikin ɓacin rai tafara magana. Ahanaf bazan taɓa lamuntar wanan abunba, wannan zalincin yayi yawa ko da ace ba akan ƴaƴana wannan abun yafaru ba to ni nan mai iya tsayama koma waye ne dan ganin yasamu adalci. bare akan yarana.
Ahanaf saidai kayi haƙuri a wannan ƙaron bazanja bakina nayi shuru ba wallahi, kuma kaji na rantse.

Kansa yadafe tare da furta ya Allah wannan wace kalar jarabawa ce ya Ubangiji ina neman afuwarka ka sassauta mana wannan lamarin, wannan Rana ce dana ci buri akanta najima ina tsumayin zuwanta da muradin ganinta.
dana san haka zata kasance dani da na roƙi Allah karma ya nunamin wannan BAƘAR RANAR.
Yaƙarisa maganar cikin matsanan cin kuka tare da ɗaura kansa akan ƙafafun Ayiya, bayansa ta dinga bugawa a hankali cikin sigar rarrashi.

A gidansu Noor kuwa tuni labari ya riski mahaifiyar ta najin saɓanin da aka samu gurin ɗaurin auren. cikin tashin hankali ta miƙe tsaye tare da cewa wllhy bazai yuyu ba wannan ai hauka ne ma.

Nabeela Binji ce💃💃💃

Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610

More comment
More taping 😉😉

Share Fisabilillah 🙏🙏🙏.

♣️DUHUN INUWA♣️

STORY

AND

WRITING ✍️✍️✍️

BY

NABILA S BINJI

PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM

Page

0️⃣3️⃣

Wannan abun ba zai taɓa faruwa ba Wallahi. saboda ko a lokacin mullkin mallaka ban taɓa jin irin wannan zalincin ba.
Kallonta tamaida kan Yassar wanda ya kasance yaya ne a gurin Norr kuma shine wanda ya kawo mata wannan baƙin labarin
Saboda a gaban idonsa kumai yafaru ba labari aka basa ba.
Tace "Yassar ka tabbata Maganar da ka faɗa min gaskiya ce kuwa? saboda muddin na bin cika nagane ba gaskiya bane tohm fa kasani ranka sai yafi nawa ɓaci wllhy"
Ta faÉ—a ba alamar wasa a tattare da ita.

Cikin son tabbatar mata da gaskiyar Al'amarin Yassar "yace wllhy Mommy ba ƙarya nake faɗa miki ba, Har fa suma Ahanaf yayi agurin ɗaurin auren sakamakon jin da yayi an ɗaura auren Noor da Al ƙaseem.
Nan fa Yassar ya kwashe duk abunda yafaru agurin É—aurin auren ya faÉ—a mata cikin nutsuwa"

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un ita ce Kalmar da Mommy tayi ta nanatawa, cikin kiÉ—ima da tashin hankali Mommy ta nufi hanyar fita daga É—akin.

Cikin zafin nama Yassar ya Kama hannunta yace "Mommy Ina zakije haka? Dan Allah Kar kice zakiyi Wani Abu a cikin wannan Taron, saboda Hakan ba ƙaramar matsala zai jawo ba" Yassar ya fada cikin sigar rarrashi.

"Yassar kasakar min hannu Idan ba so kake Na Ɓata Maka Rai ba yanzu"

Mommy Dan Allah "ki tsaya kiyi tunani kafin ki yanke hukunci saboda yanke hukunci cikin fushi ba Abunda yake janyowa Sai nadama Mai matuƙar muni" Yassar yafaɗa cikin marairaice fuska.

Wane hukunci Zan yanke Yassar? Ai Ni bani da abun cewa yanzu har Sai naji gaskiyar Magana agurin Dadyn Ku da Kuma dalilin yanke wannan danyen hukuncin" sannan nasan wane mataki yakamata NaÉ—auka.

Sakin hannun nata yayi.

Jiki ba ƙwari tabar ɗakin .

Shima Yassar mara Mata baya yayi cike da jimamin wannan abun, Dan shi Allah yasani ba Wanda yake tausayi kamar Shadow. ganin halin da yashiga dazu yayi matuƙar daga Masa hankali sosai,

Wane hali Norr zata Shiga Idan taji wannan abun? Gaskiya su Dady Basu kyauta ba kwata kwata. Ai da wannan abun da sukayi gwarama ace fasa ɗaura auren sukayi gabaki ɗaya zaifi sauƙi sosai akan wannan abun da suka aikata.

Ko wannen su da Abunda yake tunani a ransa a haka har suka karasa part din Dady.
Yassar yaja yatsaya yace "Mommy Dan Allah kibi komai a hankali, har muji menene dalilinsu Na aikata haka,
"Duk abunda kwanciyar hankali beyi ba tohm fa tashin hankali ba Zai taɓa yinsa ba"

To Insha Allah zansan ta yadda zan Ɓullowa lamarin, Zaka iya tafiya Allah yayi Maka Albarka.
Ajiyar zuciya Yassar ya sauke tare da cewa ameen ya Allah, Nagode sosai Mommy.

