← Book details Dr Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 20

Sashe 4

Dr Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata rana ranar Sunday Abbeiy Zaune yaƙe a babban falon gidan sa Alhaji Mamman Mustapha ya shigo da Sallama jin Muryan dan uwan sa yasa Abbeiy juyowa yana kallon sa, rike yake da wata karamar yarinya wacce baza ta wuce shekara ɗaya da watanni biyu ba
Karitso wa yayi yana sakar wa Abbeiy Murmushi
Yana zuwa ya sami waje kan kujera ya zauna
Abbeiy ma Murmushi yayi yana kallon É—an uwan nasa kuma yana kallon Yarinyar yace"Wannan fa Mamman?"
Murmushi yayi yana kallon Kyakkyawar fuskarta yace"Jeki wajan Abbeiy ki"
Mikawa Abbeiy yayi
Yarinya kamar tasan abinÉ—a yace ta fara mikawa Abbeiy hannu tana Dariya
Bayan Abbeiy ya karɓe ta yana yi mata wasa yace"Beautiful Baby, Mamman a Ina kasamo wannan Kyakkyawar Yarinyar nan?"
"Ƴata ce yaya"
"Ƴar ka kuma Mamman taya?"
Gyara zama Mamman yayi yana kallon yayan nasa yace"Eh ƴa ta ce sunan ta ZAHRA Mai sunan Mahaifiyar mu, nasan yaya zakayi Mamakin jin hakan, bayan dawowar ka daga wajan nemamin auren KOSHSHE iyayen ta suka fitar mata da Miji, banji labarin haka ba sai aure sauran kwanan biyu KOSHSHE ta sameni taƙe sanar min cewa ita Ni take so dan haka ko na aure ta ko ta shiga ɗuniya ta lalace, babu yadda na iya haka mukaje wajan limamin unguwar su ranar Juma'a aka ɗaura mana aure, ahalin KOSHSHE najin haka suna ce basu babu ita, haka na ɗauke ta na ajiye ta a gida na daƙe can muka ci gaba da zama, tunɗa KOSHSHE ta sami ciki bata da Lafiya kullum babu dare ba rana haka muƙe yini mu kwana cikin rashin lafiyar ta, ranar da cikin KOSHSHE ya cika wata tara da kwana goma sha ɗaya da Daddare misalin ƙarfe 9 ta fara na kuda, cikin gaggawa na kaita Hospital nan muka shiga bata taimakon gaggawa, bata wani shan wahala ba ta haifi ƴar ta, bayan ta haihu aka gyarata likitoci suka Kaita ɗakin hutu nan ko minti biyar bata cika ba Allah yayi mata ratsuwa "
Shiru yayi yana share hawayen sa yaci gaba da faÉ—in"Yaya nayi kukan rashin Matata, Mata ta gari, bayan kwana uku na É—auki Zahra na kaita wajan dangin Mahaifiyar ta nan suka ce su basu karban ta É—an haka na fita da ita daga gidan,nan na É—auki Zahra na kaita gidan marayu Ni kuma naci gaba da yin aiki na"

Numfashi Abbeiy yaja kafin yace"Than Why ka É—auko ta yanzun ka kawo ta?"

Har kasa Mamman ya É—uka yace"nasan zakayi fushi dani akan ban kawo ta tun farko ba amma kayafe min Please yaya, ga Zahra na baka ita har a bada Æ´ar kace ka haÉ—a ta da Zaifudden matsayin yara a gunka ina neman wannan alfarmar yaya"
Ɗafe kafadan sa Abbeiy yayi yace"Zahra da Zaifudden duka abu guda ne a waje na kaji insha Allahu yadda na ɗauki Zaifudden matsayin ɗa haka Zahra ma taƙe matsayin ƴa a guna"

"ai nima hakan ne kadda ku manta dani mana" suka jiyo Muryan Ammeiy daga bayan su

Murmushi Abbeiy yayi yace"wato laɓe kikayi mana kenan?"

Tana Dariya ta karitso ta zauna kan kujera tana kallon Mamman tace" kadda ka samu damuwa kanina Insha Allahu Zahra zan É—auke ta tamkar Ni na haifeta kaji?"

Cikin jin daÉ—i Mamman yace"Nagode da wannan Auntie na"

Murmushi Ammeiy tayi tace wa Abbeiy"Kawo ta Alhaji"

Tana karban ta Zahra ta farayin Dariya tana kallon Ammeiy
Itama Ammeiy dariya tayi tana wasa da ita

Mamman kallon Abbeiy yayi yace"Ina Babana yaƙe banganshin ba?"

