← Book details Dr Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 20

Sashe 7

Dr Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana zuwa Bedroom ta sami Mima har ta fito daga wanka tana zaune kan stool tana kuka

Zuwa tayi gaban ta kafin a hankali ta É—afe kafadar ta
Ƙuƙa sosai Mima taƙe harda shashsheka tana girgiza kanta cikin kuka tace"Yaki kulaki ko? Nasani ai bazai kulaki ba yasan maye yayi"

"Shittt is okay sis kinji aiki yaƙe shiyasa amma zaizo ai" cewar Mary tana zama bakin bed tana kallon Mima

Murmushin baƙin ciki Mima tayi tana kallon Mary tace"Tunɗa na taso Abbeiy, Ammeiy basu taɓa ko da nuna Ni da yatsa ba balle suyi yunkurin marina ko duka amma shi Hero kullum kamar jaka haka ya ɗauke Ni ya ɗaƙe Ni ya sani punishment babu abinɗa bayayi min ɗuk da hakan saboda shiɗin yaya nane bana kulasa amma yau ya ɗaga hannu ya mareni haka? Maye nayi masa Mary? Maye na raga Masa da yaƙe nunan wannan tsana haka? Wllhy Mary na tsani Hero bana Son ganin sa na tsane saaaa" taja Maganan tana kara sautin kukan nata
Wani tari ne tazo mata mai ƙarfi har tana riƙe setting zuciyarta

Da sauri Mary ta miƙe ta ɗauko mata ruwa ta bata
Kin sha tayi tana tura hannun ta kafin ta miƙe ta shige Toilet taci gaba da yin tarin tana hawaye

Mary kuka taƙe tana tausaya wa ƴar uwar ta

Wanke fuskar ta tayi ta fito tana shashsheka
Wajan Wardrobe ta nufa tana zuwa ta buÉ—e ta É—auko doguwar riga mara nauyi tasa kafin ta haura kan bed ta Kwanta

Mary kallonta taƙe har ta Kwanta
Muryar ta taji tana faÉ—in"Sis Mary Anya su Ammeiy da Abbeiy ne suka haifan?"

Da sauri Mary tace"Why kiƙe faɗin irrin wannan Maganan? Sune suka haife mu ɗukan mu Uku"
Murmushi tayi bata kara ce komai ba har Bacci ya É—auke ta

Yana gama yin wayan bayan ya kashe kiran ya miƙe ya fice daga ɗakin a babban falon gidan ya zauna yana tunanin Maganan Hafsat
Tashi yayi ya fice , Parking space ya nufa yana zuwa ya faÉ—a cikin Motan sa nan ya fice daga gidan da gudu

Bai tsaya ko inaba sai gidan su Safwan, bayan yayi Parking ya fito dai dai kuma shima Safwan ɗin ya fito yana ƙoƙarin shiga cikin Mota ya hango Motan Zaif yayi Parking
Kallon sa Zaif yayi kafin ya isa inɗa yaƙe
Hannu suka haÉ—a suka gaisa kafin Zaif yace"U have a Time? Zamuyi mgn"
Murmushi Safwan yayi yace"Ok mu shiga ko"
Shiga ciki sukayi a falon Side É—insa suka zauna bayan ya kawo masu abin sha ya zauna yana kallon Zaif yace"ina sauraron ka Dr."
Numfashi Zaif yaja kana ya bawa Safwan ɗuk abinɗa yaƙe faruwa harda yaje wajan Hafsat ya faɗa masa kuma ya kara da cewa shi ba Son ta yaƙe ba itama haka
Numfashi Safwan yaja kana yace"Alhmdllhi gaskiya nida kaina bansan abinɗa zanyi ba Tunɗa naji labarin wai kai za a aurawa Hafsat na hakura amma yanzu kuma tunɗa kace Kaima ba son ta kaƙe ba yanzu maye abinyi Ni kuma inason abina"

Shiru Zaif yayi yana lumshe idonsa yana jin yadda zuciyarsa kya bugawa hannu yasa yana shafa zuciyan nasa cikin Cool Voice É—insa yace"Just go and tell for her parents you married her that is the only solution"

