← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 20

Sashe 13

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tom a can adamawa kuwa bayan su Fu ad sun dawo daga sallah d'akin da ya huce Kai tsaye ,ya hada komai nasa da yake bukata,kana ya dauki wannan littafin ya saka a jaka karama ya fito zuwa harabar gidan, Kai tsaye but din motar ya bude ya saka kayan sannan ya dawo ya kwanta, ko da ya kwanta kasa bacci yayi Sabi da tsananin tunanin abin da zai karanta a littafin Nan, har ga Allah ya matsu yaji menene asalin wannan labarin da har yanzu kowa yake Masa wasa da hankali yaki sanar Masa, Yana Haka bacci Mai dadi yayi awan Gaba da shi.

💔_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 11*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 11*

***********

"Gwggo kinsan halin oga atiku akan komai zai iya cewa zai hallaka rayuwa ta ,shiyasa na zabi nayi hijira na bar garin adamawa gaba daya , yadda idan ya nemeni bazai samu inda nake ba ,ballanta n'a Har yace zai kasheni" "uhm mujahidu kenan, bantari numfashin kaba amma saï nake ganin kamar zama anan yafimaka alheri daka tafi can wani garin inda baka da dangi ko wani asalin , a tinanina ko Mai zakayiwa atiku bazai iya hallaka kaba kawai dai fad'a yake Amma Ni ban yarda zai iya kashemin Kai ba" "hmm bazaki gane ba gwggo atiku mugune Ni danake zaune dashi ni nasan waye shi kedai kawai ki barni natafi addu,a kadai ita nake bukata daga gareki" "uhm tom shikkenan mujahidu insha Allahu Zan maka addua sosai kobayan ka tafi, ALLAH ta tsare ya kiyaye ka daga sharrin mahassada da makiya adawo lafiya allah ya hadaka da nagari Ameen " daga Haka mujahid ya amsa da ameen yayi murmushi yace "ko kefa gwaggo ta "sai Kuma ya Mike ya nufi hanyar fita batare da sanin inda ya dosa ba.

.....Tun da garin Allah ya waye su ammi suke ta shige da fice a cikin gidan, su girka wannan su sauke wannan ,wani abun ma sai kagani da idonka, bayan ammi ta Gama nunawa yan aikin gidan abin da zasu karasa fito was tayi zuwa falo, anan ta samu Adeena a zaune tana Wasa da Yar baby ita kadai Babu kowa a falon hakanne ya sa Ammi ta kalle ta murya asanyaye cikin nutsuwa tace "Adeena ! Ina sauran yaran gidannan ya a Kai ban ga kowa ba sai ke kad'a i?

Baki ta turo gaba ta kalli Ammi Tace "na saka su a cikin 'yar tsanan nan" daga Haka Bata Kara cewa ammi komai ba ta cigaba da wasan ta.

Hau shine ya Kama ammi Bata San lokacin da ta daka Mata duka a baya ta ce "dan ubanki ni wai sa arki ce , ina Miki magana kina cemin suna cikin Yar baby Sabi da kin Raina Ni " ta sake daga hannu zata Dake ta Abjeed yayi sallama , da gudu Adeena ta Mike ta fad'a jikinsa ta fashe da kuka har da shashasheka,

"Subahanallahi Adeena mai ta faru waya tabaki, lafiya kike kuka?"

"Na hada da Kai da ita din na jibga haba yarinyar tabi ta rainani kamar wata da,arta ta Mai Dani kakarta " "Dan Allah ammi kiyi hakuri Mai tayi Miki Haka kika daketa ?" "Ban sani ba zoka matse bakina idan naji zafi sai na fad'a maka ,Ina kaje?" Ammi na fita ne Ina lambu Bata fad'a Miki bane?" "Ina zata fadamin tana min shakiyanci Wai Kuna cikin Yar baby kajimin yarinya ,wataran saina gurgude Miki kugu na huta da masifarki" juyowa adeena tayi a nutse ta murguda wa ammi Baki tare da cewa " to gurgude din Kuma wallahi abbanmu ya dawo saina fada masa kina duka na" man Adeena Ammi tayo zata daketa da sauri Abjeed yace "yi hakuri Ammi yarina ce fa saï a hankali kiyi hakuri jinki" kafin ya karasa fad'ar maganarsa Adeena tayi caraf Tace "Bata ta dakeni wallahi yau dinnan zansa abbanmu ya sallaneta Daman nasan kishi take Dani tun da abbanmu ya ce ni matarsa ce shikkenan take adda bamin " "oh innalillahi wa'inna ilaihirraju un Adeena yaushe kika koma Haka Aina kika koyo rashin kunya, Ni mahaifiyar Taki kike cewa ajira abba ya dawo ya koreni " ammi tayi kwafa ta girgiza Kai tayi cikin daki Rai a bace.

