← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 20

Sashe 11

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Abba ya saka yace "karamin su babban su, kan lafiya ?" "Yar dariya yayi yace "Kai abbana a she zaka ganeni wallahi nazata bazaka ganeni ba Dan muryata na sauya bakaji ba?" "Uhm Abjeed kenan ko Ina bacci najiyo sautin muryarka saina Gane kaine" "to abbana meyasa?" "Sabi da muryar ka ta fita da ban ,muryar ka ki wata macen albarka dan dadi" "uhm uhm Kai abba dan Allah kadaina yabona sai kasa naji nidin wani hadaddene" "ah to da fa bawani yabo gaskiya bake fad'a Abjeed Dina ,kasan ma mene kuwa ?" "A,a Abbana sai ka fada?" "Uhm n'a zaga kasashe da dama Har yanzu Banga mutumin da ya Yi ko kwata na kyawun kaba " zaro Ido Abjeed yayi yace "Kai abbana shikkenan dai abar Zan cenan yaushe zaka dawo?" "Gobe insha allah ka dawone ai nayi tunanin Kana Dubaï " "a,a Abbana nayi kewarka ne shiyasa n'a dawo kuma Daman Ina farincikin dawowar Yaya Abeed shiyasa nadawo" "au aveed din ya dawo ne ?" "Eh abba yaya Abeed ya dawo sai dai kamar baiyi farincikin dawowa taba" "to meyasa Mai kagani?" "Abbana kaima kasani ai Sabi da Ina hanashi tunani Mana yanzuma kaganshi can Yana fama da tunani" ",uhm bansan meyasa Abeed yakeso ya illata kansa Sabi da zarah ba Ni kaina mahaifinsa na hakura ballanta na Kuma shi da yayi silar wargatsa mata rayuwa, "shikkenan barni dashi Zan dawo gobe insha allah" ",Tom shikkenan abba saï ka dawo amma wannan abin kadaina" "mai kake tambaya ta Haka?" "Kasani abbana" " uhma karaminsu babbansu Kai ko to na daina Shan komai " "uhm abbana kenan shikkenan Zan ganema idan ma baka daina shaba " "tom shikkenan bye" "uhmm uhm Abbana kagaji Dani kenan?" "A,a ni n'a isa ingaji da king" "to naji har da wani cemin king wato cin hanci za a bani to bai isheni ba ka fadamin wani abu" "Kai oh ni dan gidan innata wato yaronan ka rainani da yawa saï kace wata budurwar ka duk lokacin da zamuyi waya saï kasa nace maka i love you , to wallahi kakiyayeni" "hhhh abbana gashinan ka fada to Nima I love you too baby boy" kitt ya katse wayar batare da ya jira abin da Abba zai ce ba,

"Kajini da yaran zamani wai ni ne baby boy ? Hmm abba yayi kwafa ya juyo in da yaji ana dariya kasa_kasa yace "to Kai Kuma fa wa kakewa dariya?" Abba ya fad'a tare da hade girar sama da ta kasa" Fu,ad ne yace " wallahi abbanmu da Kai da yaya Abjeed Idan kuna wani abun saï kace abokanai ko Yaya da Kani" "uhm Fu,ad kenan ban San meyasa ba Abjeed ya Mai Dani kamar wani kakansa Ni Ina tunanin ma Anya dannan ba a can asbiti aka canza min shiba " dariya ce ta kubucewa fu,ad besan lokacin da yace "abbanmu Anya kuwa yakamata ayi bien cike dan duk kanmu yaya Abjeed ya fimu kyau da komai Allah na tuba ayi mutum kamar aljani" "kull fu,ad kafa na sake jin irin wannan maganar abakin ka Ni ma da Wasa nake Abjeed danane na sunna Kuma mahaifiyar ku itace mahaifiyar sa" yayi maganar ransa a bace,

"Abbanmu! abbanmu dan Allah kayi hakuri nima dawasa nake ,abbanmu Wai Ni naji kamar Yaya Abjeed Yana cewa Yaya Abeed ya dawo Kuma har yanzu Bai canza halinsa ba still dai Yana cikin damuwa Wai Mai yake damun sane abbanmu !? Kullum Ina son insane Maine ainihin labarin yaya zarah meyasa Yaya zai damu Akan ta Haka Amma kaki ka sanar dani, asanina dai tasowar danayi a gida hoton yaya zarah kawai nasani kuma shinake kallo Amma har yanzu bansan menene ainihin tarinhin rayuwar gidan mu ta baya ba domin ni a lokacin bani da wani wayo sosai ban sani ba dai ko Yaya Abjeed yasani tun da shi ya girmeni Abba Ina son insan menene labarin Yaya zarah Kuma wacece ita ? Menene dalilin da ya hadaka da ita tun da Naga ita ba 'yarka bace Dan da ace Yaya zarah 'yarka ce wani abun bazai taba had'ata da yaya Abeed ba, n'a rokeka abba ka barni labari Akan asalin tarihin A.k FADAMA".

Fu,ad ya karasa maganar Yana durkushe wa a gaban mahaifinsu cike da son sanin abin da yake tambayar mahaifin nasu.

