← Book details Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 15

Sashe 8

Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akan kujera Ayiya ta zauna fuskarta ba yabo ba fallasa,
Haidar da Kamal kuma a ƙasa suka zauna gefen Ayiya.
Shuru ne yaratsa palon ba Abunda kakeji Sai ƙarar tv.
Malamai Idan har bakuda Abun faÉ—a zaku iya Tafiya Dan Allah, saboda a halin yanzu nafi son Na zauna nikaÉ—ai, Abba yafaÉ—a idanunsu Akan tv kamar badasu yake Magana ba.
Ayiya zatayi Magana Haidar ya girgiza Mata ka Alamar Dan Allah tayi shuru kawar da Kanta tayi gefe batare da tace ƙalaba.

Gyara Zama Haidar yayi cikin nutsuwa ya Fara faÉ—awa su Abba duk Abunda ya faru tun bayan kulle Shadow da sukayi ajiya da dare, da Kuma dubawar da sukayi Basu ganshi ba bayan sun dawo masallaci.

Wata Matsananciyar faɗuwar gaba Abba yaji cikin tashin hankali ya dubi Haidar Wanda kansa yake a ƙasa,
Har zaiyi Magana Sai kuma yafasa ya dafe kansa da yake matuƙar Sara Masa Kamar ana buga Masa guduma.
Nan take Kuma Sai yaƙara jin duk Duniya ba Wanda ya tsana Sama da Ahanaf.

Ga Kuma kukan Ayiya da yake taɓa Masa zuciya,
Yama Rasa Abunda yake Masa DaÉ—i a duniya.
cikin ƙaraji yace YA ISA YA ISA da wanne kuke so Naji ne? Ko su kuke Sai kun haukatani?

Dan Allah Ku Tashi kubani guri Abba yafaɗa Yana nuna Haidar da Kamal a ƙufule,
Tashi sukayi suka fita fuuuuuuu Kamar zasu Tashi Sama,
Ita ma Ayiya Tashi tayi da nufin bin bayansu cikin sauri Abba ya riƙe Mata hannu yace "Ina Kuma zakije Haj?

Kasakar min hannu Alh,
Ka damu dani ne bare Har ka damu da gurin da zanje? Zan tafi Nemo yarona ne Kuma kasani muddin nasaka ƙafa Na bar gidan Nan naje Nemo Ahanaf Toh Koda Na ganshi bazan dawo gidanka ba Har Abada.
Cikin sauri Abba ya rufe Mata baki yace haba Dan Allah me kike faÉ—a ne haka? Kamar bakya cikin hankalinki, Yaron Nan ki rabu dashi duk Inda yaje Shi da kansa zai dawo gida, kituna ba fa kurar sa mukayi ba, shida kansa yabar gidan Nan, Dan haka Shi da kansa zai dawo.
Girgiza Kai Ayiya tayi tace Wai bakaji Abunda su Haidar suka faÉ—a bane?
Haj Kira bu da zance "wa Æ´an can Shashashun yaran duk halinsu É—aya dashi Ahanaf É—in.
Abun da suke faÉ—a ba gaskiya bane.

Kwace hannuwan ta tayi tare da cewa Idan Kai baka yarda Da Abunda sukace ba to Ni na yarda, Dan haka zanje neman Ahanaf yanzu ba Sai anjima ba, Ayiya ta faɗa ranta a ɓace tare da nufar hanyar fita daga palon.

Ba da yawuna ba muddin Kika fita daga gidan tohm tabbas kisani Akan tsinuwar mala'iku Zaki fita, indai Ni Muhammad Imran nine mijinki Toh ban lamunce Miki kije neman wannan Yaron ba, Yana gama faÉ—ar Hakan ya nufi hanyar bedroom É—insa ba tare da yajira yaji Abunda zata ce ba.

Haidar Bai fa kamata muyi haka ba gaskiya, Idan har mukayi haka mu ba abokanan kirki bane, abokin kirki shine Mai tsayawa abokin sa a cikin wuya Ko Daɗi, Kaine kafaɗi haka. Yanzu Kuma Zaka ƙaryata kanka. Kamal yafaɗa Yana kallon Haidar Wanda Sai faman saka kayansa yake a cikin jaka Rai a ɓace.
Kaga Kuma Abbu zaizo anjima Idan yazo betarar damu bafa? "A yadda Abba yatsane mu ma zai iya cewa da sanin mu Shadow yafita daga gidan nan" Kaga bamuda ruwan wanke Kan mu, Haidar idan hankali ya gushe hankali ake sakawa gurin Nemo sa, ya kamata kayi tunani kafin ka yanke hukunci. Cewar Kamal Yana marairaice fuska.