Hannunta Abjeed ya kamo suka zauna ya kalleta yace "Adeena ! "Naam uncle Abjeed" "kalleni kiga" kallonsa tayi da sauri ta sauke idonta kasa ganin yadda ya hade girar sama da ta kasa babu alamar murmushi ko kadan ,bakinta na rawa Tace "uncle Abjeed Dan Allah kayi hakuri wallahi bazan sake ba ammice fa Bata da gaskiya kullum saikana min fad'a ita baka Yi Mata " dariya ce ta kusan subuce masa ganin yadda tayi zatai kuka ga maganar da takeyi Akan ammi har zuciyarta take fad'a ,wato ita ala Dole ammi kishiyar Tace , dogon numfashi ya ja batare da ya Bari dariyar ta fito foliba yace

"Adeena! Kinga ammi babbace Kuma ta girmeki nesa ba kusaba meyasa kullum kikeson kirinka Bata Mata Rai ammi ce fa kin Mata itace mahaifiyar mu dukka kidaina kinji ,bana son Ina gani kina Mata irin wannan Babu kyau idan kuwa kika ci gaba allah zai Kona ki a wuta" "uhm to ai itama ka fada mata ta rinka min biyayya kamar yadda uncle yake min " "to yanzu Adeena Ammi ce zata Miki biyayya haba Adeena kamar bakya zuwa islamiyya bakisan hukuncin batawa iyaye raiba ko" "tab nifa ba ammice ta haifeni ba kamar yadda Abba ya aureta Nima Haka abbanmu ya auroni " shiru Abjeed yayi batare da yace Komai ba domin zuwa yanzu yaruga da ya fahimci ba kowane ya hada wannan bom dinba sai Abba Dan Haka shikadai ne zai iya fahimtar da Adeena ta nutsu ta gane Wasa yake Mata ba matar sa bace , a fili kuma ya Kura Mata Ido "Kai uncle Abjeed Ni wallahi idonka tsoro yake bani kyaunka yayi yawa" "baiyi niyar dariya ba Amma sai da yayi "uhmm Adeena nikuma " "ehh Mana Ni Bari naje gurin uncle Naga kowa Yana shirye dhiryen dawowar abbanmu Amma shi kullum Yana kunshe a daki ,Bari na kirashi" "uhm tom shikkenan maza tashi kije Tun da dankine ko zaiji maganarki ya fito" Bata sake cewa komai ba ta Mike da gudu ta nufi wani daki Dake kallon falon gidan ,ko sallama batayi ba ta fada dakin da gudu saï jinta yayi a kirjinsa tana dukansa "uncle ! Uncle!! Uncle katashi Dan Allah Ni ka bude ido" tayi maganar tana sa hannu a daidai kan idonsa taba gwale idon wai ala Dole saï ya tashi,

Bude Ido yayi Rai a bace kamar Daren mutuwa ya zabga tsaki ya kalleta yace "Adeena mené Haka ? "Kaii Adeena kuma? "Uhm sorry Mommy lafiya sokike ki kashe Dan Baki " "a,a ni ba so nake ba ganinai kowa zai fito yayi Hira Amma ban da Kai Kai kullum kana cikin daki nayi nayi kana fitowa kaki, kumama Tai abbanmu zai dawo Amma Kai ko farinciki ma bakayi, jiya ka dawo gidannan inata murna dana ta dawo Ashe kace murna ta koma ciki duk kasa jikina yayi sanyi kullum Kai damuwa Haka ake" ido ya Kura Mata sosai Yana kallonta kamar ba itace take zaro wadannan zantukan ba, Yana mamakin yadda yarinya karama take zama tana zaro wadannan zantukan, "mommy Wai keko kike wannan zancen?" "Ban fahimta ba da waye Naga mu biyune a cikin d'akin" "uhm ai kawai Naga kin fage sai Dada kikemin ,to Allah ya huci zuciyar mother yanzun Nan Zan tashi ai bansan yau Abbanmu zai dawo ba shiyasa kikaga ko shiryawa banyi ba" "to yanzu kasani ai sai katashi ka fara shiri nima yanzu wanka zanje nayi Nay kwalliya dan Kar ammi tafi Ni yin kyau " " to Adeena yau Kuma keda ammin naki ?" "To ai dukana tayi kumama yau bazan shiga dakinta na dakko kayaba sai dai ka fita ka sayomin sabo " "haba mommy sabon Kaya Kuma ki tausayamun nagaji bazan iya tafiya ba Allah kiyi hakuri kishiga d'akin ammi ki dakko kayanki" "tab Ni fa bazanje ba nayi ritaya nida shiga d'akin ammi sai nayi sati guda kumama duk abin ta yau idan Abbanmu ya dawo kwana nane ba nataba" zaro Ido Abeed yayi tare da ruke Baki yace "kwananki Kuma kedawa zaku kwanta din?" "Ni da mijina abbanmu Mana?" "Ah lallai mommy kin debota da zafi lallai kina son ammi tayi kulikulin kubura da ke tab ah lallai" "uhm wa abbanmu yananan zata dakeni tab kaga Ni katashi ka sayomin kafin ka dawo nayi wanka a nan dakin ,dan yau bazan SHIGA dakin Ammi ba " tayi maganar tana turo Baki "shikkenan gimbiyata ai ba sai kinyi kuka ba duk yadda kika ce Haka za,ayi" Yana Gama fadar Haka ya saka rigarsa jallabiya blue ya fito falo, anan ya samu Abjeed a zaune ya kishingida da bayan kujerar ya lumshe Ido Babu abin da yake damunsa gashin idonnan nashi kuwa ya sakko Gaba daya ya rufe Masa kasan Ido Zara Zara abin dai gwanin Sha,awa Dole abbansu yace shi har yanzu Bai ga namiji Mai kyau irin Abjeed ba,
Chapter 13 · 0% Book details