Wani gwauran numfashi abbanmu yaja hade da tsuramin Ido Yana kallona cike da mamaki ,can Kuma sai Abbanmu ya cemin "Fu,ad kana son sani abin da ya fitar da Zara,u daga daular fadama ko? Fu,ad labarine Mai tsayi wan da ya shafi abubuwan ban tausayi da ban Al,ajabi a cikin sa ,sannan labarine Mai rikitarwa ,idan nace Zan baka labarin Nan bazai yuwu mugama shi a yanzu ba Dan Haka namaka alkawarin Zan baka labarin ka biyoni bashi"

Cikin furgici n'a kalli abbanmu hade da hafiyar wani masifaffen yawu nace "abbanmu wannan abin da ka fadamin ya Kara sakamin kaunar sonjin wannan labarin abbnmu Dan Allah ka taimaka kafara bani labarinan ko a takaice ne kafin mu zauna kasamu lokaci" "uhm fu,ad kenan shikkenan Zan baka rabarin Amma ba da kaina ba Zan dakkoma ka asalin littafin da marubuciyar nan ta rubuta Akan Zara,u sai na baka ka karanta kaji" "to abbanmu meyasa bazaka bani da kanka ba sai nake ganin kamar jin komai daga bakin ka sai ya fi" "a,a fu,ad ka karanta komai ni balallai n'a iya fada maka wani abun ba sabi da kunya da nauyin ka da nakeji, kaje cikin Wan cen d'akin ka bude drowar zaka ga littatafai guda uku babban ciki shine wan da zaka ji dukkannin abin da kakeson sani" "to abbanmu Amma Abbanmu Naga d'akin arufa Ina mukullin sannan abbanmu Zan iya tafiya da littafin faransa ?" "Eh zaka iya Amma kada ka Bari Abeed ya gaji, sannan mukullin Yana jikin kofar " Abba ya fada tare da mikewa ya hau sama Yana cewa "kasha karatu lafiya"

Bayan tafiyar abbanmu sama Fu,ad ya Mike yanufi kofar wadda daga gani an dade ba a bude ta ba ganin yadda Kura ta baibayeta ga Yana har jikin mukullin, cikin azama Fu,ad ya dauki mukullin ya saka sai ga kofar ta bude , murmushi yayi kana ya tura kofar ya danna Kai, Nan take ya dawo baya da sauri kasan cewar kurar da ta daki fuskarsa ga Yana da tacika d'akin, tari ya somayi na yan mintina Yana tunanin ya shiga ko karya shiga domin tun daga yanzu har yaji tsoro da kid'ima ya Soma ziyartar zuciyarsa, tunani ya shigayi can Kuma sainaga ya Yi addu,a ya danna Kai ciki hade da saka hannu ya shiga Kore yanar har ya Isa bakin drowar , batare da Bata lokaci ba ya shiga duban littafin can ya hangosu kamar yadda Abba ya fad'a masa babban littafin ya dakko ya juyo Zan fito Nan take idanunsa suka Kai kan hotunan Abeed dake manne a jikin bangon dakin ,Can Kuma ya hango hoton wata kekkewar yarinya a gefe Mai Kama da Yaya zarah bakinsa har rawa yake wajen cewa "Kai Adeena Mai yakawo hoton Adeena Nan d'akin Daman ta zauna a cikin gidannan to kenan waye ya haifeta Daman ba 'yar abbanmu bace to idan ba 'yar Abba bace Yar wace ko dai 'yar Yaya Abeed ce ? Kai bazai yuwuba, fu,ad yayi saurin fita daga dakin ya koma dakinsa inda ya samu Zaid sai baccinsa yake hankali kwance, saurin zama yayi ya bude bangon littafin ya Soma karantawa kamar Haka,..........

Asalin labarin ya Soma ne Tun daga farkon zuwanta gidan mu ,ita din ba kowa bace face kaddara ta,wadda ta kasance nakaso a rayuwata dama' iyayena Baki d'aya ,wannan daki nane wan can Kuma d'akin Dake gefena na hannun hagu shine sakin ta.

Saurin rufe littafin fu,ad yayi ya fita Dan ya tabbatar da abin da yagani a cikin littafin, Yana karasawa cikin falon ya nufi dakin dayake a hannun hagu ma,ana dakin kaddarar yake son gani, Kai tsaye ya karasa bakin kofar ya tsaya kamar yadda yasamu mukulli a jikin kofar d'akin da ya dakko littafin Haka itama wannan kofar mukullin a jiki take, murdawa yayi ya shiga , Nan take yaga wani uban Kira da datti wan da yafi ma na d'akin can, duk da Haka tusa Kai ciki yayi tare da Kade yanar d'akin, a hankula ya shiga zagaye harabar d'akin Yana kallon ko Ina nacikin d'akin ,komai yananan yadda yake sai dai datti da d'akin yayi kawai zama yayi a gefan gadon sai jiyayi ya zauna a kan wani abu ,da sauri ya tashi ,wayoyine guda biyu a ajiye sun Yi Kira sunyi tilis hatta zanin gadon ma yayi datti kamar ba fariba, sai kayan Wasa Teddy a kasa manya Kai kana ganin d'akin kasan d'akin macene, wayar ya dauka ya Soma dannawa sai dai Babu alamun zata kawo Dan Haka ya bude bayan wayar sai ga memory ya Fado, da sauri ya dauka ya ajiye komai ya nufi hanyar fita, har zai fita ya ci Kara do wani kekkewan hoto a bakin kofar ,Baki ya bude tare da cewa "woww Yaya Zarah da kina k'arama kinfi kyau kamarki sak kamar Adeena ,to Amma Ni Wai abin da nake son tabbatar wa shin Adeena 'yar wace Daman ba Ammi ce ta haifeta ba?" Fita yayi tare da tunani kala kala a zuciyarsa ya koma d'aki kana ya dauki littafin zai cigaba da Karan tawa , zaid ya tashi daga bacci ya Soma kuka.

"Oh my God"
Chapter 11 · 0% Book details