Wani irin iska Mai zafi Haidar ya furzar tare da cewa wllhy Abba yaci Albarkacin furfurar da Ke É—auke a fuskarsa da Kuma mutunci haihuwar Shadow da yayi da Sai Na Masa Rashin mutunci da Ko Sunana yaji an Kira Sai gabansa yafaÉ—i, Amma kashh ba damar haka.

Zan tsaya Har Abbu yazo muyi Magana dashi baki da baki in yaso daga Nan Sai Sai mu tafi abun mu, Shadow Dai shine abokin mu Kuma Zamu cigaba da neman sa tare da yi Masa addu'ar neman tsarin Allah a duk Inda yake.

Murmushi Kamal yayi yace Hakan ma yayi Boss dan wallhi Nima Bana son Zama a gidan Nan, gabaki É—aya lamarin gidan tsoro yake Bani,
gidan da Ada Idan kazo ko kai waye Sai rayuwar iyalin ta Burge ka,
Saboda soyayya da shakuwa da take a tsakaninsu.
Amma yanzu gidan ya Koma Kamar gidan wasu enemies. Allah ya tona asirin duk Wanda yake da hannu a cikin wannan lamarin.

Ameen ya Allah cewar Haidar Yana jingi jikinsa da Bango.

Misalin ƙarfe 20:15 Na Rana Abbu ne zaune a katafaren palon Abba fuskarsa a turnuƙe Kamar Wanda aka aikowa da Mala'ikan mutuwa,
Cikin ɗaure fuska Abbu yace Muhammad Ina So kafaɗa min Menene dalinlin da yasa ka ɗaura auren waccan yarinyar da Ƙaseem maimakon Ahanaf?

Cikin rawar murya Abba yace Amma Yaya Ai da Kabari ka huta kaci abinci tukkunna.
Ɗaga Masa hannu Abbu yayi tare da cewa Ai Na huta 1 da Yan mitina muka sauka ƙasar Nan Toh Ina ga ba Wani hutu da nake buƙa yanzu.

Kabani amsata shine Kawai Abunda nake buƙata,
Menene dalilin aikata duk wannan Abun Muhammad? Abbu yafaɗa Yana ƙure Abba da idanunsa da suka Fara sauya Kala zuwa ja tsabar ɓacin Rai............✍️✍️✍️

Yanzu ma a kafara😥😥

Duk fa abun Nan da Abbu yakeyi be San cewa Ahanaf baya gida ba.

Me zai faru Idan Abbu yasan yasan Ahanaf baya gida?

Nabeela Binji ce💃💃💃

Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610

More comment
More taping 😉😉

Share Fisabilillah 🙏.

♣️DUHUN INUWA ♣️

TAPING......📲📲📲

STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI

PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM

Allahumma salli 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama sallayta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed, allahumma barik 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama barakta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed.

Allahumma a'innee 'ala zikrik, washukrik, wahusni ibadatik.
Allahumma innee as-alukal-jannah, wa-a'u'zu bika minan-nar.🤲

PAGE

0️⃣8️⃣

____________kayi haƙuri Yaya wallahi nima bansan dalilin da yasa n...... tasss Abba yaji saukar mari akan kumatunsa, hannunsa yasa ya dafe gurin da Abbu ya mare sa,
É—ago yayi yana kallon Abbu cike da mamaki.
"Kana da hankali Muhammad kasan abunda ka keyi kuwa? ka aikata wannan gagarumin laifin sannan harka iya buɗe baki ka faɗamin cewa bawani dalili? kar kazama Maha'inci Muhammad katuna fa Ahanaf amana ne agurinka Alƙawari kayi zaka kula da shi, zaka bashi farin ciki zaka mantar dashi ƙuncin rayuwa zaka zamar masa Garkuwa.
Ina duk wannan Al'washin naka yake? Ashe dama bada gaske kake ba? Ashe dama raÉ—aÉ—in mutuwane yasa kafurta duk waÉ—an nan abubuwan? Mai yasa kake so kazamar ma Ahanaf DUHUN INUWA Muhammad?