Juyawa Yassar ya Tafiyar sa.
ita Kuma Mommy ta Shiga palon bakinta dauke da sallama,

Dady ta hango tsaye agaban TV Yana kokarin canza channel. "sallamar da tayi ya amsa hankalinsa Yana Kan TV karasawa cikin palon tayi, ta zauna a Kan É—aya daga cikin kujerun falon tare da cewa Ashe ma kana ciki ya gajiya.
Alhmdllh ya amsa fuskar sa dauke da murmushi.

Ya jama'ah dafatan kumai dai lafiya Ko? Ya tambaye ta cikin kulawa.

Zamanta ta gayara tare da sauke ajiyar zuciya tace Ina fa lafiya Alhj? Yanzu nake Jin Abunda yafaru agurin ɗaurin aure Nan shine nace Bari nazo naji daga bakinka, saboda kasan ba a ɗaukar maganar Yara a haukai a zauna ba tare da ƙwaƙwaran bincike ba.

Alhj Shin da gaske Abunda naji yafuru gaskiya ne Ko kuwa shatifaÉ—i ne?

Ta kuwa yayi a hankali har ya Isa gurin da take zaune Shima ya zauna tare da Kama hannayenta yafara Magana, "Eh Abunda kikaji gaskiya ne ba shatifaɗi ba. mun ɗaura auren Al ƙaseem da Noriya Maimakon ita da Ahanaf"

Gaban ta ne ya FaÉ—i sosai, Sai kuma ta danne cikin sanyin murya tace tohm Alh Ko Zan iya sanin dalilin haka?

Murmushi yayi tare da murza hannayenta yace wannan ba hurumin ki bane ba Hjy.
Ni yanzu Abunda nake so da ke shine kije kisami Noor ki Gaya Mata Abunda yake faruwa Kuma ki fahimtar da ita falalar yiwa iyaye biyayya akan duk Wani hukunci da suka yanke akan yaransu Idan har ba saɓon Allah bane.

Cikin sauri ta kwace hannuwan ta a cikin nasa tace Wai da gaske kake kun daura auren Norr da Al kaseem? Kuma har kake tunanin ni naje nasami Norr Na faɗa Mata wannan maganar? Wllhy wannan abun bazai taɓa Saɓowa ba.
Alh niba Zan faÉ—awa Norr wannan lamarin ba saboda Ina matukar sonta Kuma Ina son farin cikin ta sanin kan kane Norr Tana son Ahanaf Kuma so Bana Wasa ba,
Har Takai Ga Bata iya Ɓoye wannan abun agurin kowa, Hatta Kai da kake mahaifin ta kasan haka.
Batare da kayi tunanin halinda Ƴarka zata fada ba ka yanke wannan mummun hukuncin.
Kuma abun baƙin cikin Wai bama fasaaura auren kukayi ba Sai kuka ɗaura da ƙanensa.
Ina zakuje da hakkin Yaran Nan Alh? Ai Haihuwa ba hauka bace,
bafa Dan kun haife su bane Zai baku Damar aikata duk Abunda kuka Ga dama a kansu ba.

Allah da kansa a cikin Al Ƙur'ani Mai Girma Yana cewa ƴaƴayenku da matayenku ababen kiyone agareku, kuma zamu tambaye ko wannanne ku akan abinda muka baku kiyo.
Kenan kaga Ko tsakanin iyaye da yaransu akwai hisabi ranar gobe ƙiyama.

Alh "yakamata kuyi gaggawar canza wannan ba hagon tunanin naku tun kuna da sauran lokaci, saboda har yanzu kuna da Damar gyara kuskuren da kuka TAF KA tun lokaci Baiƙure muku ba.

Ya'isa haka Dan Allah, Dady yafada tare da ɗaga Mata hannu, cikin matsancin fushi wanda tunda take Bata taɓa ganin yayi irinsa ba yace "Haj Ina Dai ce Norr ƴata ce Ko? Kuma Ina da hakki akan nasakata ko Kuma Na hanata, tohm Dan Allah Ina roƙonki da kija bakinki kiyi shiru akan wannan abun Kar ki tunzurani nayi Abunda bakya tunani" yafaɗa a hasale tare da ciro waya daga aljihunsa ya Danna Kira.

Amaryar Shadow wannan wanka haka kin ganki kuwa? Wallahi kamar mutum ya saceki ya gudu dake tsabar kyau "cewar Meenal datake ta faman yiwa Norr picture's "ni ce Nan zan turawa Shadow su saboda abani kyakyawan Goro taƙarisa maganar tana dariya.

Murmushi Norr tayi tare da cewa kanki akeji Kuma, Ni Kam nagaji da wannan ɗauke ɗauken naki da yaƙi ƙarewa tun dazu kike Abu ɗaya Dan Allah kibarshi haka Mana, nasamu nakira my Shadow naji muryar sa Ko zanji sanyi a Rai.. ringtone ɗin wayar tane ya hanata ƙarasa maganar da ta fara. hannu tasa takarɓi wayar daga hannu Meenal, tare da cewa Ɗan Halak kamar kasan yanzu nake Shirin kiranka.
Chapter 3 · 0% Book details