← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 20

Sashe 3

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana shiga dakin ta Mika Masa Tace "Abba gashi wallahi sai da na tsaya dafawa shiyasa na dad'e" "uhm Allah sarki sumayya da alama kina son wanan 'yar uwar Taki Naga bakeson abin da zai taba lafiyar ta" ya karasa maganar Yana daukar wani zani a gefan sa Yana Sawa acikin ruwan Yana daddanna mata a jikinta, Allah sarki ita kuma baiwar Allah saï mimmika hannu da kafa take tana tsala ihu tsabar zafin da takeji, sumayya kuwa taune le'be tayi ta juyar da fuska a zuciyar ta Tace "kad'an ma kika gani yarinya kin Shiga hanun mugaye in dai Har Kinga kinsamu Salama to ba kya wanan duniyar ne" "afili kuma ta kalli abba Tace " Abba tausayi take bani da wanan abin ai gwara akai ta asbiti Dan Allah" ta karasa maganar tana goge kwalla, kallonta Abba yayi yace "kiyi hakuri kinji sumayyy Nima bawai bana son na kaita asbitin bane idan na fita kowa kallona zaiyi Kuma idan na tafi wazai zauna wajen makoki kina ganin dai yadda mutane suka cika kofar gida yanzu Haka Zan tsallake natafi asbiti da acema zaidu babbane sai na bashi ya kaita ke Kuma Kinga macece ba zai yuwu ki huce ta ciken mazanna. Nawaje ba" "hakane Abba Amma da ka bani na kaita Allah" a zuciyar ta Kuma tace"Wai shi Abba kamar yasan taget Dina duk yadda zanyi na fitar da aljanar yarinyar Nan daga gidanan na yi Amma ko ta Ina na bullo sai Abba ya kauce Ina ma ace ya bani ita na kaita wallahi saina hullar da ita" afili kuma tace" Abba kayi shiru bakace komai ba "uhm tun da nace bazaki iya ba kiyi hakuri kawai ki zauna kinji, karki damu zata samu lafiya insha allah" "Tom shikkenan abba Allah ya Bata lafiya" suna tsaka da wanan maganar saiga zainab ta shigo dauke da madarar a hannunta ajiye was tayi a gefan malan sanan ta kalli jaririyar Tace "subahanallahi maiya sameta haka?" Ta wani gigice kamar mutuniyar arziki "malan lafiya Naga jikinta duk ciwo ?" "Uhm kedai Bari wallahi fadowa tayi mikomin madarar na Bata" Mika Masa tayi ,har ya dakko kofin zai fara Bata da chokali sai Kuma yaga sai tiriri take "a,a haba zainab Yana ga madarar Kuma tana da zafi wanan ai sai ta kona Mata Baki" "ah haba malan idan baka gode mun ba ai bazaka tsinemin ba duk kokarin danari wajan hada madarar nan abin da zaka sakamin da shi Kanan nufinka Zan iya cutar da ita kenan" ta fashe da kuka har da majina "kawai dai kace min Dan bani na haifi yarinyar Nan ba nakeso na kasheta, Haka kakeso kace ko Sabi da bani na haifeta ba shine zakace nayine domin na Kona Mata Baki haba malan " "kinga Dan Allah ya Isa karki dameni ki karamin wani damuwar kiyi hakuri ba abin da nake nufi ba kenan yanzu dai dauki ki firfita ya Sha iska" "uhm shikkenan Amma malan shikkenan dai.." "shikkenan me Ke barshi ma nasan yadda zanyi" Afusace ya dauki madarar ya kurba ya jujjyata a bakinsa sann ya durkusa fuskar yarinyar daidai bakinta ya Dora nashi bakin yashiga zuba mata madarar a hankula tana shanyewa idanunta a bude cikin idon mahaifin na ta sai faman kallonsa take kamar Mai Shirin Gane wani abin, "nashiga uku ikon ALLAH malan mai zan gani tsabar soyayyar ce yasa saï ta Haka zaka Bata madara tasha?" "Banza yayi mata ta cigaba da diban madarar ya na zubawa a bakinsa Yana Bata har ta koshi, bayan ya kammala ya kalli zainab sake zaune a gefe ta saki Baki yace "bani zani" "malan mai kuma zakayi da zanin?" "Ina ruwanki ki bani zani nace" "Tom" Tace sanan ta Mike ta d'akko Masa zani ta Mika Masa sanan ta tsaya tana kallon abin da zaiyi da zanin, abin mamaki taga ya Dora jaririyar a bayansa ya saka zanin ya daureta Yana faman jijjigata batare da yace uffan ba ,haushi da bakin ciki ne ya kama zainab Dan Haka Tace" Amma malan yanzu duk matan dake cikin gidanan gani ga sumayya ga munira duk bamu Isa mu Goya taba sai Kai haba malan wanan ai duk salon ka janyo mana zagi ne" still Bai kula taba ya cigaba da kaiwa da komowa a cikin falon Yana jijjiga ta har tasamu tayi bacci "Dan Allah malan ka sakko ta n'a goyata yanzu idan wasu suka shigofa saï su zagemu Akan Haka" "Babu wan da zai zageki Akan Haka da ce 'yarki ce shine za a zageki akai amma wanan ana gani ansan mahaifiyar ta itace ta rasu yau kuma Bata da Wanda zai goyata saï ni d'in kingane" ya karasa fadin Haka tare da ficewa daga dakin ya nufi dakinsa, "kutumar uba"zainab ta kurma wata uwar ashariya Tace "wallahi da sake tur'kashi lallai kam yanzu aka fara wasan.

