← Book details Dr Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 20

Sashe 2

Dr Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"No Abbeiy kabar shi kawai zan shigar mata shi" karba yayi ledan yana nufi Side din sa

Yana zuwa a falo ya ajiye ledan ya wuce Bedroom É—in sa
Bayan yayi wanka ya shirya cikin kananun kayansa kafin ya fito falon
Remote ya É—auka ya kai BBC Channel yana kallon labarai

Ya daÉ—e yana kallon kafin idanun sa ya sauka kan ledan da ya shigo dashi
Tsaki yaja yana daukan wayan sa ya kira Mary tana dagawa yace"kice tazo ta amsa " yana gama faÉ—in haka ya kashe wayan yana ayyana abinda zayyi Mata

Mary bayan Zaif ya faÉ—a mata sakon
Juyowa tayi ta kalli Mima wacce taƙe kwance tana karatun Novel Book na Hausa
Sosai ta shagala da karatun dan Book É—in ba karamin daÉ—i yayi ba Marubuciyar ta tsara Book natan yadda ya kamata
Bataji sanda Mary ke yi mata Magana ba dan gaskiya wannan Book a wajan Mima ba karamin daÉ—i yayi mata ba
Buginta Mary tayi tace"dalla Kitashi Uncle Yana kiranki"

"Ya bani Maye Kuma" ta bata amsa atakai ce tana kuma cigaba da karatun ta

"Wai Ni kike tambaya, idan kinje zaki sani ai"

Gyara kwanciyar ta tayi tana ci gaba da karatun ta

Ganin ko ajikinta yasa tace"Mima cewa fa yayi wai nagaya miki kije ki ansa, bansan maye zaki ansa ba"
Aiko da sauri ta tashi daga kwancan tana kallon Mary tace"Wllhy ice cream dina ne Wow"
Sauka tayi ta nufi hanyar fita taji muryar Mary tace"gaskiya a hado harda rabo na dan yau kam da rabon zan aza ruwan zafi"
Harara ta dalla mata cikin matsifa tace"Yasin zakiga aikin raban ki kuwa, kuma ai ban hanaki aza ruwan zafin ba "

Mary tana dariya tace"A iso lafiya"

Ko sauraron ta batayi ba ta fice tana magana ƙasa ƙasa

Babu kowa a falon hakan yasa ta fice tana salle tana waka

Tafiya tayi kadan ta samu waje ta zauna tana mai da Numfashin cikin jin haushi tace"gida babba haka sai kace filin wasan cricket, inama ace Abbeiy zai yarda na ringa kawo abokan wasan namu mu ringa buga wasa anan amma bazai bari ba"

Sadda ta huta sosai har ta fara salle tana gwada yadda wasan zayyi daÉ—i idan a filin gidan ne kafin ta tuna da abinda ya fito da ita taja tsaki ta nufi Side É—insa

Tana zuwa ta buÉ—e kofar falon ta tura kanta ta shiga ko Sallama babu
A tsaye a bakin window ta hango sa

Zaif kan yana tsaye yana kallon ta, ta glass duk abinÉ—a take yi akan idon sa
Cikin ransa faɗi yaƙe"yarinya kamar shaidaniya haka"

Tsayawa tayi a bayan sa kafin tasa hannu ta riko hannun sa cikin shagwaɓa fuska tace"Hero gani"

Kallon Up and down yayi mata kafin ya kamo hannun ta suka nufi wajan zama
Bayan ya zauna kan kujera itama ya zaunar da ita sannan yasa hannu ya É—auki ledan ya buÉ—e
Ice Cream É—in roba biyu ne duka biyu ya buÉ—e Marfin kafin ya É—auki spoon ya diba ya kai bakinta

A hankali ta ware Lips dinta ta karɓa tana Murmushi

Mika Mata spoon din yayi yace tasha

Nan Mima ta fara sha tana lumshe ido

Shiko Zaif cigaba yayi da kallonsa

Rabin roban tasha kafin ta kallesa tace"na kashi Hero"
Murmushin gyafen Baki yayi irrin ta mugunta kafin ya juya ya kalleta yace"bana wasa daƙe dan haka ki shanye All robans oya now"ya karishe maganan da karfi yana tashi ya zaro bel ɗin sa

Aiko MIMA babu bata lokaci ta fara shan ice cream
Roba daya tashi
Kafin ta kallesa taga yana zura Mata ido cikin kuka tace"Wllhy Yaya Zaif na kishi fa cikina fashewa zayyi"