Waro ido Safwan yayi kana yace"Like how kana nufin Ni kadai a a no sai dai mutafi tare da kai da ita kaga daga nan zamu samu daman fada musu komai"

"Ok"yace kafin ya miƙe tsaye yana miƙa masa hannu suka fito a tare akan gobe zasu ya kira ita Hafsat ɗin ya sanar mata cewan Zaif

Karfe 3pm ya dawo gidan bayan yayi Parking ya fito yana ɗafe kirjinsa da taƙe ta bugawa

Da Sallama ya shigo falon
Ammeiy ce zaune tana shafa kan Mima daƙe Kwance kan cinyar ta tana fidda numfashi daƙer da jikinta ɗuk yaɗau zafi sai Mary da taƙe kusa da Ammeiy tana kallon Tv
Zama yayi kan kujera yana gaida Ammeiy
Kin karban gaisuwan tayi tana kallon sa cikin fushi tace"Ina ka ajiye wayan ka inata kiranka kaki dagawa"

Sunkuyar da kai yayi yace"Ammeiy wayan na barshi a nan gida kafin na fita"

"Yayi maka kyau" tace tana kai kallon ta kan Tv plasma daƙe falon

"Ammeiy lafiya ko?"

Tana hararan sa tace"karda kace min bakasan cewa Mima ba lafiya?"
Idonsa yakai kan kyakkyawar fuskarta wacce take kumbure gyafe duka biyu inÉ—a ya mare ta gashi yayi jazir yatsun sa sun fito raÉ—a raÉ—a
Zuciyan sa ne yabada sauti rass
"Kai naƙe tambaya fa Son"
Yana tsosa kyaya yace"a a Ammeiy amm ban sani bafa"
Mary kallonsa tayi
Harara ya dalla mata kafin ta É—auke kai

"Alright gashi yanzu dai tana zazzaɓi kayi Medicine ɗin ta daman dana jika shiru ne yasa na kirawo Abbeiy ɗin ku amma bai dawo ba Tunɗa kariga sa zuwa sai kayi mata injection"
"Ok"yace kafin ya miƙe ya nufi Side ɗinsa

Ammeiy tayar da Mima tayi daga nannauyin baccin wahalan da ya É—auke ta tace"Daughter jeki Son yayi Miki injection" Bata Musa ba ta Tashi ta nufi Side É—insa
Tana zuwa baya nan a falon hakan yasa ta shige Bedroom É—in sa
Tana zuwa ta sami shi zaune yana haÉ—a injection
Bata ce Komai ba ta zauna kan stool tana sunkuyar da kai ƙasa
Bayan ya gama haÉ—a wa ya kalleta kafin yace"Come"
Tashi tayi tsaye ta ɗan daga hannun rigar ta sama kafin ta duga gabansa ta miƙa masa hannun
Kallonta yayi yaga ta runtse Idanun ta tana sunkuyar da kanta

A hankali ya tsoka mata allurar
"Ashhhhhhh!!! Heroooo!!! Zafiii"
Tace tana riƙe hannun sa

Bayan ya cire allurar ya kamo hannun nata yajata zuwa jikinsa ya rungume ta sam a tare suka sauke nannauyin zajiyan zuciya
Mima lamo tayi a jikinsa, can kuma ta fashe da kuka tana girgiza masa kai cikin shashshekar kuka tace"Suwaye ne iyaye na?"

Da sauri Zaif ya É—ago yana kallon ta
Hannu tasa ta Share hawayen ta cikin ƙasa da Murya tace"Baka sona Ka tsaneni ɗuk kiyayyar da kaƙe nunan Why not baka nunawa Maryam ai itama daga muƙe kodai nice daman a cikin ku?"
Runtse Idanun sa yayi yana jin kansa na masa barazanar tarwatse wa idanun sa yayi ja

Ganin haka yasa ta ficewa daga dakin tana kuka ƙasa ƙasa

Tana fita babu kowa a falon zama tayi kan kujera tana shi gaba dayin Kukar ta

Tashi yayi ya fito falon nan a riske ta Zauna tana shashshekar kuka tana girgiza kai ga yadda idanun ta sun kumbura saboda kuka da tasha gashi fuskarta sunyi jazir

