← Book details Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 15

Sashe 12

Duhun Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shadow Yana Gama Zana Shabana ya juya Yana kallonta Yana jiran ta sallame sa, ita hankalinta Baya ma kansa kwata² Zanen Kanta Kawai take kallo,. Sai Daga Baya ta Maida hankalinta Kan Shadow tana murmushi tace "bawan Allah ya sunanka?"
Kawar da kansa yayi gefe batare da yace Mata ƙala ba,
Sake maimaita tambayar tayi Nan ma dai Shiru Shadow yaƙi yayi Magana.
Kodai Baya Magana ne cewar Hafeeza Tana kallon Shadow.
Bai kallesu ba Kuma Bai tan kasu ba.
Jakar hannunta Shabana ta buÉ—e ta É—auko kuÉ—i masu yawa tabama Shadow tace gashi Malam.
KuÉ—in ya Kalla ya É—auke kansa alamar Baya so.
Wasu kuɗin taƙara Akan na farko ta bashi Nan ma yaƙi karɓa.
Shabana batan San cewa "Shadow ba kuÉ—i yake So ba Shi Abinda yaci yake nema, tunda ya fahimci Idan ya zana mutum Akan É—auki abinci a bashi,
Sai ya Maida hakan Kamar sana'a duk lkcn da yaji yunwa yakan Zana duk Wanda yake kusa da Shi, Idan ka bashi Abinci ya karɓa yaci Idan ka bashi kuɗi Kuma Sai ya Tafiyar sa.
Yanzu ma Hakan ce tafaru dan fafir Shadow yaƙi ya karɓi kuɗin da Shabana ta bashi.

Tohm Shi wannan me yake so Kenan? Cewar Shabana Tana kallon Hafeeza.
Oho Kuma kinga yaƙi Magana balle musan Abunda yake so.

Tafiya Shadow ya Farayi Yana Sosa kansa da yasha datti Yana Masa ƙaiƙayi.
Bayansa Shabana tabi Tana faÉ—in
bawan Allah mekake so ne? Ko kulata Shadow baiyi ba ya tsallaka titi ya tafi Abunsa.
Tsayawa tayi tana kallonsa har ya ɓacema ganinta juyawa tayi ta Kuma Gurin Hafeeza jikinta ba ƙwari.
Sai ɗaukar hoton Zanen Hafeeza keyi, kallon fuskar Shabana tayi taga ba ɗigon walwala a tare da ita, Hafeeza tace dan Allah kizo kusa da Zanen Nan Na ɗauki hoton yadda Zan ƙara kafa shaida da kayan jikinki tunda Har su ya Zana.
Ba musu Shabana ta matsa kusa da Zanen Hafeeza tayi Mata hotona masu kyau.

Tafe suke cikin Mota Hafeeza ta kalli Shabana tace "Kai Wallahi Mahaukacin Nan fa ya kwashi gayya kinga fa kusan mutane 27 ne su kace Suna Son wannan Mai Zanen ya Zanasu"
Murmushi Kawai Shabana tayi batare da tace wa Hafeeza ƙalaba.

_________Bayan sati É—aya
A kullum Shabana Sai tayi tunanin wannan Mahaukacin da Ko sunansa batasani ba, haka Kawai takejin Tana son sake haÉ—uwa dashi.
Taje gidan Man da tafara ganinsa yafi a ƙirga Amma Bata sake ganin Ko Mai kama dashi ba.
Takan tsaya Gurin da Zanen yake ta ƙura Masa Ido Kamar wacce Bata taɓa ganinsa ba.
Har masu aiki gidan Man sun Saba da ganin Shabana, saboda Idan tazo takan kwashe kusan sa'a É—aya agurin Tana jira taga ko wannan Mahaukacin zaizo
Idan tagaji da tsayuwa Sai ta buÉ—e Mota ta zauna.
Amma Haka zata ƙaraci zamanta ba Shadow ba alamar sa.

Cikin firgici Shabana ta tashi zaune Kan makeken gadonta, tana furta Kalmar Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un,
Hannayenta tasa ta dafe Kanta da yake matuƙar Sara Mata tamkar Zai tsage gida biyu.

Runtse idonta tayi tare da cewa
Oh! Allah Gani gareka,
"wannan wane kalar Mahaukaci ne? Kodai da Aljani nayi gamo ne?"
Tun lkcn da nayi tozali dashi nakasa samun sukuni,
kullum Sai Na tunashi yafi a ƙirga na Rasa dalilin da yasa nakasa mantawa dashi.
A hankali tafara buÉ—e idanunta da suke cike da tsantsar damuwa tafara sau kowa daga kan gadon.
Kai tsaye toilet ta nufa,
bajimawa ta fito kaya tasaka ta É—auki car key É—inta tafita cikin sauri.
Wani ɗaki ta nufa Tura ƙofar tayi bakinta ɗauke da sallama.