Daga bell din yayi ya wasa mata shi a baya
Kara ta kwalla tana fashewa da kuka
Nan tashi shanye Ice Cream tana kuka

Bayan ta shanye tas ta fara ƙoƙarin tashi tana rike cikin ta, ta nufi hanyar fita

Zaif baice mata komai ba harta fice

Tafiya take daƙer harta iso kofar shiga falon su

Tana zuwa ta fashe da kuka mai sauti
Ammeiy ce ta leko daga Bedroom dinta tana kallon Mima da tarike cikinta tana kuka

"Wai maye haka" ta tambaye ta

"Ammeiy ice cream tasha fa"cewar Mary daƙe Zaune a kan kujera tana kallon su tana dariya

Wani irin kallo Mima tayi mata na zan kama ki ai

"Mami Ina rabo na" ta tambeta
Cikin matsifa tace"yana gidan ku Æ´ar rainin Sense kawai"

Ammeiy ce tace"bakin baya mutuwa kenan ko?"

GyaÉ—a Mata kai tayi tana tafiya kamar mata mai ciki rike da cikinta , ta shige Bedroom

Dariyar Ammeiy tayi tana girgiza kai ta shige Bedroom dinta

Da Daddare bayan sunyi shirin kwanciya Mima ta kalli Mary tace"Dariya kikai min dazun ko? Gud you see ur resort"

"A a ai Bama haka dake ai Sis yi hakuri" ta faÉ—a tana riko hannun ta

"Ok naji nayi Saida safe" tace tana jan Balanket ta rufu
Itama Mary rufuwa tayi ta kwanta tana bin abinda Mima zatayi mata dan karya ne Kayiwa Mima laifi ta kyale ka a haka har Bacci barawo ya sace ta

Da washe gari Tun karfe 3am Mima ta farka
Bayan tayi wanka ta É—auro Alwala ta fito ta shirya cikin kayan ta na wasa
Kallon Mary tayi tana Murmushi ta girgiza kanta ta fice daga dakin

SanÉ—a take a hankali tana waige waige har ta fita daga Falon
A waje ma babu kowa duk sun tafiyin sallah dan lokacin sallan Asuba yayi maza duka suna masallaci

BuÉ—e get tayi tana lekowa ganin babu kowa yasa ta fice da sauri tana waige waige

Wata bakin Mota ne na hango nan tana zuwa ta buÉ—e bayan mota ta shige tana faÉ—in " muyi sauri kadda sufito su ganmu"

Nan mai Motan yaja suka bar kofan gidan

Mary Bata tashi ba sai kusan karfe 8am
Salati ta farayi tana kallon window ganin rana ya fito rau

Tashi tayi da nufin shiga Toilet taji budewar kofa juyowa tayi tana kallon mai shigan
Zaro ido tayi tana kallon ta tace"wai har kin dawo daga wasan ko maye"

Tana ajiye karar nata tace"Gashi ko kinga newa idon ki kuwa"

"Shine baki tasheni yin Sallah ba duba fa
har karfe 8am fa "

"Wai kinason kice min bakiyi Sallah ba haryanzu?" Cewar Mima tana nufar Toilet

"Eh Mana ai kinki kita sheni ai"
"Ayya Sorry tunda bakiyi Sallah har yanzu ba Bara nayi wanka na fito kinga yau an yafe miki yin Sallah"
Tana gama faÉ—in haka ta shige Toilet da gudu ganin Mary ta nufo ta

Suna zaune kan Daining ta fito fuskarta a harÉ—e ta sami waje ta zauna
Gaida Abbeiy da Ammeiy tayi tana kallon Mima da take mata dariya ƙasa ƙasa

Ammeiy ce ta kalli Mary tace"Daughter lafiya naga Ranki duk a ɓace"

Tana hawaye tace"Ammeiy ai Gatanan "

Mima na dariya itama tai kwaikwayon tace"Ammeiy ai Gatanan"

Abbeiy sawa ya daga mata tayi shiru

"Maye tayi miki Daughter" inji Abbeiy yana kallon Mary da take share hawayen ta
Tace"taki ta tayar dani nayi sallan Asuba fa"

Mima na ajiye cofin hannunta ta kama baki tace"laaa jimin sharri Abbeiy itafa jiya tace kadda na tayar da ita da asuba nan gaba saboda a sanyin nan bazata iyayin sallah da asuba ba shiyasa fa naki na tayar da ita"

