Sashe 12
Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fu ad yace tare da rufe littafin ya ruko hannunsa tare da janyosa jikinsa yace "Zaid menene ?" To ya Isa daina kukan kaji, Yana maganar Yana Dan jijjiga bayansa ,"zakaje gurin abbanmu taso maza muje n'a kaika gurin abbanmu kaji, yafada Yana sakko dashi daga kan gado, sannan ya Kama hannun sa suka futa wajen falo, Kai tsaye sama suka nufa gurin abba, lokacin da suka karasa dakin a rufe yake Dan Haka fu ad ya Kwan kwasa ,murya a tausashe Abba yace "Wanene?" "Abbanmu Fu ad ne" batare da abba yasake cewa komai ba ya Mike daga kwancen da yake ,hawayen idonsa ya goge sannan ya ajiye hoton dake hannunsa ya tashi ,zuwa bakin kofar ya bude Masa, kallo daya Fu da yayi Masa yasan kuka yake, hakanne yasa shima ya hade girar sama da ta kasa yace, "abbanmu kuka kake ko?" Murmushin karfin hali Abba ya kwakulo yace
"Fu ad ba kuka make ba" "uhm abbanmu kenan to shikkenan Amma wancan hoton dake kan bed dinka da?" "Hmm Fu ad ka isheni da tambaya fa " "tom shikkenan Abba tun da Haka kace Daman Zaid na kawo maka ya debe maka kewa" "ah to kushigo" Abba ya matsa suka shiga ,a kan gadon Fu ad ya ajiye Zaid shima ya zauna tare da Mika hannu ya dauki hoton, murmushi kawai yasaki yace "uhm kaddarar 'yan gidannan kenan" idon Zaid ne yakai kan hoton nan take idonsa ya ganomasa wadda kejikin hoton ,a tsorace yace "umm umma " yayi maganar tare da Kara matsawa kisa da hoton tana kallonta ,Nan take ya fashe da kuka ya shiga shafa hoton da hannnu, cike da mamakin Zaid Abba ya karaso ya rike Zaid yace "yaro kasanta ne a ina kasan ta?" Daga Kai yayi kawai "
"Aina kasanta ?" "Umma na ce" Zaid ya fad'a a takaice ,ummanka kuma?" To ummanka to tana Ina?" Fu ad ya watso Masa tambaya "ta taaa ta mutu" zaro Ido Abba yayi a tsorace yace "ta mutu Kai wannan ba ummanka bace nasan zarah na Raye Ina da tabbacin zata Bata mutu ba, sai dai in Mai Kama da zarah ce ummanka " "a,a abbanmu saï ta iya yuwuwa umman tasace shekara nawa da barin yaya zarah daga gidannan tun bani da wani wayo sosai ga shi har na girma na mallaki hankalin kaina,"
"Kai fu ad "yata tana Raye Bata mutuba " Abba ya Mike a fusace ya bude wata kofa ya shiga tare da rufewa, shikuwa Fu ad kallon Zaid tayi Tace kaga abbanmu ko zaka zauna dashi" Kai kawai Zaid ya daga batare da yace Komai ba , Fu ad ne ya jjanyosa jikinsa ya Shiga jijjigashi har yasoma lumshe Ido.
*Kaduna gidan su Amnaa
Umma ce zaune a gaban wayarta tana dannawa tare da jera number wayar Dr Abeed a jiki, bayan ta Gama rubutawa ne ta janyo amnaa jikinta tare da Dora hannu a kanta tana bubbuga bayanta ,sannan ta Soma Kira, bugu biyu Abeed ya daga
"Assalamualaikum" ameen wa, alaikumussalam barka da wannan lokacin dortor da fatan kaje gida lafiya ?"
"Lafiya kalau alhamdulillah, sai dai ban gane dawa nake magana ba sorry ban dauki murya ba" ya fad'a a takaice dai dai lokacin da yake gyra kwanciyar sa .
"Ayya yaro nice wadda n'a kawo yarinyar asbitin ku a Kaduna Har kace gida zaka koma ka bani katin ka ,latina wadda ka ce zaka dinga taimakawa ?"