"Ai yana Makaranta a London"

Cikin jin daÉ—i Mamman yace"Alhamdulillah Allah ya bada Sa'a"
Da Amin suka amsa

Akwatin da Mamman ya shigo dashi yaja ya buÉ—e nan ya ciro da wata farar ta karda ya mikawa Abbeiy yace wasikar Mahaifiyar Zahra ce tace idan ta ratsu na baka ka karanta"

Abbeiy karɓa yayi yana buɗe paper ɗin

Nan ya fara karanta wa kamar haka

*Assalamun Alaikum, yayan mu ina maka Barka da warhaka, na rubuta wannan sakon saboda kai kuma ina neman wata alfarma a gunka, yaya koda bayan raina ne inason ka aurawa Zaifudden Zahra a matsayin Matar sa ta sunnah ko taki ko taso amma shi Zaifudden kada kayi masa dole sai ita Zahra kadai zai zauna da ita a a koda yana da wacce yaƙe so to kabarshi ya aura bayan haka sai ka aura Masa Zahra Dan Allah wannan alfarmar nake nema a gare ka yaya Ma'assalam Allah ya saɗamu da Alkairi Amen*

Abbeiy numfashi yaja kafin ya kalli Ammeiy sannan ya mika mata da paper'n nan Ammeiy ma ta karanta

Abbeiy kallon Zahra daƙe wasa a jikin Ammeiy yayi yace"Insha Allahu Baba na Mijin kine Mama ta Allah ya raya mana ku"

Murmushin jin daÉ—i Ammeiy tayi haka Mamman ma

Tashi yayi yana kallon su yace"Bara na wuce kadda dare yayi min gashi gobe inada aiki sosai a Hospital"

Abbeiy ganin har ƙarfe 3:39pm yayi ya kalli Mamman yace"yamma tayi ai kabari gobe ka fita da safe yanzu kam ko ka fita baza ka samu shiga gari ba ai tunɗa ƙarfe 5:00pm suke rufe gate"

"A a zan tafi ko a BENISHEKH (My local government area 🥰) zan kwana"

"To a can É—in akwai gidan da zaka kwana ne?" Cewar Ammeiy

Murmushi yayi yace"Matar yaya ai zan kwana a Locust H4 ( our 🏠 Number Miss you 😢) gidan wani babban likita wadda muƙe aiki dashi a Hospital ɗin tamu"

Abbeiy kallon sa yayi yace"Wani Mutum ne wannan wadda har zaka je gidan sa ka kwana kana ganin ba matsala?"

"Eh yaya Mutumin gaskiya bayi da matsala harta iyalin sa bata da matsala suna karban baki sosai wallahi gashi yana da yara kuma dukka mata ne su 7 da maza 2 yaya"

Numfashi Abbeiy yaja kafin yace"To Allah ya kiyaye hanya sai ka kula kaji abuda gida dukka mata wannan Akwai bin rai"

Yana tashi yace"Babu komai yaya yaran ma suna da karki babu ma kamar ɗayan ƴar tasa wacce taƙe karatun likita a yanzun haka gaskiya tana da hankali Wllhy"

Abbeiy na tashi yayi dariya yace"kodai zaka auro ta ne irrin yabo haka?"

Tsosa kyaya yayi yana kallon sa yace"Tab na isa itama fa anyi Saven Date É—in ta fa"

"Wow hakan yayi ka gaishe su to "

"To yaya Bara na yuce" Kallon Zahra yayi kafin yayi mata Kiss a goshi yace"Miss You Sweetheart Bye"

Ammeiy bataso tafiyan nasa ba haka ta hakura tayi masa Fatan Alkairi

Abbeiy ma badan yaso ba Mamman ya tafi

Da washe gari kamar daga sama aka kira shi a waya yana Office bayan ya amsa aƙe sanar masa da Motan dan uwansa Alhaji Mamman Mustapha yayi hatsari kuma Allah yayi masa ratsuwa

Abbeiy cikin tashin hankali ya nufa gida bai jima da zuwa ba sai gashi an shigo da gawar Mamman
Tsosai Abbeiy yayi kukan rashin É—an uwan sa tilo tak

