← Book details Dr Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Dr Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbeiy ne ya kalli Zaif yace"Gobe idan Allah yakaimu Zahra zata fara zuwa Hospital"
Kallon Abbeiy yayi kana yakai kallonsa kan Zahra yaga sai Murmushi taƙe
"Bakaji na ne Dr. Nace Gobe Zahra zata fara aiki"
Murmushin da yafi kuka zafi yayi yace"Allah yakaimu Abbeiy"
Abbeiy yana Murmushi yace"Amen"
Tashi yayi ya fice daga Falon yana ɗafe kansa daƙe juyawa kamar zai faɗi
A hanya daƙer ya isa part ɗin sa yana shiga Bedroom ya nufa ya faɗa kan Bed ya Kwanta Yana maida numfashi
Wani irin tari ne yazo masa da sauri ya miƙe ya nufi Toilet nan ya fara tari kamar zai cire kirjinsa jin yadda yaƙe masa raɗadi
Wasu gudan jinine suƙe fitowa daga bakinsa kamar an aiko su , sosai yaƙe tarin har yana riƙe setting zuciyan sa
Bayan yaji saukin sa ya wanƙe bakinsa ya fito ya faɗa kan bed nan bacci yayi Wuff dashi

Da asuba Mima ta shirya cikin riga da wando sai ta sanya safan kafar ta dana hannu ta É—auki jakarta da itacan wasan CRICKET sannan ta sanya Face kap ta fice daga É—akin

Kofar get ɗin gidan ta buɗe nan ta nufi Motan da yaƙe zuwa ɗaukan ta
Tana shiga bayan motan ta kalli Budurwar daƙe cikin Motan tace"Hmmm yau babu boye boye kenan kodai takurarran baya nan?"
Murmushi Mima tayi tace"Ruky kenan ai yana nan yanzu na daina jin tsoron sa ai"
Dariya sukayi suna tafa hannu

Suna isa gun wasan CRICKET
Da sauri suka fito suna jin spiker ƙe kiran sunan su babu ma kamar na Mima

Couches daƙe tsaye suna jiran zuwan su Mima suna ganin fitowar su , suka nufo su daya daga cikin yana kallon Mima yace"Master Zee ƙe muƙe jira fa"

"Sorry Sire" tace tana shiga cikin filin wasan CRICKET

Nan Couch ya bada hannu ya busa wushir daga nan aka fara wasa

Jama'ar daƙe wajan masu jajayin riga sune mabiyan bayan Mima
Su kuma masu blue É—in riga su ne mabiyan Ruky

Aiko wasa ta É—au wasa

Mima taci Ruky tso uku
Ita kuma Ruky taci Mima tso biyu

Wasan kuma karewar sa maki 5 ne

Cikin kankanin lokaci Mima ta cinye wasan nan Team na Master Zee suka fara yin ihu wasu kuwa suna É—aga hoton Mima suna jin daÉ—i

Hannu Ruky ta bawa Mima tana faɗin"Shegiya ƙe dai baki faɗuwa a wasan nan gaskiya"
Itama Mima tana Murmushi tace"aiko gwara kinyi joining My Team yafi miki inba haka ba zan ringa cinki kuwa"
Dariya Ruky tayi tana kallon Mima tace"Muje kadda rana tayi kinga kadda asan mun fita"
Mima na dariya suka nufi wajan Motan su , suna ƙoƙarin buɗe kofar suka jiyo Muryan Couches ɗin su suna yi masu Magana
Tsayawa sukayi
"Master Zee yakamat izuwa yanzu ki ringa karban kyautar ki kina tafiya dashi gida"
Shiru Mima tayi kafin tace"zamuyi wannan Maganan daga baya yanzu ina sauri"
Tana gama fadin haka ta shige Mota Driver yaja yabar wajan

A ɗan gyafen gidan su Mima nan aka sauƙe ta , tana Murmushi tayi musu by by kafin ta juya ta nufi cikin gidan

Tana shiga kuwa dai dain Zaif ma ya fito nan idanun sa suka sauka kan Mima
Wani irin jirine yaso ɗiban sa taƙe a ɗafe kansa

Mima da batasan ma Zaif yana tsaye daga wajan Parking space ba ta wuce ciki Abinda

"Ina taƙe zuwa da wannan uban safiyar nan kuma daga ina ta taso da wannan shigar tata?" Cikin sauri yabi bayan ta.......

