← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 20

Sashe 6

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tana shiga ta sameta a zaune ta zabga ta gumi ta kasa komawa bacci ,gefan ta ta samu ta zauna ta ce "sumayya lafiya kuwa naganki a Haka ?" "Uhm umma tunani nake Ni sai nake gani kamar abin da mukayi bamu kyau ta ba hukuncin da akayiwa Zaid ya Yi tsauri jikina duk yayi sanyi ban San maiyasa nakejin na aikata wani babban zunubi arayuwa ta ba umma mufita mu nemosa Dan Allah" "afita anemosa to bazan jeba shashasha kewai maiyasa Baki da hankali ne Ina ruwanki da halin da zai Shiga ,to Bari kiji na fad'a Miki idan ma kina mafar kin fadawa malan karyane abin da yafaru sharrine kika Masa to ki daina Dan wallahi bayan korar mu da zaiyi inya sani har Kotu saiya Kai karar mu an yanke Mana hukunci ,yanzu kuwa idan kikayi shiru zamu kashe AMNAA sanan mu yi amfani da wan can dukiyar" "wace dukiyar Kuma umma?" "Shashasha wancan dutsen gold din na cikin akwatin can da fateema ta bani kafin ta rasu" " okay na gane yanzu dai umma Ina son ba koma school gobe Kuma kinsan Abba Bai biya kudinnan ba" "oky ai Babu damuwa Allah ya kaimu goben Ameen" "ameen umma".

Washe Gari da safe karfe 6 Mai gadi ya tashi zaidu saga bacci ,ya sauya Masa Kayan jikinsa sannan ya gyra Masa bakkon kayansa yace "tom zaid na maka iya taimakon da Zan iya maka yanzu abin da nakeso ka tashi ka tafi Tun kafin wani a cikin gidannan yasan kana dakinnan ,kaga idan akasan kana cikin dakinnan korata zasuyi kayi hakuri kaji bayan wuya sai dadi, duk halin da zaka tsinci kanka aciki kada ka cutar da wani ko kace zaka dauki kayan wani haramun ne kaji" sannan nayi niyar taimakon ka Amma Babu Dana iyalina ba anan garin suke zaune ba da na kaika gida na Amma Babu ko Mai na Allah basa karewa a duniya kaje Allah zai taimaka maka" batare da Zaid ya ce masa komai ba ya goge hawayen idonsa ya Mike sannan ya dauki bakkon sa da ta so fin karfin sa dan ta masa nauyi ,ya Soma tafiya ,har ya Kai bakin kofar d'akin ya juyo ya kalli baba Mai gadi yace " naaa na na na nagoooooo de" daga Haka ya fita ya zare sakatar gate din ya fita, tun da ya fita ya Soma tafiya Bai San in da zai nufa ba har sai da yayi nisa da gidan su sosai zai Sha kwana sannan ya juyo ya kalli gidan ya kurawa gate din gidan Ido ,kana ya Shiga lungun ya ciga ba da tafiya a kasa Babu Mai taima kon sa, duk in da ya huce kowa sai ya d'ago ya kallesa Amma Babu Mai cewa uffan Akan Haka, har ya fita bakin titi, Wasa Wasa zaid yayi tafiya mai nisa har ya soma jigata Sabi da yunwa da ta Soma tambayar cikin sa, Tun da bai ci abincin safe ba gashi lokacin har karfe 11am tayi ,Amma duk da Haka Bai daina tafiya ba sai da karfinsa ya kare Kat sannan ya samu guri a kasa ya kwanta ya Dora kansa a kan bakkonsa, duk wan da zai huce saï ya kalleshi Babu wan da ya kulashi balle ya taimaka Masa , wani yarone matashi bazai huce shekara 17 a duniya ba yazo hucewa jikinsa kaca kaca rigar sa kuwa duk a yage ,da alama Yana Shan wahala a duniya ,har ya huce inda Zaid yake ya dawo , a ga bansa ya tsuguna yace "yaro lafiya ?" "Kai lafiya ka kwanta anan?" Zaid dai Sabi da yunwa ta ci tacinyesa baya iya ko magana Dan Haka ya bi wannan matasha da Ido ,Yana rike ciki idonsa na zubda hawaye, ganin Haka yasa wannan yaron ya Gane abin da ke damun sa bakomai bane face yunwa , da sauri ya Mike ya karasa gurin wata Mata Mai sai da abinci a gefe ya Mika kudi ta bashi abin ci ta dawo gurin zaid yace "tashi kaji yaro Kaci "mikewa zaidu ya kasa Yi Sabi da ya jigata ,ganin Haka yasa wannan saurayin ya dagoshi yashiga bashi abincin Yana ci Har ya Soma dawowa hayyacin sa, saï da Zaid ya cinye abincin tas kafin ya bud'e Baki yace "naaaa na na nagoooooo de" hawaye masu zafine suka cika idanuwan wannan saurayin ganin yadda Zaid yake magana da ker yasa ya fahimci Yana cikin tashin hankali ,yasan Babu Mai tsayawa ya saurari maganarsa balle ya taimaka Masa da wani abu sa bida kafin ya Fadi kalma daya sai an Bata lokaci, Dan Haka yayi Sha,awar ya taimaka Masa ,kallon zaidu ya sake Yi wan da shima zaid kallon sa take , "yaro zaka bini?" saurin d'aga masa Kai zaid yayi Har da Dan murmushin sa, "Tom shikkenan gama hutawa saï mutafi a Can gaba kad'an gidan ogana yake Nima ka ganni maraya ne kamar Kai bani da kowa shiya taimake ni kuma nasan kaima zai taimaka maka" murmushi zaid ya Kara Masa can Kuma sai yace "mutafi ka huta?" "Ehh eh naaaannn n'a huuuuuu ta" Mika Masa hannu saurayin yayi yace to muje ko "ya dagoshi sannan ya karbi bakkon kayan suka Soma tafiya ...