A haka rayuwa tai ta tafiya cikin jin daÉ—i wani sayin Abbeiy yayi ta kukan sa haka Ammeiy zata sashi gaba tana rarrashin sa kamar jariri
Abbeiy ya É—auki son É—uniya ya aza akan Zahra Komai ya samu Zahra baya tuna kowa sai Zahra
Bayan Shekara É—aya Ammeiy ta haifu ta haifi Æ´ar ta kyakkyawa
Ranar suna taci sunan yayar Ammeiy wato Maryam
Ammeiy ɗuk Son da taƙe wa Maryam bai kai na Zahra ba saboda Yarinyar duk wadda ya kalle ta so ɗaya to sai ta shiga ranka

Bayan shekaru 20
Zaif ya gama karatun sa a London
Zaif bangaren likita ya karanta
TunÉ—a Zaif yazo yaga Zahra yaji baya kaunar ta kwatakwata
Zahra Bata jin magana amma Allah ya dora Mata Son Zaif
Kullum tana jikinsa shi kuma baya Son hakan saboda ya tsane ta shiyasa baswa shiri kullum

Zaif yana da shekaru 25 ita kuwa Zahra tana da Shekaru 10

Zahra tana Makaranta ne a Abuja
TunÉ—a Zahra ta fara zuwa School kullum ana cikin kawo karar ta na dukan yaran Mutane, kuma ita bata da wani aiki sai wasan CRICKET shine tafi so a rayuwar ta
Zahra ta kasan ce tana da ƙoƙari wajan karatu ɗuk jarabawar da aƙe yi to ba'a barin Zahra a baya saboda cikin ɗubban nin ɗalibai Zahra ita taƙe zuwa farko

Ranar da Zahra ta cika shekaru goma sha biyar ta kammala Secondary School ɗin ta inɗa Abbeiy yace ɓangaren likita zata karanta, aiko Zahra kwana tayi tana kuka idan akwai abinɗa tafi tsana sama da likita to babu ita a ra'ayin ta kawai ta zama jarumar Wasan CRICKET Amma Abbeiy ya hana
InÉ—a Zaif yana jin labarin hakan ranar haka yayi wa Zahra É—uka akan hakan

Tun daga wannan lokacin ne Zahra ta tsani Zaif har cikin ranta

Haka zata ringa kusantar jikinsa saboda baya Son hakan ita kuwa dan taga ta sanya ransa ya ɓaci yasa taƙe hakan

Zaif yana da shekaru 36 inɗa kullum yaƙe kwana da ciwon mara
Tun abin baya damin sa har ya fara damin sa, a haka ko wanni dare sai yasha Tea da lemon kafin ya kwanta

Babban Abokin Abbeiy ne yasa mi Abbeiy yaƙe sanar masa cewa yana So ya bawa Zaif auran ƴar sa
Abbeiy tunɗa Abokin sa yayi masa wannan Maganan yaƙe tunani, idan ta shine babu macan da Zaif zai aura bayan Zahra ita kaɗai ce matar sa amma kuma idan yace wa abokin nasa hakan bazayiyu ba abotan su na shekara da shekaru zai bace haka Abbeiy ya amince da zancen......

More Comment
More Typing
Share Fisabidillah

👩‍� *Dr. ZAHRA* 👩‍�

_*Funny, love story*_

*By Asmeety Ce*

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*Free Book*

*Page-9&10*

**WATTPAD LINK**Asma'u Aji Ibrahim

https://www.wattpad.com/story/302746450?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=ASMAUAJIIBRAHIM&wp_originator=mpzyPESu8LQOti9aB44TSAWdBLMfYyHXI2bTd%2F4xBGBoopEqZJVmZEtpYTjP3JfXV6X2Fj2EaDLHFWpku7oEsQX5xGWGb330DhtPLZnKCqh%2FAM7%2FAqJMgKjgMLG%2FeIY9

**Short Story**

*_Bismillah Rahman Rahim_*

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai._

**Alhmdllhi Ala kulli Hamid**

*Wacece MIMA da Zaif*

Abbeiy tunÉ—a Abokin sa yace ya bawa Zaif Æ´ar sa ya aura ya kasa FaÉ—awa koda Ammeiy ce haka har ya mance da zancan

Zahra ta gama Makarantar inɗa Abbeiy yace zata fara yin aiki a Hospital ɗin sa tun daga wannan ranar Zahra taƙe cewa ita batason aikin sai wasan CRICKET

Tun a wannan lokacin Abbeiy ya haɗa ta da Zaif inɗa ya hana ta fita ko ina daga gida sai gida, tunɗa Zaif ya kafa wa Zahra wannan dokan taƙe kara tsarar sa har cikin ranta
Chapter 4 · 0% Book details