Wani matsanan cin kuka Abba ya fashe dashi wanda shida kansa bai san dalilin yin saba,
Saidai yasan duk abunda yayansa yafaɗa gaskiya ne Ahanaf amana ne agurin sa kuma abun so da ƙauna agurinsa, amma yarasa taya akayi hakan tafaru.

Agaban Abbu Abba ya zube akan gwiwoyinsa, yace "ka yanke duk hukincin da kaga yayi maka a kaina yaya" ni mai laifine agurin ka.
Amma fa kasani har yanzu ina kan bakata bazan warware auren Norr da Al ƙaseem ba.
"Ahanaf ya kasa yimin biyayya kamar yadda É—an uwansa yayi,
Ya nuna min cewa shi yaro ne mai taurin kai ba wanda ya isa dashi" yaya bari kaji daga yau na fitar da hannu acikin duk wani lamari na rayuwar Ahanaf yaje yayi duk abunda yaga dama bani bashi" Abba ya faÉ—a cikin É—acin rai.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, Muhammad yau Kaine kake wannan furucin Akan Ahanaf? Kuma har kake haɗa masa da ƙarya da ƙage? Tabbas da wata a ƙasa wannan abun bayin kanka bane.
Ni bawani hukunci da zan yanke ma wanda ke fama da Matsalar taɓin kwakwalwa,
Amma kasani daga yau Ahanaf zai bar hannunka ya dawo ƙarƙashin kulawata.
Sanna zan tayaka da addu'a kuma zan sanya manyan malamai su taimaka mana da addu'a, saboda bazan zuba ido ina kallon ka cikin wannan halin ba.

Muhammad kai Amana ce agurina zanyi kumai dan ganin na kiyaye wannan amanar da iyayenmu suka bani.
Bana so koda da kan a kaifane Allah yakama ni da Hakkinka agobe ƙiyama, zan tsaya tsayin daka akanka da kuma iyalanka dukanku hakkine da ya rataya a wuyana.

Har yau bazan manta mutuwar mahaifiyar muba bazan manta yadda ta dankamin amanar ka a hannuna ba Muhammad,
duk duniya banida wani É—an uwa sama dakai, kaima bakada wani É—an uwa sama dani mu biyun nan mune kawai dangin juna bamuda kowa face Allah. Muhammad katuna yadda mukayi fafutuka da rayuwa kafin muzo wannan matsayin.
Munyi fama da rayuwa
Munyi fama da maraici
Maunyi fama da rashin gata, uwa uba Munyi fama da ƙuncin talauci da rashin majingina.
Amma duk da haka baisa munguji juna ba kuma baisa muka yada zumunci ba baisa nakasa riƙe amanar kaba Muhammad.
Kuma kasani har yanzu bazan karya alƙwari ba. ni bakamar kai bane Muhammad kuma kasani bana fatan zama kamar kai har abada.
Abbu yana gama faɗar haka ya miƙe tsaye da nufin barin palon saboda ransa yakai ƙololuwar ɓaci akan wannan lamarin na ƙanensa.

Cikin sauri Abba ya bi bayansa tare da rungume shi ta baya yana kuka, yace "dan Allah ka gafarceni yaya wallahi ni kaina bansan dalilin akaita wannan abun ba.
Yaya taɓa kirjina kaji bugawa yake da sauri. Hannun Abbu yakama yaɗaura a saitin zuciyar sa.
Da sauri Abbu yajanye hannusa tare da furta Muhammad kashe kanka zakayi kaji yadda zuciyar ka ke bugawa da sauri? Mai yasa kake son kashe kanka ne? wannan abun duk fa kaine ka aikata shi.
Ni fa gaskia kawai na faÉ—a maka.

Wallahi Narasa dalilin da yasa nayi haka yaya, "dan Allah karka gujeni wallhi idan katafi kabarni mutuwa zanyi kaine Babana kaine mamana kuma kaine yaya na banida kowa sama da kai dan Allah kar katafi" Abba yafaɗa yana ƙara rungume Abbu ajikinsa tare da ƙara sautin kukansa kamar wani ƙaramin yaro.
Chapter 8 · 0% Book details