More Comment
More Typing
Share Fisabidillah

👩‍� *Dr. ZAHRA* 👩‍�

_*Funny, love story*_

*By Asmeety Ce*

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*Free Book*

*Page-29&30*

*_Assalamun Alaikum Masoya ɗuk Mai buƙatar Book ɗin SARAUNIYA SADDIKA Document Naira 500 kacal. Gamai buƙata yayi min Magana ta wannan layin or WhatsApp 07089540330_****

**Short Story**

*_Bismillah Rahman Rahim_*

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai._

**Alhmdllhi Ala kulli Hamid**

Ya shiga falon yaga bata nan hakan yasa shi nufan Bedroom É—in su
Yana zuwa ya riske Mary tsaye tana yafa gyalle
Jin an buÉ—e kofa yasa ta juyowa kallonsa tayi tsaye yana mata wani irin kallo kafin yace"Where is she?"
Mary cikin tsoro ta nuna masa kofar Toilet, kafin ta É—auki Wayoyin ta da Laptop ta fice daga É—akin
Daman ta shirya aiki zata

Zama yayi kan Stool Yana jiran fitowar ta

Mima kuwa da batasan abinɗa ƙe faruwa ba
Wanka tayi ta É—auro Towel ta fito
Idon ta ne ya sauka a kansa , taɓe baki tayi ta nufi wajan Wardrobe tana ciro da kayan ta
Zaif kallonta ta ya saya yi yana kallon satala satalan cinyoyin ta wani irrin yawu ya haɗiye kafin ya daƙe yace"Daga ina kiƙe da wannan safiyar?"
Juyowa tayi ta kallesa kafin kai tsaye tace"daga wajan wasan CRICKET naƙe"
Da Mamaki yaƙe kallon ta yace"wasan CRICKET?"
Gira ta daga masa kafin taci gaba da sanya kayan ta
Yana daga tsayan ta shirya cikin kayan ta sap kafin ta ɗauki wayar ta da Laptop ɗin ta sai makullin Mota da Abbeiy ya ɓata jita ta yafa dan karamin gyallen ta ta ɗauki jakarta tayo hanyar fita

Tsayawa tayi tana kallon sa tace"Malam zaka iya bani hanya na wuce?"

Idanun Zaif sunyi jazir hannun ya É—aga da niyyar sharara mata mari tayi saurin gaucewa tana kallon sa tace"tab marina wai zakayi Hero?"

Damƙe wuyar ta yayi yana huci idanun sa sunyi jazir yace"Zahra zan iya kashe ki kuma na kashe banza Alright?"

Murmushi tayi tace"Idan kafasa Zaifudden, kill me"
Hawaye ne yaƙe zubuwa daga idanun ta

Shima Zaif hawayen yaƙe, cire hannun sa yayi daga wuyan ta yajata ya rungume ta yana hawaye

Kamkame jikinsa tayi tana kuka

Sundau lokaci a haka kafin ya zame jikinsa ya riko hannun ta suka fito falo

Direct wajan Daining suka nufa inɗa Ammeiy da Abbeiy ƙe Zaune
Kujera yaja mata ta zauna kafin shima ya zauna gyafen ta
Gaida iyayen nasu sukayi
Ammeiy daÉ—in ganin su a haka tayi tana kuma kara godewa Allah daya haÉ—e zuciyoyin yaran nasu fatan ta yanzu shine Allah yasa su dau wama ahaka

Zaif Tea kawai yasha
Ita ko Mima cika cikinta tayi kafin tace"Ammeiy zan wuce"
Murmushi Abbeiy yayi yace"Yau Mamata zata fara aiki ina cikin farin ciki sosai"

"Ni kuma ina cikin baƙin ciki ba"
Tace ta ƙasa ƙasa tayi Maganan ta yadda babu wadda yaji ta

Miƙe wa sukayi a tare
Kallonta Zaif yayi yana kallon Abbeiy yace"Abbeiy tare zamu wuce idan na ajiye ta sai na tafi Hospital"

Abbeiy Yana murmushi yace"Hakan ma yayi ai sai kun dawo Allah ya tsare"
Da "Amen" suka amsa inda ita ko Mima ba dan taso ba zasu tafi atare

