← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 20

Sashe 9

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tom Bayan oga tanimu ya bawa zaid kayan da zai Kai Tasha,shima ya shirya suka tafi tare, a cikin motarsa sai da oga tanimu ya ga anzo daidai Tasha Sanan ya sauke Zaid ya shiga ciki, duk inda zai huce sai masu gadin alhaji sun tsai dashi sun cajeshi ,ledar hannunsa ce kawai basu amsa ba Sabi da sunyi waya da alhaji yace Aiken sane, sai da zaid ya karasa gate din da zai sadashi da alhaji wani matashim saurayi ya fito daga cikin motar ya tsaya a bakin gate din ,har zaidu ya huce ya dawo dashi yace "kai zo Nan" da sauri Zaid ya tsaya Yana tuno kashai din da oga atiku yayi Masa sai kawai ya cigaba da tafiya, shikuwa wanan matashin saurayin ganin Haka yasa ya bi Zaid da sauri ya rukosa, yace "Kai Ina zaka ? Wane ya Aiko ka" a lokaci daya ya jefowa Zaid wadanan tambayoyin Dan Haka kuwa Zaid ya Yi shiru yakasa cewa uffan, can Kuma sai wannan saurayin ya karbi ledar dake hannun Zaid ya kwance ,Mai zai gani sai ga kayan maye da kwayiyi n'a bugawa, zare Ido yayi yace "Kai waya Aiko ka? Wa akace ka kawowa wadannan kayan?" Yana magana Yana dakawa zaid tsawa, shidai zaidu shiru yayi Yana kallon saurayin cike da furgici a kan fuskarsa

Zaune yake cikin mota mai kimanin nera billion dubu dari da saba,in ,Yana zaunene ya jingina bayansa a baya ,ma,ana mazaunin mai zaman banza ba mazaunin dreba ba, kekkewan dattijon da a kalla zaiyi kimanin shekara 68 a duniya, farine tass Kai Kana kallon wannan dattijon kasan ya jima Yana Jin dadi a duniya Dan har yanzu da sauran karfinsa a jikinsa, konnen sa ne ya tsinkayo Masa tsawar da saurayin yake dakawa Zaid ,dasauri ya tsintse idonsa tare da cewa "Kash aiki ya lalace, da sauki ma tun da Fu,ad ne, mikewa yayi da sauri ya zuro kafarsa wajen motar ya Soma takawa har ya karasa in da suke, zaro Ido yayi ganin yadda ma,aikatan nasa suka Dora bindigun su a kan d'an karamin yaro kamar zaid, a fusace yace "Kai fu,ad mené hakan?" "Uhm barka da fitowa abbanmu daman yaron nanne muka kamashi da kwaya " "to sai me Ina ruwanku da kwayar da take hannun sa "

"Am sorry abbanmu Amma dai Bai kamata ba wannan yaron yazama Dole mutafi dashi idan muka barshi anan zai girma a Haka kuma ya Bata rayuwar wasu yaran" "no ku barshi ya tafi" "abbanmu doka ce Kuma zatayi aiki akai muje mota muyi magana" "ina zamu Babu inda zani kusake shi" "tom shikkenan zamu sakeshi Amma muje mota muyi magana" gyd'a Kai kwai abba yayi ya koma cikin mota fu,ad ya bishi a baya, suna Shiga fu,ad ya Kamo hannun sa tare da tausasa murya yace " Abbanmu! Ina sane da cewa wadannan kwayoyin Kaine kasaka a kawo maka ,kawai na basar ne dan bana son wani yafahim ci babban mutum kamar Abban mu Yana aikata irin wannan ,haba Abba kainefa wadan da mutane da dama suke koyi da halayyar ka dan Allah kayi hakuri n'a rokeka ka daina irin Wannan abin, nasani bai kamata ace nine wan da Zan sameka na fad'a maka Haka ba Amma Abbanmu Ina so kada kayi la,akari da cewa Ni karamin 'dan Kane Kuma Mara shekaru dayawa ,duk da bani da shekaru Ina da hankali da hangen nesa Dan Allah Abba amatsayina na Dan karamin Dan ka narokeka kadaina ,inajin Babu dadi Abba da ba Haka kakemin ba kamanta yadda ka raineni wallahi abba inda ka kara shan wadannan abubuwan wannan karan nima sha,zanyi bazan sanarwa da yaya Abjeed ko Yaya Abeed ba " zaro Ido Abba yayi yace "

"Ana da hankali kuwa Fu,ad ,Ni kake fadawa kaima zaka Sha kwaya ? Bana so kada ka Soma dan Allah , indai Akan wadannan abubuwan ne nadai n'a Sha, Daman damuwa ce nake ragewa da ita" "haba abbanmu Wai har yaushene wannan damuwar taka zata kau, zuwa tsawan shekara nawa run Ina karami nake kallonka da damuwa a fuskar ka Har yau narasa lokacin dazaka daina damuwa ka hakura mana yaya bazata taba dawowa ba Tun da Har zuwa wannan lokacin Bata dawoba" "a,a Fu,ad zata dawo komai Daren dadewa zata nemeni, duk da cewar banine na haifeta ba Amma a cikin jinina da zuciyata nake jin ta ,damuwar rashin ta ta hanani sukuni tsawan shekaru da dama ban San yaushene Zan sake saka ta a cikin idanuna ba,har yanzu ban cire rai ba indarai da rabo zata dawo gareni kafin numfashina na karshe ya kare" ya karasa maganar Yana share kwallar da tacika Masa Ido take kokarin sakkowa.

