← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 20

Sashe 16

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban San Mai yasa yarinyar Nan ta nemi shigowa rayuwa taba,Ni dai har zuwa wannan lokacin Ina tsaye a inda tatafi ta barni ,a tsarin rayuwata bana da bajed din na auri wata a ahalin mu , Sabi da Ni nasan kaina bazan iya adalci ba ,domin zuciyata daban take da ta sauran mutane ,amma Kuma sainayi kokari na bar abin a zuciyata na Soma takawa zuwa part dinmu, a lokacin da na Shiga falo kafin ba bude kofata sai da nayi duba zuwa kofar d'akin ta ,a take tausayinta ya shiga zuciyata ,Sabi da yadda Naga tana zubar da hawaye a kaina ,babban kato barar da na tafka a rayuwa ta kenan tausayi ,ko da so daya ban taba Jin son zarah a Raina ba ,Amma Kuma lokacin da na Yi tozali da ita sai naji Gaba kidaya tausayinta ya mamayemin zuciya, abin da zai Baku mamaki Ni Abeed har yanzu ban fara sonta ba ,Sabi da Ni kyaun mace ko muryar ta baya taba rudani, a yanzuma da kukaga n'a tsaya ina kallon bakin kofar dakin ta, ina kallon gurinne sabi da tsananin tausayin ta danake Yi Sabi da masifar da ta tunkaro ratuwarta ganga Ganga.

Bayan shiga dakina, kwanciya ya nayi zanyi bacci Ashe ita ba bacci takeba takasa baccin, Wai kunsan maiyasa ta kasa baccin? Allah sarki baiwar Allah ,kawai Sabi da nace Mata I kiss you Kuma bansamu tayi min ba wannan dalilin ne ya hanata bacci, Ina kwance Ina nishadina sai jin bugun kofar ta nayi a hankula , da farko na tsora ta Amma Kuma sai na Dake nace "waye da cikin darennan za a damu mutane" siririyar muryar ta naji ta ce "yaya nice? Tana fadar Haka na gane wacece jikina a sanyaye nace "zarah lafiya bakiyi bacci ba?" "Yaya nakasa bacci burina kawai namaka abin da kake so bana jin dadi ace ka nemi Abu kuma nakasa yi maka" "uhm Zara,u kenan Babu komai kije ki kwanta" "a,a wallahi Yaya Ni sai na Yi maka" Babu yadda na iya Haka n'a taso jikina a sukwane n'a bude kofar ,matsa mata hanya nayi ta shigo sannan n'a Tura kofar, . Babban abin da nake tsoro shine yafaru a lokacin abin da zarah Bata sani ba shine inhar na soma kulafuci a kan Abu to Dole ne sai na sameshi domin Sha,awata halittace kamar yadda aka dasa a jikin kowane Dan Adam Nima Haka tawa take Amma tawa daban take da ta wasu, hannuna guda daya na daga na Dora a kan kafadar ta data kuma n'a saka shi a saitin mazaunen ta, na matseta a jikina na wajen "yan dak'iku, kafin daga bisani na Dora bakina a kan nasa ,cikin nutsuwa da solo irin n'a 'yan duniya bake kissing din bakinta kamar nasamu sweet.....

"Uncle! Uncle Fu ad!! Wallahi abbanmu yace idan bazaka zoba kayi ta zama ,Sabi da karainashi yakiraka ka zauna ,Haka Abba yace n'a fada maka"

Kamar saukar aradu yajiyo muryar Adeena tana kwalamasa Kira ,tsaki Fu ad ya daka ya ajiye littafin ya danyi shiru can Kuma ya lumshe Ido ya bude yace "Kai Amma Allah ya Isa wallahi sai da nazo daidai gurinnan za a katseni haba abbanmu yazakanin Haka ,Ni wallahi abin cinma har naji na koshi", Fu ad ya daka tsaki ya Mike tare da saka farar jallabiya ya bude kofa ya fito,yayi sama fuuuuuuu.

Tashin hankali wan da ba a samasa Rana abin da Fu ad ya manta shine Abba yace kada ya Bari Abeed ya ga wannan littafin gashi yabar kofar dakinsa a bude,

Abeed ne ta sakko daga dakinsa dan yadda yajiyo Adeena na kwala Masa Kira har sau uku tana zuwa tana cewa Abba Yana Kira Amma yaki fitowa, hakan yasa Abeed ya sakko domin yaga abin da Fu ad yake a d'akin har yaki zuwa Kiran da Abban Basu yake Masa,

Kai tsaye Yana zuwa d'akin ya shiga yayi sa a yasamu dakin a bude, bedroom ya huce ya Shiga dube dube , baiga komai ba kawai sai ya juyo zai fita, Nan take idanunsa suka hango Masa wannan littafin Dake bude a kan bed din fu ad, "innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Abeed ya furta Hadi da cewa nashiga uku, take yaji jiri na Shirin kwasar sa , yayi saurin zama a kan bed din sharaf Yana kallon littafin idanunsa dauke da hawaye, hannunsa yakai kan littafin ya dakko yashiga shafawa Yana zub da hawaye masu zafi da dumi, "why Fu ad sirrina, Wai Mai yasa a gidan Nan akeson ayimin tonon siririne nashiga uku" Abeed ya fad'a tare da kifa kansa a tsakanin cinyoyinsa ,Nan take jikinsa ya dauki rawa yakaa ko motsawa daga gurin.