*Bayan wata buyu*

"zonan shalele na" tayi maganar tare da mik'a mata hannu, nok'e wuya tayi gami da k'ara k'an k'ame mahaifin nata cike da furgici, "uhm malan kaga Taki zuwa,kizo kinji maza zoki karbi Madara" Takara Kiran 'yar k'aramar yarinyar a Karo na biyu, murmushi malan yayi ya Mike tsaye yace "Ni Zan fita ga tanan Dan Allah ki kula da ita kinji" "Tom shikkenan honey sai ka dawo" ta fad'a tare da d'aukar AMNAA da bazata huce wata biyu a duniya ba, kuka AMNAA ta somayi tana zillo ajikita, ganin Haka yasa malan ya dawo ya na cewa "Wai Ni zainab Mai yasa yarinyar Nan Bata son zuwa gurinki n'a rasa dalili?" "Uhm malan kenan ni kaina mamaki nake Bari sumayya ta dawo ko munira nasan zata yadda da su musamman munira" "okay tom shikkenan sai na dawo Dan Allah ki kula da ita" "insha allah" Tace sanan malan ya fita.

💔_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 6*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 6*

Baifi minti 5 da fita ba ta dungurar da AMNAA a k'asa tare da dungure mata Kai Tace "shashasha,wato ka ajiye baiwarka mai kular maka da yarinyar ",tana maganar tana kallon yarinyar tana zare mata ido, "ubanki zakici wallahi sainayi ajalin ki indai nice ba yafi sonki Akan sauran 'yan,uwan ki ba, takarasa maganar tare da d'aukar ta da hannu d'aya ta ajiyeta a waje, ajiyeta keda wuya ruwan sama ya sakko kamar da bakin kwarya, aikuwa yarinyar ta chanyare da ihu tana kuka tana faman Mika hannu tazo ta dauketa ,Amma Ina Sabi da tsabar mugunta saima ta sake turo kofa ...

Allah sarki wannan baiwar Allan da bataji ba Bata gani ba batasan komai a duniya ba sai soyayyar mahaifinta da kiyayyar zainab , yarinyar da har yanzu batasan wacece mahaifiyar taba ,kallon zainab take a matsayin itace jigon rayuwata ,
Chapter 6 · 0% Book details