"Ehhh n'a gane n'a fahimta maman Amnaa ko sorry wallahi ban manta da kuba Kuna Raina yanzu Ina Amnaa take ya jikin nata?"
"Jiki alhamdulillah , Amnaa gatanan tana kwance a jikina kasan uwa da da sai Allah idan bata kwanta a jikina ba ajikinwa zata kwanta ,kuma kaga karamar yarinya ce batasan kowaba saï ni ga kiwa datake fama da ita ,to dai Zan iya cewa tana yadda da wata yarinyar makwaftan mu ,Allah sarki yarinyar akwai kirki"
Uhm ,Abeed yayi murmushi yace "Allah sarki wata yarinyar kuka samu?'
"Eh wallahi yar makwafciya Tace yarinyar a kwai hankali ga biyayya ga iyaye ,Kuma kaganta kekkewa Wallahi, Ni da zaka yarda ma yadda baka da auren Nan ai saika ganta ko Allah zaisa ka yaba da hankalinta"
"Uhm maman Amnaa kenan kedai kawai ki kwalleni yadda kika ganni yanzu dai inason ganin Amnaa zuwa anjima domin tana min Kama da wata kwanwata Zan haku anjima a video call sai kuga juna"
Washe Baki umma tayi bakin ta harrawa yake wajen cewa "ah to to Babu damuwa sai ma bakirawo wannan yarinyar itama ku gaysa ko ya kace ?"
"Tom shikkenan Babu damuwa zuwa anjima bye" ya katse wayar kitt.
Umma Bata jira wata wata ba ta janye Amnaa daga jikinta tare da dungurar da ita a kasa Tace "shegiya taji jiki Mai dadi tayi lamo kamar wadda zan shayar, "
Sumayya dake gefe tayi shiru ta zabga tagumi Tace" Allah umma nakamu da soyayyar wannan doctor din tun kafin naganshi anjima ,Kuma shi gashi da alama tarkon mu Bai kamashi ba sai wani share zancen yake Anya kuwa zai Soni?"
"Dalla Can banza shashasha waya fada Miki bazai soki ba shi waye, wane namijine zai ganki yace Bai kyasa ba ai karya yake dolena ya soki wallahi ,to idan Bai Suki ba uban wa yake jira ko wannan macacciyar yarinyar yake jira ta girma ya aura, aikuwa da ya cika asararre Dan Wasa da zuciyarsa zayyi yarinyar da saura kiriss n'a aika shegiya lahira "
"Hmm ban da kince Yana so ya dinga ganinta Allah da kasheta mukayi kawai muka huta haba ,nifa har na fara kishi da ita" ta karasa maganar hade da saka kafa ta ture Amnaa dake kwance Yana kuka " allah sarki rayuwa kenan .
*Oga atiku*
"Hmm Wai haryanzu Baku samu mujahid ba,to kenan Ina wannan yaron ya shiga ne ? Dole n'a nemo mujahid Tun kafin ya tona Mana asiri" "wallahi oga duk in da muke tunanin zamu samu mujahid munje bamu sameshi ba ,kuma tun farko da an nemu shawarata tun kafin ya fita daga gidannan zamu Gama dashi ,Dan Bai Kama ta ace wan da yasan sirrin mu mu barshi ya tafi ba ,kaga yanzu sai mudinga taka tsan tsan idan ba Haka ba sai dai mu hakura mujira sammaci daga gurin hukuma" "no "oga atiku ya Mike a fusace tare da buga kafa yace karyane wallahi duk inda za a samo shi a samomin shi gawarsa kawai nake bukata ,ba a Isa a kamani ba anyi kadan a kamani a zauna lafiya , kuje kuduba ko Ina a fadin adamawa inason Naga gawar mujahid" da sauri ya ran nasa suka hada Baki suka amsa sannan suka juya suka nufi hanyar fita.