Wajan ta ya nufa yana zuwa ya zauna gyafen ta kafin ya sanya hannu yaja ta zuwa jikinsa yana share mata hawayen cikin rarrashi yace"Stop Cry Ok"
Sautin kukan nata ta kara tana faÉ—in"bakai bane"
"Ni kuma?"
GyaÉ—a masa kai tayi
"Maye nayi Ni kuma?"
Hannu tasa tana bugin kirjinsa tana mukan shagwaba
Murmushi yayi yace"to ai ƙece bakijin magana shiyasa kikaja na mare ki"
Kukan ta kara tana bubbuga kafa
Kansa yakai dai dain kunnen ta yace"Kina Son Ice Cream?"
GyaÉ—a Masa kai tayi
"Ok sai kinyi min Alƙawarin daga yau bazaki tsaya da wani saurayi ba ko hira kinji?"
Mamaki ne Yakamata amma ta daƙe ta share tace"To Hero nayi Alƙawari"
Murmushi yayi ya raÉ—a mata wani abu a kunnen ta
Dariya sukayi dukan su kafin kuma ya kara matseta a kirjinsa yana cusa kansa cikin wuyan sa

Abbeiy da tunɗa zun yaƙe tsaye yana musu kallon Mamaki, "lalle yaran nan dole gobe goben nan a ɗaura auran su insha Allahu" haka ya faɗa yasa gyara murya
Cikin sauri Zaif ya zame jikinsa daga na Mima yana tsosa kyaya
Abbeiy Murmushi yayi yana kallon Mima yace"Mamata bakida lafiya ohhh sorry"
Tashi tayi ta faÉ—a jikin sa tana hawaye tace" Abbeiy da sauki"
"Eh na kira Ammeiy ku tace wai kikace mata faÉ—uwa kikayi a Toilet garin yaya kuma?"
Zaif da sauri ya É—ago ya kalli Mima sai kuma yaga tana kallon Abbeiy tace"ina wanka sulbi ya É—auke Ni na faÉ—i Abbeiy"
Shafa kanta yayi yana kallon Zaif yace"anjima kazo Bedroom É—ina kasame ni"
"To Abbeiy"yace yana É—ukar da kai

Abbeiy barin falon yayi ya haura Bedroom

Kallonta Zaif yayi Yace"Why kikayi masu ƙarya?"
Shiru tayi bata ce Komai ba ta haura Bedroom É—in su
Dan ita yanzu haka tana kallonsa tsanan sa na daÉ—a karuwa

Zaif tashi yayi ya fice, Parking space ya nufa yana zuwa ya É—auki motan sa yabar gidan

Misalin ƙarfe 8:20pm
Yana zuwa Side É—insa ya nufa wanka yayi ya sanya jallabiyan sa fari kafin ya É—auki ledan da ya shigo dashi ya fito falon, zama yayi ya kunna Tv yakai tashar Aljazira
Wayan sa ya É—auka ya kira Mary tana dagawa yace"Kice tazo" yana gama faÉ—in haka ya kashe kiran

Marya kallon Mima tayi wacce tana sanye da doguwar wandon bacci mara nauyi da ves É—insa tace"Uncle na Call u"
Kamar taki sai kuma ta tuna da Ice Cream É—in ta, hijabinta ta É—auka ta sanya kafin ta fice
Tana zuwa ta tura kofar falon ta shigo bakinta É—auke da Sallama
Amsa mata yayi ciki ciki
Zama tayi kan kujerar daƙe nisa dashi
Yayi kamar bai ganta ba , can kuma sai yace"Come here"
ÆŠagowa tayi ta kallesa taga kamar bashi yayi Maganan ba idanun sa na kan Tv

Tashi tayi jiki a sanyaye ta zauna gyafen sa ƙanta a katsa

Ledan ya miƙa mata baice komai ba
Karɓa tayi tana ƙoƙarin tashi ya zaunar da ita kana ya ɗauki injection ɗin da ya haɗa ya kamo hannun ta ya tsoka mata allurar
"Wayyo Hero!!"
Tafada tana kallon sa Idanun ta cike da kwalla
ÆŠauke kansa yayi yace"Get out"
Tashi tayi tana share hawayen ta ta fice daga Side É—insa
Chapter 7 · 0% Book details