← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 20

Sashe 5

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" A,a har yanzu bakisan Mata ba zainab bana tunanin wannan d'an karamin yaron zai iya aikata abin da kukace amma Bari naji ta ba kinsa" "zaid! Zaid !! d'ago ka kalleni kaji ko" dagowa zai du yayi ya kurawa mahaifin nasa ido cikin farga ba da rashin sanin abin da zaice.

Cikin nutsuwa ya Soma yimasa magana Yana cewa "zaid shin da gaske ne ka Shiga dakin yayarka sumayya kuka abin da Tace kayi mata kay?" ,"Haba malan wannan ai ba adalci bane yaza ai kadinga Masa irin wannan tambayar Kai ma kasan gaskiya sai karinga takewa" "Kinga zainab ya isheki Haka kibari kamar yadda namata magana a nutse shima nayi Masa"

"Zaidu kabani amsa hakane?" "Ah ahh an abb abb abba wallllllllll walla wallahi ba Haka bane "
"Dalla Can rufe Mana Baki shashasha kafin kayi magana daya saika Bata Mana Rai ka bude baki kayi magana ko yanzu jikinka ya gaya maka"

Habawa nan take cikin sa ya Murda jikake kulululu ya hadiye wani masifaffen yawu lokaci guda ya tuno da gargadin umma da Tace duk abin da sumayya Tace tace to idan ba Haka ba sai ta yanka shi Kuma ta yanka jaririyar su, "Kai zaidu magana fa nake maka shin dagaske ne anyi Haka ?",Abba ya Kara jefo Masa wata tambayar a Karo na biyu.

"Eh ehhh eh abbbba da da dagaske ne an anyi Haka ?"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! innalillahi wa'inna ilaihirraju un !! Innalillahi wa'inna ilaihirraju un !!! Nashiga uku zaidu innalillahi wa'inna ilaihirraju un !!!! Abba ya fashe da kuka ,itama sumayya kuka ta sake fashewa dashi tana cewa "wallahi Abba in dai baka koreshi ba Ni saina kashe kaina Sabi da duk lokacin da na ga fuskar yaronan Dole abin zaina dawomin Kuma zanji ciwo ace kanine Dan iska kuma abba wallahi idan ka barshi baka Kore shiba zai zauna ne ta Bata rayuwar mutane Har da yaran ma kwafta tun da yanzu Yana yaro ma yayi Haka balle kuma ya girma Nan Gaba saiya zanyo mana masifa " "hakama bazata faruba dolene ya bar gidannan bazai yuwu na zauna dashi a Haka ba" "uhm kokai fa wallahi idan ka barshi nan gaba yar wani zaiyiwa ciki shikkenan kaga saï ya Bata maka suna ya Bata sunan gidan Nan sannan ya Bata rayuwar su yadda bamai Sha,awar zuwa neman auren "yayanka "

"Ki ma daina fad'ar Haka dolene na koreshi ayanzu Amma ban taba tunanin Haka daga gurin zaidu ba iya tarbiyya na bashi hakama mahaifiyar sa"

Kuka zaidu ya saka ya Soma cewa "abbbbbba ab Dan allla allah...." Bai karasa maganar ba yaji saukar wani gigitaccen mari a kuncin sa "uban me kuma zaka cin ?yimin shiru naji da bakin cikin daka kunsamin"

"Hmm to yanzu Mai ake jira ya d'ebo kayansa ya bargidan Nan" "a,a zainab yanzu darene abari sai da safe sai ya tafi" "wlh baza a bari sai da safe ba yanzu zai tafi" tatashi a fusace ta shiga d'akin su ta d'ebo kayansa a cikin bakko ta hurga Masa, "tashi ka huce kafita" mikewa zaidu yayi abin tausayi Yana kuka Yana Jan numfashi har da majina, "kukan me ka tsaya yi tashi" ta kama hannunsa ta tunkudashi saï gashi ya Fadi kasa Nan take bakinsa ya fashe jini ya Soma wanke Masa Baki, saurin runtse ido abba yayi ya Mike ya shiga daki domin baya son ganin zaidu a damuwa kawai Babu yadda ya iya ne sunfi karfinsa dan Haka ya zauna a bakin gado ya saki kuka kamar karamin yaro ,yasan yanzu idan yace bazai Kori zaidu ba zasu iya kaishi Kara mebi ma a yankewa zaidu hukunci na shekaru a gidan yari to da wanan abin gwara ya koreshi din.

Munira Dake gefe a tsaye ta karaso da sauri ta durkusa gaban umman tasu tashiga rokonta "Dan girman Allah umma kada kiyi Haka kiyi hakuri Dan Allah kada ki koreshi kiji tsoron Allah, zaidu Babu abin da ya aikata muku Shidin kawai karamin yarone Bai San komai ba sai kadaici da damuwa bashi da kowa sai mu yanzu idan kika koreshi Ina zaune?" Bashi da inda zaije bashi da wayon da zai iya neman abinci yaci sokike ya wulakan ta BAYAN Yana da iyaye ,ko so kuke kusa shi ya Rika bin layi Yana bara dan neman abin da zaifi?" Umma kada ku gurbata rayuwar sa dan Allah ,Yana da tarbiyya Yana da addini daidai gwargwado kada kiyi sanadiyyar fadawar sa gurbatacciyar hanya , dan Allah kiji tausayin sa kada ki koreshi".