*A.k FADAMA*
Tun da Abba ya shiga d'akin Bai fito ba sai da ana kwalla Kiran sallar magriba Dan Haka kaitsaye ya shigo d'akin da ya fita ya bar su Fu,ad. Ciki Dan yayi tunanin sun fita, Yana shiga cike da mamaki ya gansu daga Fu,ad har Zaid baccinsu suke Sha cikin kwanciyar hankali, murmushi yayi a zuciyar sa yace "oh su zaid iyayen rigima wai ummana ce, allah ya kyauta" hannu ya Kai kan kafar Fu ad ya shiga bugunsa cikin nutsuwa yace" Fu ad ,Fu ad tashi Mana lokacin sallar magriba yayi kanaji ana sallah kana bacci oya maza Mike kayi alwala mutafi, Babu musu Fu ad ya Mike tare da furta la,ilaha,illalahu Muhammadur rasululla (s.A.w) sannan ya ce "allah abba banmasan baccin ya daukeni ba" "shikkenan ai yanzu dai tashi Zaid shima mutafi yayi salla idan muka dawo ka hada kayanka jirgin asba zamubi kaji" "a razane yace "abbanmu asba fa?" Eh ko da wani abunne?" A,a abbanmu Daman kan maganar littafinnan ZAN iya tafiya dashi San wallahi ban karantaba Zaid ya Sona kuka nadai fara farko" "tom shinkkenan zaka iya tafiya dashi amma kada ka Bari Abeed ya gani " daga Haka Abba Bai sake cewa komai ba ya sauka kasa,
Fu,ad kuwa mikewa yayi yanufi bathroom cike da tunanin abin da yasa yace kada ya Bari Yaya Abeed ya gani.
Yana Shiga alwala ya dauro sannan ya fito bedroom,Kai tsaye in da ya bar Zaid ya koma ya shiga tashin sa, "zaid tashi Kayi sallah kaji" motsawa zaid ya somayi can Kuma ya Mike Yana murza Ido, cak Fu ad ya dagasa zuwa bathroom ,shina alwalar ya Yi Masa sannan ya fito dashi hannunsa ruke da nasa ,suka fita zuwa masallaci.
*Faransa*
Kwan ce take a kan luntsu memiyar katifarta mai rai da lafiya ,kekkewar dattijuwar da akalla bazata huce shekara 55 a duniya ba, bude idonta tayi da sauri jin yadda yarinyar ta shigo tana tsalle cike da karagi tana cewa "ammi! Ammi!! Ammi yau abbanmu zai dawo woyyo dadi"" innalillahi wa'inna ilaihirraju un" Adeena narasa maiyasa Har yanzu girma kike bakya hankali yanzu Dan Allah kin kyau ta kenan Ina bacci na Mai dadi Zaki zo kina min ihu aka, cemiki akai bansan Abban zai dawo bane? To Mai da murna ciki yarinya Abba dai sai gobe zai dawo ba yau ba" baki Adeena ta ta'be zatai kuka tana magana Tana babbuga kafa Tace "Allah ammi uncle ne ta fadamin yau abbanmu zai dawo kuma nasan bazai mun karya ba" "eyeee ah lallai yarinyar nan wato uncle bazai Miki karya ba itakuma ammi zata Miki karya kenan to Dan ubanki uncle din ma bani na haifeshi ba ,Ni yakata kifi sanin gaskiya a gurina Sabi da Ni matar Abban ce" "wallahi ke ba matar abbanmu bace " "la ha ila Adeena kina da hankali kuwa Har kina rantsuwa Ni ba matar Abban ku bace ,to kenan matar wace Kuma duk yaran gidannan wace ta haifesu? "Tab nice matar sa Naga abbanmu yace ke ba matarsa bace nice matarsa Kuma duk yaran gidannan har su uncle Abjeed duk Ni na haifesu ba keba" "ah to yayi kekika haifesu ko to zonan zakici kwal ubanki yau tun da Ni kin Mai Dani kakarki" ammi ta Mike da sauri, kafin ta gana tashi Adeena ta watsa a guje, tana dariya.