Suna fita suka shige Mota nan Zaif yaja Motan yabar giÉ—an

A wajan Parking space daƙe Hospital ɗin
A nan yayi Parking
Mima hannu tasa da niyyar buÉ—e kofar Motan
Ganin haka yasa Zaif kamo hannun nata yana kallon ta yace"Ban baki Umarnin Magana da na miji ba, kuma daga nan Ban amince ki fita koda bakin Get nan ba idan bani na baki izini ba, batun nazo kuma idan kin gama aikin ki zanzo nan da 3:30pm mutafi gida"
Kanta a ƙasa tace"To insha Allahu zan kiyaye"
Yana Murmushi yace"Gud Wifey"

Ɓuɗe Marfin Motan tayi ta fice
Tsayawa tayi tana kallon sa kafin tace"Sannu uba na nace sannu, kana faɗin kadda nayi koda magana da ko wanni na Miji naga dai Kaima na mijin ne so yanzu za'a fara kuma fita dai Wllhy sai inɗa Mai na ya tsaya aha Kuma ina jiranka karfe ukun sai kazo" tana gama fadin haka ta shige cikin Asibitin tana kunkuni ƙasa ƙasa

Murmushi Zaif yayi shi tsiwar tama burgesa yaƙe
Jan Motan yayi yabar harabar Hospital É—in

Parking yayi ya fito dai dain kuma Umar shima ya fito yana kallon Zaif yayi Murmushi yace"nima Zaif ban gane maka ba 2days"

Kallon Kamar ya Zaif yayi masa

"Mushige ciki muyi Magana"cewan Umar suna shiga cikin Hospital É—in

Direct Office É—in Zaif suka wuce
Suna zuwa suka sami kujera suka zauna

ÆŠafe kansa Zaif yayi yana fesar da numfashi
Kallonsa Umar yayi yace"Dr. Tell Me maike damin ka Please duk ka canza ka rame "

Idanun sa da tayi jazir ya ware su kan Umar yayi kallonsa cikin raunin murya yace"I'm feel in love"
Zaro Ido Umar yayi yace"What!!"

Fesar da numfashi Zaif yayi nan ya bawa Umar labarin abinɗa ya shiga tsakaninsu da Mima da kuma yadda yanzu yaƙe Son ta

Umar Murmushi yayi yana kallon Zaif yace"Your Rong Dr"
Wani kallo Zaif yayi masa

"Yes Your Rong, Dr Why ka aikata hakan tun yanzu ai dole ta raina ka, kuma fa kace ada baka kaunar ta baka Son ta saida Ka amshi budurcin ta kafin kafara Son ta aiko nine dole nace ba sona kaƙe ba sha'awata kaƙe"

Cikin damuwa Zaif yace"Than What Shall I do?"

Umar gyara zama yayi kafin yace"Zaka share ta, ka fita daga harkan ta kuma ka daina nuna kana damuwa da ita batun Son ta kuma kayi kamar baka Son ta kai dai Abinda zakayi kayi kamar baka taba sanin Mai suna Zahra ba a rayuwar ka, kaga daga nan Ni nafada maka da ƙanta Zahra zata zo tace tana Son ka, kuma batun kwanciyar Aure kuma ka hakura nadan lokuta kadan ita da kanta zatazo ta naimeka da kanta tana buƙatar ka, Kuma da Son samune ma idan tazo kaja mata aji kayi kamar kaima baka buƙatar hakan sai kaga tana shan wahala sannan ka biya mata buƙata kaga daga nan ma zakayi yadda kaƙe so da ita, nidai shine shawarar da zan baka idan yayi maka fa"

Murmushin da bayyi zato ba ya kuɓuce wa Zaif yana shafa kansa yace"That Good Solution"

Mima tana shiga Direct Office É—in Abdullah ta nufa tana zuwa ta same shi kuwa yana saka da aiki
Jiransa tayi ya gama kafin ya fito da ita nan yabi ko ina na cikin Asibitin ya nuna mata da kuma aikin su
Office dinta ya nuna mata nan tayi godiya ta shiga

Tana zama kan kujera tace"Aiki banason ta amma sai nayi?"

Wata Nurse ce ta shigo hannunta riƙe da wasu Files
"Barka da zuwa Sister"

"Yawwa"tace tana kallon Nurse É—in
Murmushi Nurse É—in tayi kafin tace"Are You DR. ZAHRA ?"
Chapter 15 · 0% Book details