Kukan da Fu,ad yake rikewa ne yakasa rukuwa saï da ya zubo , Sabi da tsananin tausayin Abban su da ace Yana da damar da zai iya dawo Masa da farin cikin sa da ya rasa a baya tabbas zaiyi hakan ,Amma Babu dama dukiya da murlki da sarauta da iko baza su taba iya mai do Masa da shi ba sai dai wani ikon Allah, jiki a sanyaye Fu,ad yace "abbanmu to Mai zai Hana ka dauki yaronnan ka ceceshi daga wannan halin da ake kokarin saka sa a kai ka rikesa Tun da Naga baiyi nisa a harkar ba, ko hakan zai sa shaye shayen da kadade kanayi Allah ya dubeka ya yafemaka, Mai bima ta dalilin Haka allah ta dawo da yaya zaraah" "a,a fu,ad baza a Yi haka ba ba Haka mukayi da wadannan mutanen ba ,idan nace Zan dauke musu yaro naci amanar su kawai abin da nakeso da Kai ka saké shi yatafi" "a,a abbanmu Babu wani alkawari da ka karya daga gani wannan yaron Babu abin da yasani Dan Allah ka taimakesa ,da ace suna da wata dangan taka da yaron bazai guduba ,Abba Yana ganin na Kama yaron wan da ya kawosa ya gudu ,Kuma da d'an uwansune ai ba zasu yadda su sashi a wannan had'arin ba kayi tunani Abba"

"Eh Kuma fa hakane tabbas nayadda kaidin Mai basira ne shikkenan kaje ka d'aukeshi kushiga motar da kazo a ciki saï mutafi dashi gida, inyaso gobe saï muhuce kasar mu dashi" " wayyo allah dadi abbanmu nagode sosai" fu,ad ya fad'a jikin Abban nasu ya rungume, "oh nifa kaga abin da take hadani da Kai fu,ad har abada bazaka taba girma ba ,yanzu sabi da shashanci mené n'a fadowa kaina Kai ko kunya ma bakaji saika karyani ,idan ka karyani ka huta ai" "hhh abbanmu kenan ballema bazan taba karya kaba kamanta nine auta Taya Zan girma anki ayimin Kani" yayi maganar a shagwabe , "to ai gashinan kasamu magajinka sai abar Masa ciyar " "uhm Abba Wai har yazama danka Kai ammafa nayi farinciki Allah ya Kara lafiya Abban mu" "ameen thumma Ameen Fu,adu na" "a,a fa Abba Ni kadaina cemin Fu,adu ga sunana Mai dadi zaka na cemin Fu,adu"

"Ikon Allah to Mai kakeso nace maka?" "Fu,ad zaka ce " "Tom shikkenan fu,ad yanzu nayi daidai" "eh yauwa ko kaifa yanzu kam kayi daidai" yafara Yana zuro kafarsa wajen motar tare da yiwa abbansa sallama ya koma gurin da yabar Zaid da ma,aikatan su. Yana karasawa yace "am Abba yace kusake shi " Babu musu suka matsar da bindigun su daga kan zaid , sankuyawa fu,ad yayi yace "Yaya sunka?" "Za za Zaid" ya fad'a daker , wanan abin da Fu,ad yaji yasa zuciyarsa ta karayin rauni Bai San sanda kawalla ta Shiga zubo Masa ba a zuciyar sa yace "Allah sarki bawan Allah mebi ma maraya ne" afili kuma yace "kanina zaka bini?" Saurin girgiza Kai zaid yayi alamar a,a "maiyasa kabiyoni mutafi bazan cutar da kaiba " kuka Zaid ya saki Yana son yace wani abu Amma ya kasa fad'a sai da ker ya iya cewa "Yaya mujahid" ganin Zaid Yana kokarin Bata musu lokaci hakan yasa fu,ad ya dageshi tsam ya saka shi acikin mota shima ya Shiga sanan ragowar ma,aikatan suma suka shiga suka Soma tafiya motocin suna fita a jerea jere.

💔_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 9*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 9*

Har gumi oga atiku yake wajen tukin motar da ker ya iya saita kansa ya dawo gida ,Yana shiga a tsai tsaye ya tadda su mujahid suna jiran dawowar sa, shi kuwa mujahid Babu abin da yake dubawa sai bayan oga ko zaiga bullowar Zaid Amma shiru hakan yasa jikinsa yayi sanyi idonsa ya kada yayi jajur bakinsa ya Soma rawa daker ya iya bude Baki yace "oga Ina Zaid...... Kar dai kacemin zaid ya mutu ? Oga kamin magana Mana Ina zaid yake naga kuntafi tare Kuma ka dawo Kai kadai han kalin ka kaima a tashe Naga sai gumi kake Dan Allah kayi min bayani karka cemin sunkama Zaid ko ya mutu, "oga atikunw yayi Masa shiru kawai ya tsaya ya zuba Ido yana kallonsa cikin ikon Allah ganin yadda lokaci daya yanayin mujahid ya canza kamar ba mujahid din da yasani ba yarasa dalilin da yasa ya damu da wanan Zaid din" mujahid ne yakara cewa a Karo na biyu "oga Ina Zaid?".......
Chapter 9 · 0% Book details