Shikuwa Fu ad bayan yaje Kiran da Abba yamasa tsabar zumudin ya cigaba da karanta littafin ,abin cinma karba yayi ya sakko da shi kasa ,Wai shi a nufinsa Yana cin abin cin Yana ci gaba da karanta littafin sa.

" Innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Ya furta lokacin da ya shigo dakinsa Bai San lokacin da yasaki a bincin ya kife a kasa ba, ganin yadda Dan uwana nasa ke kuka kamar ransa zai Fita, ga idanunsa dayayi jajur duk yazama abin tsoro, bakin fu ad har rawa yake wajen cewa "narantse da Allah Yaya Babu abin da nasani akai , yanzunan na Soma karantawa Dan girman Allah kayi hakuri Yaya" jikin Abeed a sanyaye ya Mike batare da yace Masa komai ba ya Soma takawa har sai da ya karaso gaban sa yace "so kake kaga komai ko, ko sokake kaji abin da yasa abbanmu ya tsaneni? Mezakayi da tarihin da ya shude , ko sokake kaji abin da Bai kamata kajiba, ban taba tunanin zaka iya daukar wannan littafin daga inda na ajiyeshi har ka ta ho dashi faransa, nayi tunanin daga inda labarin ya faru a inayan muka taso muka barshi, Ashe Kai so kake ka dawomin da ciwon da nakeso n'a manta a matsayin sabo" Abeed ya karasa maganar tare da goge hawayen sa ya dauki littafin ya fice dashi a hannunsa.

Shi kuwa Fu ad har lokacin jikinsa Bai daina rawa ba ,Sabi da tashin hankalin da yaga Ni a cikin idon yayan nasu, jiki a sukwane Babu kwari ya ja kafarsa zuwa bakin gadon ya zauna shaff ,tare da dafa Kai yace "innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Innalillahi wa'inna ilaihirraju un !! Wallahi tsab zuciyata zata iya bugawa muddum ban karasa karanta littafinnan ba, domin ni yanzune nakarasaka Book d'in a zuciyata ban jin yadda na Soma karantawa Zan hakura da shi ba".

💔_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 13*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 13*

***********

Abeed kuwa Kai tsaye sama yayi hannunsa dauke da littafin, abbanmu da sauran yan gidan suna zaune suna cin abinci suka ga hucewar sa da littafin a hannunsa ga hawaye a kwance fal a cikin idanuwansa, hankalinsune ta tashi ,da sauri Ammi ta Mike zata bi bayansa, abba ya dakatar da ita, kallonsu Adeena tayi Tace "Kai mai yasamu Uncle Dina?" "To Adeena Mai kika gani?" "Abbanmu kuka Naga yanayi ,Ni wallahi nagaji ku kullum bakwasan shi duk na fahimceku kullum kuntsaneshi sai kuyi tasashu kuka bansan Mai yayi muku ba" "to Adeena mudinne muka tsaneshi yanzu Kuma wakika ga yayi Masa wani abu Naga daga kasa ya hawo" "uhm uhm Allah ban Yar da ba Ni barima na tashi bazanci abincin ba ,dazufa da ker na rarrasheshi ya daina kukan yanzuma kun Kara sakashi kuka ko?"

"Kiyi hakuri my mommy anan gurin Babu wan da ya saka danki kuka ki daure kici abin cin kinji "

"A,a wallahi bazan ci ba" Adeena ta Mike zata bi bayan Abeed Abjeed ya ruko ta tare da daka Mata tsawa yace " ke ana Miki magana kina ke sai kin je to jeki din, kiga yadda zanyi kasa kasa Dake anan gurin".

Abjeed yayi maganar Rai a bace.

Gigicewa Adeena tayi ta fada kan abba tare da fashewa da kuka, cikin masifa abba yace "lafiyarka kuwa Abjeed ? Menene Haka dafa magana saï kafara daka mata tsawa kabarta tatafi mana" "uhm abbana Kana fifita yarinyar nan bansan maiyasa ba , an hanata Abu ita ala Dole Tace sai tayi ,tabarshi yaji da abin da yake damunsa Mana ,haba dame zaiji da damuwar ka daina masa magana ko Kuma da takaicin nunawa Fu,ad inda litttafin sirrinsa yake,haba Abba nasan wallahi Babu Wanda zai fadawa Fu ad inda littafin Nan yake saikai,na rokeka Dan Allah ka barshi Haka, sokake ka dawo nasa da ciwon da ya Dade da warkewa, nayi imani Fu ad ya gana karanta littafin Nan ba Yaya Abeed ba hatta Kai da ammi kunshiga uku, to maiyayi zafi Dan Allah abin Nan ya isheni, Sabi da hakafa na tattara kayana na tafi Dubai sai gashi Kuna son dawo da sabuwar matsala" Abba dai shiru yayi ya kasa cewa komai, domin jikinsa ya karayin sanyi da wannan lamarin, tabbas Bai kamata ya sanarwa da Fu ad inda littafin Nan take ba ,shima ba Dan ra ayin kansa bane ya fada masane kawai dan ya daina ta kura Masa.
Chapter 16 · 0% Book details