Matar dake tsaye Tana waya ce ta amsa sallamar Tana bin Shabana da kallon tuhuma.
Dagani Babu tambaya wannan farar dattijuwar mahaifiyar Shabana ce Cox Suna masifar Kama da Juna.
Bayan ta gama ne ta sauke wayar daga kunnenta tare da
Cewa "Sai Ina Kuma? Keda Kika ce kanki na Miki ciwo sosai"
Tafaɗa tana ƙure Shabana da manyan idanunta Dan talura yarinyar Tata tafara sauya halayenta.
Duk Wanda yasan Shabana yasan rigimammiya ce ta ƙarshe,
but yanzu tazama wata silent kamar ba ita ba.

Kanta taÉ—an Sosa tare da cewa gidansu Hafeeza zanje Ammi.
Bazakije ba cewar Ammi tana É—aure fuskarta,
Kusa da ita Shabana ta matsa tare da rungumeta ajikinta cikin shagwaɓa tace Dan Allah kiyi haƙuri Ammi kibarni naje akwai Abunda zamuyi ne.
Harara Ammi ta ɓalla Mata Ai kullum zan cen ki kenan,
Kifita daga idona Na rufe Shabana Naga kina so ki ɓaci da yawo yanzu Wanda da ba halinki bane.
Kije Allah ya tsare Amma Dan Allah Karki yadda mahaifinki ya dawo gida baki dawo ba.
Kinfi kowa sanin halinsa Idan yafara faÉ—a kamar Zai tayar da gari Ammi tafaÉ—a tana Dariya.
Ita ma Shabana dariyar tayi tare da cewa insha Allah Zan dawo da wuri Ammi.
Tohm Allah ya yadda
Ameen ya Allah.
Har ta buɗe ƙofar zata fita tajuya tana kallon Ammin taɗan marairaice fuska tace bakimin Addu'a bafa Ammi.
Murmushi Ammi tayi tare da cewa Allah ga Æ´ata zata fita, yadda tabar gida lafiya ya Rabi ka mayar min da ita lafiya, Allah kayi Mata Albarka Kuma ka tsareta da sharrin mutum ko aljan.
Wata sassanyar ajiyar zuciya Shabana tasaki tare da furta Ameen ya Rab Ammina tana murmushi.

Fita tayi daga gidan ranta fari ƙal ba yaune mahaifiyarta ta Saba yi Mata Addu'a ba
Amma Sai taji tafi Jin daÉ—in ta Yau fiya da ta kullum.
Duk lokacin da zata fita Sai Ammi ta mata Addu'a sannan take tafiya tun tanada ƙurciya take wannan halin nata shiyasa Ammi ke matuƙar ƙaunarta.

Kai tsaye gidansu Hafeeza tanufa a Palo ta Tarar da ita zaune tana cin Abinci.
Wata uwar harara Shabana ta ɓalla mata tare da cewa acici mala'ikun tukunya.
Dariya Hafeeza zayi tare da cewa oh ni Hafeeza naga ta kaina
da ace ke kike ciyar Dani da na Boni Kenan.
Ba halin kiganni Ina cin Abinci Sai kin min gori?
tohm Bismillah zo kema kici Hafeeza ta faÉ—a Tana murmushi.
Ya mutsa fuska Shabana tayi sannan tace ke Malama ni ba wannanne ya kawoni ba zuwa nayi ki rakani gidan Mai plz.

Cike da mamaki Hafeeza ke kallonta tare da cewa ba kince bazaki Koma neman Sa ba?
Kirufawa kanki Asiri Shabana maybe fa wannan Mahaukacin ba mutum bane tun fa wannan lokacin bamu ƙara ganinsa ba har Yau.

Kusa da ita Shabana ta zauna tare da sauke ajiyar zuciya tace "Naso matuƙa na manta da wannan Mahaukacin amma nakasa Hafeeza kullum lamarinsa ƙara girma yake a cikin zuciya ta, Hafeeza bansan wannan Mahaukacin ba hasali ma Gani ɗaya na taɓa Masa a rayuwata. Amma narasa dalilin da yasa nakasa mantawa dashi nakasa manta fuskarsa nakasa manta kallon da naga Yana mun"
Hafeeza kallon da yake min kallone Wanda yake É—auke da abubuwa da dama
Neman taimako neman tausayawa
Amma nakasa taimakon sa Cox ban san Abunda yake so ba bansan menene a cikin zuciyar sa ba Amma tabbas a wannan lokacin akwai Abunda yake so agurina Kuma nakasa sanin Menene"
Hafeeza intaƙaice miki zance yanzu ma daga bacci na tashi Kuma nayi mafarkin wannan "Mahaukacin still irin wannan kallon Naga yana min kamar Koda yaushe Idan nayi mafarkinsa" tafaɗa tana goge guntun hawayen da ya taru a gefen idanunta.

