← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 20

Sashe 2

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Misalin karfe 12 na Rana su malan suka dawo daga makabarta Dan Haka doctor ta Dan kawa malan jaririyar da fateema ta Haïfa tare da k'ara bashi hakuri suka tafi, Tun da ya kalli wannan yarinyar yaga wani abin mamaki da Al,ajabi yarinyar sak mahaifiyar ta Babu abin da ta Bari nadaga kyau da kamanni irin na mahaifiyar ta, Nan take malan yaji wani so da kaunar yarinyar ya shiga zuciyarsa yaji aduniya Babu abin da take so irin wannan yarinyar, hakan ne yasa yaji tsoron ya bawa zainab rukonta Dan yasan halinta zata iya cutar da ita, sai Kuma wata zuciyar tashi Tace "cutar war me Kuma ita tarasa wadda zata cutar sai wannan kankanuwar yarinyar Mai tasani? Kada ka damu Allah zai kare ta" Kai kawai ya jijiga yace "to idan ban bawa zainab rukwon wanna yarinyar ba wazan bawa?" Yana fadin Haka ta bude kofar gidan ya shiga, a zaune ya samesu sunyi jigum jigum suna jimami can Kuma ganin malan d'auke da yarinya a hannun sa yasa ta Mike ta karaso ta amsheta, durumm gaban ta ya Fadi ganin fuskar matar da ta fi tsana a duniya a fuskar wannan yarinyar Nan take yanayin ta ya canza Tace "malan! Kar dai kace yarinyar da fateema ta Haifa ce?" "Eh zainab itace kinga ikon ALLAH ko ita Kuma Haka kaddarar ta tazo in gota kisamu ki hada Mata Madara Tasha kinji, Dan Allah ki kula da rayuwar yarinyar nan kiji tsoron Allah idan kika cutar da ita allah Yana kallon ki" "uhm malan kenan Kana tsammanin Zan iya cutar da jininka haba malan bantaba tunanin zakamin irin wannan fassarar ba" "a,a zainab ba abin da kike tunani bane kawai dai na tuna mikine akan kiji tsoron Allah Ni Zan koma gurin zaman makoki kije ki hada madarar nasan yunwa takeji" "tom shikkenan sai ka dawo ta fada tare da juyawa ta Shiga dakin ta , tana shiga sumayya ta bi bayan ta , a bakin gado ta sameta Tace"umma Wai Mai baba yake fad'a ne kuma saiki kula da ita din,?" "Hmm sumayya kenan sai kace bakisan Hali na ba wallahi summa tallahi sai Naga bayan wannan yarinyar badai ya barta a gurina ba hmm karya damu" "umma Mai zakiyi Mata Danni wallahi har nafara kishi da ita ayanzu fa Zan iya rantsewa baba yafi sonta akan mu Dan wallahi Naga tsan tsar son wannan yarinyar a cikin idanuwan sa" "uhm kada ki damu n'a fada miki wato nufinsa nayi kishi da mahaifiyar ta n'a samu ta mutu saï kuma wannan yarinyar ta bullo itama nufinsa kishi zanyi da ita wallahi bai isa ba yayi kad'an" ta Kai idonta kan fuskar yarinyar Tace "shegiya aljana Mai Kama da mahaifiyar ta sai Naga wan da zai Bata madarar a Daren yau ko kwana baza Tai ba wallahi ta sheka basai in da abinci zata rayuba to bazan bada madarar ba" ta dungurar da jaririyar a kan gadon Nan take yarinyar ta kwalla uban kuka ,ita kuwa ko a jikinta tayi ficewar ta , sumayya kuwa harar ta watsa mata ta daga hanci daya ta sa hannu ta mintsineta a kafa nan take gurin ya kwailaye abin ka da fatar jarirai, Allah sarki baiwar Allah ga yunwa ga azaba tun kafin ta zama cikakkiyar mace.

💔_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 2*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 2*

________malan na zaune a wajen mako ki yaji jikinsa ya basa kamar a kwai wani abun a gidan ,dan Haka ya Mike ya shiga, tun da ya bude gate din ya shiga jin kukan yarinyar har tsakiyar kansa, cikin tashin hankali ya ce "zainab wannan ba jaririyar ce take kuka ba Kuma kinaji?" Zumbur zainab ta Mike daga in da take zaune ta shiga kame kame Tace " am uhm Daman u hm wallahi malan haba daya na shiga damuwa ne Akan mutuwar fateema shiyasa ban ma San tana kuka ba, Kuma yanzu nagama Bata madara ta samu tayi bacci shine na kwantar da ita" "ayya Allah sarki zainabu karki damu mebi Bata kwoshi bane yanzu Ina madarar sai na Kara Mata da kaina" wani masifaffan yawu zainab ta hadiye gami da tauna lebe ta daga hanci daya Tace "au yanzu malan kana nufin Zan iya cutar da ita kenan har da zakace mebi Bata kwoshi bane ko?" "No ba Haka nake nufi ba ai nasan duk rashin imanin ki Dole Zaki ragawa wannan jaririyar,idan ma kince zakiyi Mata wani abun mai ta sani batasan komai ba koma kin aikata Mata wani abun ke da Allah yanzu dai bani madarar na Bata, ke kuma sumayya Shiga dakin ki dakko min ita" Babu musu zainab ta Shiga kiching ita Kuma sumayya ta Shiga daki ta samu yarinyar har takusa fadowa daga kan gadon Sabi da tsabar mukunta sumayya ta janyo janin gadon saiga shi jaririyar ta fad'o kasa jikuke timmmm, Nan take ta canyara uban ihu wan da yayi sana diyyar shigowar malan a guje Yana salati "innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Sumayya mai yasa méta Haka?" Kukan muna furci sumayya ta daki Tace "wallahi Allah Abba Nima ban sani ba Ina shigowa na ganta a kasa duk taji ciwo Allah sarki abin tausayi Allah ka kaita asbiti kaga cikinta duk ya kurje" "innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Ya furta tare da sa hannu ya dauki jaririyar ya rungume a kirjinsa zuciyarsa na bugawa sosai Yana Jin son yarinyar da tausayin ta na Kara shigar sa.

"Sumayya bani ruwan zafi kinji" da sauri sumayya ta futa zuwa kiching anan tasamu mahaifiyar ta take fad'a Mata abin da ya faru, dariya zainab ta shiga Yi har da rike ciki Tace "shegiya Ashe dai kedin jini nace, yanzu uban mai zaiyi da ruwan zafi tsabar fi,il?" "Uhm wai gasa mata gurin zai danyi saï ya goge ciwan?" "Ah lallai to baza a Kai ruwan yanzu ba ta mutu shegiyar yarinyar, bakiga nami minti 30 a cikin kiching din Nan ba hmm ai na fiso ta jigata sosai kafin nakai yadda ana Bata cikin shegiya zai kulle ta mutu har lahira kowama ya huta" "to umma Amma zaidu fa bake tunanin zai iya zamar Mana matsala?" "Mestwwww zaidun banza zaidun hofi shi awa, guba Zan zubawa d'an banza shikkenan narabu da bakar masifa " "tab nayar da umma mai fada da ke saï ya shirya nidai idone nawa yanzu dai bani ruwan na kaiwa Abba Kar yayi tunanin Ni na hullo da ita" "tom shikkenan ga shi can a cikin kula ki dauka ki Kai masa"Tom Tace sanan ta juya ta dauki kular tayi waje.
Chapter 2 · 0% Book details