Kallon Mamaki Mary keyiwa Mima ji tayi Abbeiy yace"Ohh ashe kece da laifi Daughter Kuma kike kuka"
Cikin kuka Mary tace"Wllhy Abbeiy bamuyi haka da ita ba sharri ne kawai take yi min"
Aiko itama MIMA kukan ta fashe dashi tana tura Plat É—in dake gabanta tace"shikenan tunda baza ku yarda dani ba daman ba sona kuke yiba na sani ai"
Rungume ta Abbeiy yayi yace"Sorry is ok gaskiyar ki ne, look Daughter na karaji kunyi abu tukun nan Kizo kicanza magana to Wllhy sai nabata miki rai"

Mami na kwance kirjin Abbeiy tana kallon Mima tayi mata gwalo tana Dariya........

More Comment
More Typing
Share Fisabidillah

👩‍� *Dr. ZAHRA* 👩‍�

_*Funny, love story*_

*By Asmeety Ce*

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*Free Book*

*Page-5&6*

**WATTPAD LINK**Asma'u Aji Ibrahim

https://www.wattpad.com/story/302746450?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=ASMAUAJIIBRAHIM&wp_originator=mpzyPESu8LQOti9aB44TSAWdBLMfYyHXI2bTd%2F4xBGBoopEqZJVmZEtpYTjP3JfXV6X2Fj2EaDLHFWpku7oEsQX5xGWGb330DhtPLZnKCqh%2FAM7%2FAqJMgKjgMLG%2FeIY9

**Short Story**

*_Bismillah Rahman Rahim_*

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai._

**Alhmdllhi Ala kulli Hamid**

Ammeiy kallon Abbeiy tayi tace"Amma Alhaji kana ɓata Yarinyar nan fa ɗiyewa gaskiya hakan babu daɗi"

Ko kallonta Abbeiy bai yi ba ya fita yana faÉ—in"Ni na wuce "

"Allah ya bada Sa'a ya kiyaye"

"Amen"yace kafin ya fice

Ammeiy tashi tayi ta nufi Bedroom É—inta

Mima ce ta kalli Mary tana dariya tace"Malama ashe babu daÉ—i kenan, jiya kikai min dariya harda cewa(Ina rabo, kin kawomin rabon nawa) to kinga ai yanzu na rama kinsan ZAHRA bata bari ta kwana ta lalace ehe"
Tana gama faÉ—in haka ta tashi tana murguda baki tabara wajan

Mary sosai tayi da nasanin yiwa Mima dariya jiya, dan ita babu abinɗa tafi tsana kamar ace lokacin sallah ya barta abinda yana damin ta sosai , jiki a sanyaye ta miƙe tabar wajan zuwa Bedroom

Abbeiy ne zaune a office Yana aiki wayan sa yayi kara
Hannun yasa ya É—auka

"Na,am Dan iskan yaya kake"

Daga É—ayan bangaren yace"Nrml ya aiki ya kwana biyu"

Abbeiy yana dariya yace"Alhmdllhi ya iyali da sauran su"

"Duk suna lafiya"

"Yayi kyau" cewan Abbeiy yana Murmushi

"Abokina ya najika shiru fa haryanzu fa kai muƙe jira"

Abbeiy dariya yayi yace"Wllhy sorry fa na manta amma insha Allahu dana koma gida zakaji bayani "

"To ina jiranka , kagaida min da iyali"

"Insha Allahu zasuji sai anjima" Abbeiy yace yana kashe wayan

Da yamma suna zaune a falo ya shigo bakinsa É—auke da Sallama
Bayan ya zauna ya gaida Abbeiy da Ammeiy nan Mary da Mima suma suka gaida sa ,amsa yayi fuska babu yabo ba fallasa

Abbeiy ne ya kallesa yace"Uncle kasan abinda yasa na kira ka?"

Cikin ladabi da biyayya yace"a a Abbeiy"

Zama Abbeiy yayi yana kallon Zaif yace"munyi magana da Abokina Alhaji Tanimu akan Maganan auran ku da Aisha shiyasa nace gobe kaje ku fahimci junan ku kafin asa ranar auren"

Tunɗa Abbeiy ya fara magana Zaif zuciyan sa yaƙe bugawa, har Abbeiy ya kammala Maganan

Kamar mai koyon Magana yace"T..to Abbeiy" a rarrabe yayi Maganan yana lumshe idonsa jin kansa yayi masa wani irrin tsara wa
Chapter 2 · 0% Book details