💔_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 3*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 3*

"Umma Dan Allah ki daina da mun kanki akan wannan Dan abin mene Dan ya goyata" "dallacan shashasha rufemin Baki ke da bakisan ciwan kanki ba ,ko da Kuna yara Babu wadda yata'ba goyawa acikin ku sai yanzu zai wani Fara goyata Ni fa aduniya bana kaunar jinin fateema ya sarara a duniyar Nan, wallahi duk yadda za ai saina tarwa tsa rayuwar yaran Nan" " uhm umma kenan ance duk abin da babba ya hango yaro ko ya hau dala da gwaran dutse bazai hango ba to Ni yanzu na hango Miki wani abu da zai faru a Nan gaba" "to sumayya Mai kika hango?" "Ba so kike ki kashe jaririyar Nan ba karta girma?" "Eh hakane Amma yanzu Ina tunanin Babu wata hanya da Zan iya kasheta tun da mahaifinta kullum Yana makale da ita sai dai in ta girma na ci ubanta" "umma kenan to idan ta girman ma bazaki iya kasheta ba" "mai?" Nashiga uku mai yasa kikace Haka 'yarnan ?" "Abin da yasa nace Miki Haka lokacin da zata girma zaidu ya tasa yazama saurayi ya mallaki hankalin kansa ,Kinga kuwa Baki da damar taba kanwarsa a gabansa idan kika fiya takura Matama zai iya daukan kanwarsa su bar gidan Nan" "tabbas kuwa hakane Amma sumayya kina da basira Taya akai kika gano Haka ni ban sani ba?" "Uhm umma nifa 'yar yauce nasan komai n'a rayuwa kuma kullum idona dada budewa yake yanzu abin da zakiyi shine Dole zamuyi yadda zamu fitar da zaidu daga gidannan tun kafin ya girma ya mallaki hankalin kansa" "hakane 'yar albarkar 'yata" "to Amma umma hanyar da zamu fitar da shine bani da ita inason ya bar gidan Nan na har a bada yadda Abba ma zai tsaneshi ya koreshi da kansa" "hhhhh yarinya kina da uwa shu,Uma Taya zamu rasa hanya kedai kawai ki zuba Ido ki Sha kallo zai du a satinan mahaifin sa Zai koreshi da kansa" "to umma ko fadamin Mana Taya kenan kinsan yadda Abba take son zaidu kuwa shi kadaine fa namiji acikin mu?" " An jima da daddare Zan turoshi d'akin ku ki kasance cikin shiri ai kin dai Gane abin da nake nufi ko?" "Kan bala'i wallahi na gane ai kuwa Babu makawa mukayi Shirin Nan sai Abba ya koreshi Kinga sai musamu damar cin uwar yarinyar Nan " "ai dolema na hallaka jaririyar Nan ko Dan Sabi da akwatin gold dinnan" "akwatin gold Kuna ta me?" " Bakisan komai ba 'yanan Zan Baki labari Nan gaba kadan" "Tom shikkenan umma Bari n'a je n'a fara shiri".

*After one week*

Bayan sati d'aya da haihuwar yarinyar Abban su ya Yi sadaka wan da yayi daidai da kwanan mahaifiyar yarinyar a makabarta yau tacika bakwai Kuma yau ne suna Dan Haka ba ayi wani taro ba kawai ya yanka ragone na suna kamar yadda kowacce yarinya ko yaro idan yazo duniya ake yanka Masa, Haka itama aka yanka Mata katon rago sannan mahaifinta ya rada mata suna Mai dadi da ma,ana *FATIMA* wato sunan mahaifiyar ta ya mayar Mata Amma ana Kiran ta da *AMNAA* Masha Allah Allah ya Raya bisa sunnar annabi Muhammad (s.a.w)
Chapter 3 · 0% Book details