Kafa tasa ta harbe ta da kafa ta Soma surfa bala'i "munira zanci... Hmmm da ace ba a gida n'a haifeki ba wallahi da saina ce canzamin ke a Kai ,ni duk yarona indai ta Sha nonona Babu dugon imani a zuciyar sa amma ke bansan uban wa kikayo ba Naga alamar sai na fara Saba Miki tukunna Zaki daina min shishshigi a lamurana ,wallahi muddum kika Kara magana akan zaidu saina tsine Miki albarka shashasha kawai"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Zaki tsinemin fa kikace umma ni Zaki tsinewa?"

"Eh tsinemiki zanyi huce ki ban guri"

"Kai kuma tashi tunkafin na karkasheka anan" tayi maganar tana daga zaidu ta ja hannun sa zuwa waje, me gadi Tace ya bude Mata gate Babu musu ya bud'e Mata ta tura zaidu waje sanan ta hurga Masa jakar kayansa.

Juyowa tayi ta kalli Mai gadin Tace "sauran Kuma Naga ka taimake shi abakin aikin ka" tajuya ta koma cikin gidan.

Tsayawa yayi maigadin Yana kallon ikon allah Can Kuma sai ya mayar da gate din ya rufe ya saka sakata a zuciyar sa yace "Allah sarki rayuwa idan ba mahaifiyar ka agida sai yadda kagani gashi wanan yaron mahaifiyar sa ko sati uku Bata cika da rasuwa ba Amma jibi ,Allah ya kyauta" ya koma kan kujera ya zauna.

Cikin tsakiyar dare misalin karfe 4 hadiri ya hado Ganga Ganga yayi bakikkirin saï waljiya ake gari yanata kara, Can Kuma sai ga wani ruwa Mai karfin gaske ya sakko shahhhh kamar da bakin kwarya sosai , Mai gadi dake zaune a waje ya Mike ya Shiga dakinsa ya kwanta can Kuma sai yaji bazai iya kwanciya ba Yana da tabbacin zaidu Bai bar kofar gidanan ba Dan Haka ya Mike cikin sauri ya bude gate aikuwa can ya hangoshi ya takure guri daya sai rawar d'ari yake ruwa ya jikeshi jakaf, "yaro" dasauri zaudu ya dago ya a kallonsa, "zonan kaji" Babu musu zaidu ya taso d'auke da kayansa a hannunsa ya shigo, maigadin ya Kama hannun sa ya kaishi dakinsa, sanan shima ya Shiga,.

💔_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 5*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 5*

Acan cikin gidan kuwa Abba ya kasa bacci yarasa Mai take Masa dadi sai faman juyi yake Yana tunanin halin da 'dansa namiji tilo guda d'aya yake ciki ,ji yake ajikinsa duk inda zaidu yake a yanzu baya cikin koshin lafiya, zaune ya Mike ya kalli zainab yace "yanzu Ina zaidu yanufa gashi ana ruwa karfa yakamu da zazzabi " "to sai mai?" Mu ina ruwan mu Kai kadamu kanka " "uhm zainab Dole n'a damu wlh damuwa tazama Dole hankalina bazai kwanta Bari naje n'a duba ko Yana waje" "kaje ka duba kuma?" "Eh dubawa zanyi idan nayi Haka allah saiya kamani" Yana Gama fadar Haka ya fice waje" sauri ya shiga Yi har ya karasa bakin gate din ya zare sakata ya leka ko Ina Amma yanemi zaidu sama ko kasa ya rasa, jiki a sanyaye Babu kwari ya juyo karaf suka hada ido da Mai gadi yace " alhaji lafiya wani abun kake nema ne ?" "Am uhm dan Allah bakaga inda zaidu yayi ba" tinani mai gadin ya somayi da kamar ya ce Masa gashi a dakinsa sai yaji tsoron Kar nemansa yake sukara dukansa Sabi da Bai tafi ba koma gudin tsoron Kar ya rasa aikinsa yasa yace " gaskiya Banga zaidu ba"

"Oh good innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Shikkenan bansan kuma yazanyi ba " ya fad'a tare da sauri komawa cikin gidan,

Sai da Mai gadin ta dan tsaya kafin ya koma cikin d'akin sa ,cikin sauri ya janyo zaid ya shiga cire masa jikankun Kayan ya lullube sa ganin yadda yake rawar sanyi, "sannu zaid kaji ,zaka ci abinci?" "Ehhhh ZAN Zan ci" "Tom shikkenan tashi Kaci" mai gadin ya dakko Masa ragowar abincin Daren da da yaci ya rage, sosai zaidu ya shiga cin abincin har ya cinye Tass sanan ya kwanta ya Soma bacci, Allah sarki rabon sa da komawa bacci Tun da zainab tazo ta tashesa.

Acan cikin gidan kuwa bayan ya Abba ya koma zainab ta shiga tambayer sa "shin kaga zaidun?" "Uhm wallahi ban ganshi ba na duba duk inda ya kamata Amma ban ga Zaid ba ,ban San Mai yasa ba jinake kamar wani abu Yana faruwa dashi ,yanzu Ina yaje wazai rikeshi awane Hali yake bansani ba kawai mudai min yanke hukunci cikin fishi ga abin da ya ja Mana" "ban gane hukunci cikin fishi ba malan nufinka kenan da ansani anbar shi llai ma wato Sabi da ba Fatima ya so ya lallata ba ko?" "Kinga zainab ya isheki ki barni naji da abin da yake damuna karki karamin wani ciwan kan dan Allah" ..

"Okay d'akin ma ai saï n'a barmaka Tun da ciwan kai Zan Dora maka" ta karasa maganar tare da ficewa d'akin su sumayya.
Chapter 5 · 0% Book details