Tohm yanzu ya kikeso ayi Shabana? ta Ina zamu Sami wannan Mahaukacin? Sannan Idan Mun sameshi mai zaki masa ta Ina zaki taimakeshi? Hafeeza ta faɗa Tana ƙure Shabana da Ido.

Numfashi Shabana ta furzar tare da gyara Zamanta tace Nima kaina banida amsoshin waÉ—an nan tambayoyin naki Hafeeza, Abunda nasani kawai shine Ina son sake ganinsa.
Kallonta Hafeeza tayi ta girgiza Kai tace okay Bari nashiga na shirya Sai muje.
Murmushi Hafeeza tayi tace nagode Goty.
Harara Hafeeza ta ɓalla Mata tace eh Ai duk lokacin da kike son yaudara ta haka kike kirana da Wani Goty na cuta.
Gabaki É—ayansu dariya suka Saka.

Nifa gaskiya na Fara gajiya Shabana tun ƙarfe Nawa muke nan gurin Kamar wasu marasa mafaɗa
Muna zaman jiran Abunda ba tabbas.
Maybe fa Ina ga bawan Allah nan ba lafiya yake ba Hafeeza.
Idan baki Manta ba farkon ganin mu dashi irin lokacin ne
Kuma kullum irin wannan lokacin nake zuwa Nan nayi ta faman jira but Shiru.
Tsayuwa Hafeeza ta gyara tace to Kodai zamu tambayi masu Saida Man nan muji yaushe ne last É—in zuwansa nan.
Kai Shabana ta gyaÉ—a tabbas Abunda ya kamata muyi Kenan tun farko.

Gurin masu Saka Mai su kaje, Bayan sun gaisa ne Shabana ta tambayeshi Shadow.
Tana masa kwatance ya gane Wanda take nufi.
Jim yayi kaÉ—an sannan yace tabbas Na gane Shi Amma gaskiya ya kwana biyu baizo nan gurin ba Hajiya.
Hannunta ta dunƙule taɗan daki goshinta tace kashhhhhh!
Kuma dan Allah bakasan gurin da zan iya samun sa ba?
Kai ya girgiza yace gaskiya ban Sani ba Hajiya.
Godiya suka masa sannan suka Shiga Mota suka nufi hanyar gida.

Hanyar da sukabi É—azu ba ita Shabana tabi ba, wata hanyar tabi daban.
Kallonta Hafeeza tayi tace Madam ina zaki kaini ne? Kodai kema kin Sami taɓuwar hankali ne?
Ko kulata Shabana batayi ba taci gaba driving É—inta, dalilin da yasa Shabana ta canza hanya shine ganin Yamma tayi za'a iya samun cinkosun ababen Hawa.
Ta wata sabuwar unguwa suka biyo unguwar sit ba hayani.

Ke Dalla Malama kashe Mana wannan banzar waƙar Shabana tafaɗa tana hararar Hafeeza.
Bazan kashe ba
ba ruwanki da waƙata hausawa sunce Shan Koko buƙatar Rai dan haka ki barni da ra'ayina
Tohm Wallahi baki Isa ba Sai kin kasheta, Shabana ta faɗa Tana ƙoƙarin kwace wayar hannu Hafeeza, gabaki ɗaya hankalinta ya bar Kan driving ɗinda take ya Koma Kan Hafeeza.
Saiji tayi tabugi Abu kamar mutum da sauri ta take Burki kuuuuhhhhh tare da furta Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, cikin tashin hankali suka fito daga cikin Motar gabaki É—aya Shabana ta ruÉ—e jikinta har rawa yake tsabar ruÉ—ani,
Cikin kuka tace na Shiga ukku Hafeeza nayi Kisan Kai Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un.
Riƙeta Hafeeza tayi tace kinutsu kidawo cikin hankalinki Shabana, nifa Gani nake kamar wannan Mahaukacin ne da kike nema......✍️✍️✍️

Nabeela Binji ce💃💃💃

More comment
More taping 😉😉

Share Fisabilillah 🙏

♣️DUHUN INUWA♣️

TAPING......📲📲

STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI
Chapter 12 · 0% Book details